← Book details Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 54

Sashe 54

Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake.

Hijabi kawai ta dauka ta zira akan kayan dake jikinta, ta kwalama diyar kanwanta kira tace "nafita yar albarka saina dawo, ki daura abincin dare" daga ciki yarinyar ta amsa da "saikin dawo Mama" fita tayi daga dakin ta kwalama driban ta kira yafito, mota ta shiga tace yakaita orphanage dinsu Waleed ya amsa mata da to, yatada motar yafita daga gidan.

Ko cikakken 15min direban bai daukaba yakaita orphanage din, tana fadin mahaifiyar Arham ce ita aka barta ta shiga dan ta taba zuwa sau daya suka shiga ciki, kirjinta bai kara faduwaba sai dataga ma'aikatan orphanage din carko carko a tsaitsaye ana tattaunawa agaban clinic, parking direba yayi tabude kofa tafito daga motar kirjinta na bugawa, wayarta dake hannunta taciro tanemo layin Arham ta hau kiranshi danta tambayeshi maiya faru, wani abu yafaru ne amman har wayan ya katse bai dauka ba, hakan yasa tai dialing number Ammi, ringing daya Ammi ta dauka, ahankali Mama tace "Hajiya na iso" cikin muryan Ammi dabata fita sosai tace "kishigo asibitin muna emergency" shine kawai abunda Ammi tafadi mata ta katse wayan, sosai Mama taji kirjinta na bugawa yanda Ammi kemata magana, hakan yasa ta daga kafarta tana kallon mutane ta shiga tafiya harta karasa gaban asibitin tasa hannu ta bude kofar ta shiga ciki, kasan cewan emergency din asibiti bata boyuwa yasa tana ganin dakin tagane batare datama tambayi nurses din dake wurin ba tai wajen kofan, ahankali ta murza hannun kofan dakin tashiga ciki, Ammi da Mom tagani zazzaune, Mom kan kujera Ammi kuma kan gado gefen kafar Waleed, Waleed kuma kwance kan gadon asibiti, ansa mishi drip, fuskarshi tai jajir ta kumbura wuyanshi ma haka, hannunshi adaure daurewan irin na karaya dinan, wani irin mummunan faduwa gabanta yayi karfin hali tayi tadaga kafarta ta karaso cikin dakin ta tsaya gefen Waleed, bakinta har rawa yake tace "Ha....Hajiya meya sami Waleed? Meya faru? Meyasame shi"? muryanta na breaking sosai tayi maganar hankalinta a mugun tashe, dagokai Ammi tayi tazuba mata jajayen idanunta sanan ta tashi daga kan gadon tace "biyoni" da sauri Mom ta tashi tana girgiza ma yayarta kai amman Ammi ta dauke kai kaman bata ganta ba tabude kofa tafita Mama biyeda ita, itama Mom tabisu wajen, tsayawa sukayi a reception premises din cikin fushi Ammi tamata pointing dakin da Waleed yake ciki tace "wlh mutuncin ki danake ganine yasa nakiraki dan kizo kiga abinda yafaru da idanun ki, kinga Waleed dina, kinga yanda yake akwance agadon asibiti, kinga yanda yadawo, dan iskan danki ne ya mishi haka, Arham ne yama Waleed dina haka, jibi yanda yama d'ana dukan dakoni dana tsugunna na haifeshi bantaba mai irinshi ba, kitayani tambayan Arham da ina labo yazo yatayani nakudar d'ana ne dazai kamamin shi ya daddaka haka"? mamaki ne ya mugun cika Mama kaman wacce ke koyan magana tadafa kirjinta tace "Arham! " tana kwalalo idanunta waje tsabagen mamaki, cikeda masifa Ammi tace "duk abunda Waleed yama Arham da abunda zai saka mishi kenan, Waleed ko agogo nasaimai bayi karba saina sayo biyu nashi dana Arham, komi shida Arham, amman yau Arham ne zai kamashi yama wanan shegen dukan toh wallahi bazan yarda ba, wlh, bazanji kunyarki na cuci kaina ba, wlh wlh bazan yarda ba yanda yama yaron nan shegen dukan nan sai shima anmai irin ta, mai rabani da Arham sai Allah don saina yagashi, saina sa anmishi x10 abunda yama Waleed wallahi wallahi bazan yarda ba" Mom dai batace komai ba kuma batayi yunkurin hana Ammi fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham.
Chapter 54 · 0% Book details