← Book details Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Agogon hannunshi ya kalla 8 tayi na safe harda yan mintoci, masu shara da watering plant sai gaidashi suke yana amsawa atakaice dan baida son yawan magana ko dogon zance da ma'aikatanshi inbadai takama ba, karasawa clinic din yayi ya shiga da sauri nurses biyu dake wajen suka karaso inda yake. "good morning Dr" "morning" ya amsa atakaice yana tafiya, daya daga cikinsu dake rike da nursing chat sheet ne a hannunta tace "Dr the patient a ICU yanzun nan nadawo daga daukan vitals dinta everything seems normal" gyadakai yayi yana tafiya, sanan tace "jinin daka samata yakare, nacire waiting for you ka shigo tukunna" tai maganan daidai suna karasowa gaban ICU din, ahankali yace "good job Ramlat" murmushi nurse din tayi, dayan nurse din tace "Dr baby Mustafa, that sickle cell from pediatric ward da aka tsinta" gyadamata kai yayi alamun yagane wanne Mustapha take magana tacigaba da magana tace "we lost him last night" chak ya tsaya yajuyo ya kalleta, saikuma yace "wani irin we lost him? Ba Dr Kemi ke handling case dinshi ba amatsayin ta na pediatrician?" gyadamai kai tayi tace "Sir yaron yaji sauki sosai, toys din daka sayomai harya fara amfani dasu yana wasa playing sosai, ko jiya operation din da kayi ne nasan bai baka daman dubashi ba, jiya kawai middle of the night temperature shi yay rising saikuma yafara convulsing, Dr Kemi did all she could amman we eventually lost him, actually Dr Kemi ma just left yanzun nan tana tafiya kana shigowa" shiru yayi saikuma ahankali yasaki handle din kofar ICU yajuya direct pediatric ward yaje single room section ya shiga nurses din biyedashi, ahankali yake kallon wani dan karamin jariri da duka duka bazai wuce 5month ba an lullube shi da farin zani dakin an gyara tsaf, dakin hadadden gaske, toys ta saman gadon da aka kwantar dashi dake juyawa wanda zai dinga sa yaron murna yana daukemai hankali, karasawa gaban gadon yayi yaja plastic chair ahankali ya zauna yay shiru yana kallon gawan yaron batare daya budeta ba, sanan yajuyo ya kalli nurses din biyu yace "kuje boys section, akiramin Baba Mani" gyadamai kai sukayi suka fita tareda rufo mai kofan, maida kanshi yayi ya kalli gawan kafin ahankali yasa hannu yabude fuskan yaron tahanyar yaye lullubin ya kallai, yaron baida wani kiba sosai fari ne kaman yaran fulani ga gashi akanshi sak irin gashin agwai yay wani irin haske yadan soma chanza kala dan tun around biyun dare ya rasu, hawaye ne yaji sun taho mai da sauri ya sharesu sanan yatashi yakai lips dinshi ya sumbaci yaron a goshi yana kallon fuskarshi kaman zaimai magana yamai gwarancin yara, ahankali yay murmushi yace "I remember ranan da aka kawo ka gidan marayun nan 5month ago" yay dan shiru yace "wasu manoma guda uku suka kawomin kai, suka cemin sunje gona zasu shuka iri sukaga abu a kwali ga kukan jariri suna budewa aka ganka ba kaya a jikinka jini duk yabata ka daga gani daga haifoka aka yardakai, aka kawomin kai gidan nan, I collected you and held you in my arms ina kallon fuskarka ina wondering wace mahaifiya ce zata haifo wanan kyakkyawan halittan ta yardashi awulakance haka, I whispered to your eyes Mustapha don't cry again domin kuwan Allah yakawo ka idan bazan taba bari daidai da sauro daya ya cijeka ba, mahaifiyarka ta wulakanta ka amman Allah daya hallito ka yace bazaka wulakanta ba yakawo ka inda za'a baka kulawa, allura dakai, abaka duk wata aba dakake so" yay dan shiru ya share hawaye again sanan yace "na aika aka kira Mama Iyami nabata kai nace amai wanka asamai kaya akawomin shi clinic naduba Mustapha, nabaka Mustapha sunan prophet manzon mu da Allah ya aiko mana dashi, after series of tests nagano sikla ne kai, ban karaya ba nace I will do everything in my power naga karayu amman dayake Allah shine ubangijin mu yace baxaka rayuba harka kai matsayin danike tunani ba yau karasu Mustapha, Allah ubangiji ya jikanka, Allah ya gafarta maka, I so much wish dabaka rasu ba but Allah yafini sonka, till we meet again Mustapha" yay maganan ahankali yana kara sumbatar goshin shi daidai lokacin an bude kofan dakin, tashi yayi ahankali batare daya juyoba yasa hannu ya share hawayen shi tass sanan yajuyo ya kalli Baba Mani wani dan tsoho ne daya manyanta cikin shigan arziki ya shigo, hannu Baba Mani yamikamai yace "ina kwana likita, Allah ya gafarta mai kaji, Allah yasa yahuta" Baba Mami yamai gaisuwa dan yasan inhar akai rasuwa a gidan marayun nan yana mugun taba Waleed bakadan ba dudda yana daurewa baya nunawa, dan murmushi Waleed yayi yace "Baba Mani a dauke shi aje amai wanka amai sitira, in angama komi a kirani muyi jana'iza sai akaishi" gyadamai kai Baba Mani yayi yace "shikenan likita kayakuri, tafi ka cigaba da aikin ka, ladanka naga ubangiji ne abinda kake mana mu marasa karfi da wayan nan marayun ubangiji Allah ne kadai zai iya biyan ka, katafi" gyadamai kai yayi yajuya yafita daga dakin nurses din suka bishi, ICU yayi ahankali yabude kofar idanunshi suka sauka kan fararen kafar nan nata tafin kafan so pinkish suna facing kofa, ajiyan zuciya ya sauke ya shiga ciki yakarasa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannunshi akirji yana kallon fuskarta da idanunta kenan a lumshe, dauke idanunshi yayi daga kanta yadau torchlight mai kama da byro yadan duko yabude idanunta tareda haskawa yaga idanun sun gyaru dan bakin sun sauko ba kaman jiyaba da ba'a ganin bakin,, sakin idanun yayi yakai yatsunshi biyu ahankali yadaura kan wuyanta, wani irin firgita tayi cikin bacci da saida shima ya firgitan ya janye hannunshi da sauri yakoma baya, ajiyan zuciya ta sauke tacigaba da baccin ta tayi kaman ba itane ta firgita yanzun nan ba, vitals dinta yaduba yaga komi nata is stable sanan ya kalli nurse yace "by 1 zan dawo na dubata" fita yayi daga dakin ya zaga through all wards din yaduba all patients dinshi dat are on admission sanan ya sallami wanda sukaji sauki sosai aka maidasu hostels dinsu, wuraren 10 yagama komi yafito sabida kiran da Baba Mani yamai, alwala yayi yaje akama Mustapha salla suka wuce suka kaishi shibai bisu ba sabida zai koma hospital.
[10/18, 1:04 PM] +234 703 278 9649: ✍️ M SHAKUR

1️⃣ 7️⃣
Chapter 30 · 0% Book details