← Book details Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 54

Sashe 43

Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dan nisawa yayi yace "I will always love my lawyer, kinsan ciki babu hormone din dabaya tabawa ajiki, to harda na brain dinki yake tabawa saisa kike ganin abu ba'a yanda yakeba, akwai inda very Important zan lallasheki inna dawo" ya shige bayi yafara wanka, yana cikin wanka taji anbude gate, dawani irin sauri ta zabura ta tashi ta yaye labulen dakin Waleed taga motar yayarta Anty Hussaina ya danno cikin gidan, gefenta kanwar Maman su ne dasuke kira da Yakolo, sai back seat dabata gane wayeba tadai tabbatar Anty Hassana ce, salati ta buga. "Innalillahi wa innailaihi raji'un" da sauri tai wajen bayin ta bubbuga tace "Arham please kafito da sauri kasaka kaya su Anties dina sunzo" da sauri Arham yadauraye jikinshi yafito daure da towel, kayanshi Ilham ta tattara ta mika mishi daidai yayinta na kwarara sallama a falo, Anty Husai tace "karkuyi mamaki tanachan sama tana bacci abunku damai ciki kumuje saman mutadota" da sauri Yakolo tace "nifa banison shirme in mijinta na nanfa" "miji, ai mijinta Anty Yakolo tun safe yake tafiya aiki, daman tun bayan jere baki kara ganin gidaba kumuje sama" sukai stairs rawa jikin Ilham yadauka tace "na shiga uku na lalace, nabani Arham mezanyi yanzu sunzo sama" daidai lokacin yakarasa saka riganshi yace "calm down I will handle it" yay wardrobe din Waleed yabude wani jallabiyan Waleed yadauko yamika mata dan tsirara take yace "saka wanan kiga" sakawa tayi ya agurguje ya saukan mata har kasa sanan murya chan kasa yace "calm down" ijiyan zuciya tasauke ahankali sanan yashiga kalle kalle adakin, wani file din Waleed yagani akan side drawer dinshi yadauka da sauri yay hanyar kofa yace "muje" bude kofa sukayi daidai su Anty Hussaina sun hayo saman turus dukansu sukayi suna kallon Arham da Ilham dasuka fito daga dakin yay kaman bai gansu ba yace "mijinki ya isheni da aike, kidinga dubawa kina tabbatar da baiyi mantuwa kafin yatafi ba" dan dariya tayi tace "ai baby sai......" daidai ta juyo tahada ido dasu Anty Hussaina wani irin tsalle ta daka da ihu tai wurinsu. "oyoyo Anty Yakolo" tafada jikin kanwar Maman su datai turus tana kallonta, ganin haka yasa yataho shima ahankali yace "sannunku da zuwa" sanan yawuce yaraba ta gefensu yasauka kasa abinshi boldly and majestically yabude kofan falo yafice, yana fita Anty Yakolo ta fizge ta daga jikinta tace "dan ubanki wanan wani kato ne yafito daga dakin mijinki, sabida ke dakikiya mahaukaciya ce jibi gashinki bako dan kwali ya hargitse kaman na mahaukaciya, dan ubanki waye shi?" kaman zatai kuka tajuya ta kalli Anty Husai, Anty Husai ranta abace tace "badake ake magana ba, dakina Amarya ma haka mukazo gidan muka ganshi, kifada mana uban meyake kawo shi nan gidan, tuntuni muna sallama ba amsa" kaman zata fashe da kuka tace "me kuka nufi da wanan irin tambayan dakuke min? Wani tunani ne aranku? Sabida kun ganni busu busu ahaka? Nima tashina daga bacci kenan, shine ma yatadani daga bacci Waleed ya aikoshi ya daukomai wani abu adakin, shine fa nabude mai dakin ya dauka, banmasan kaina ba dankwali ba" tafashe da kuka sosai dayasa dukansu jikinsu yay sanyi, Anty Yakolo ne ta katse shirun tace "nidai tashi bar kukan ba kyau me ciki na kuka, je dauko dan kwali kisaka, kukuma mu koma kasa kawai" juyawa sukayi itakuma ta tashi tana kuka kaman gaske ta shige dakinta har lokacin gabanta faduwa yake tana godema Allah datasha da kyar.
[10/18, 1:06 PM] +234 703 278 9649: ✍️ M SHAKUR

2️⃣6️⃣ & 2️⃣7️⃣

Komawa falo sukayi duk suka zauna Anty Hussai da Yakolo sukahau hira banda Anty Hassu datai shiru tana tunani ko kadan bata yarda da Ilham ba, but still batason tama Ilham tunanin datake yi, duka duka yaushe Ilham ta girma hartai wayon da da aurenta zata dingabin wasu mazan, ta tambayi kanta saikuma tai shiru, duka duka yaushe akai auren Ilham dake mugun son Waleed kaman zatai haukane zatabi wani namijin? Ajiyan zuciya ta sauke tana kokarin kawar da tunanin daga zuciyanta dan bamata fatan abinda take tunani shike faruwa.

Wuraren 4 na yamma ya shigo gidan marayun yay parking motarshi yana tattaro wasu uban takardu daya ijiyesu a kujeran gefen direba ya kwasa dayawa yarike sanan yabude motan yafito daidai Waleed yakaraso wajen dan daga masallaci yake, wani iri Arham yaji dayaga Waleed kaman zai maida takardun cikin motarshi saikuma yarike hannunshi, karasawa wurin shi Waleed yayi hannunshi zube cikin aljihu yace "kadawo blood" gyadamai kai Arham yayi yace "yes nadawo blood, Mama ta iya saka mutum aiki, iyaye sai ahankali" zaro hannu Waleed yayi daga aljihu yamika Arham din yana kallon uban papers din hannunshi yace "what are those blood mugani"

Da sauri Arham ya kalli papers din gabanshi nafaduwa Saikuma yakara linkesu yana lankwdhesu da kyau gudun karyaga mainene su yace "they're not mine, nawani dan anguwan mu" saikuma yabude mota da sauri ya zubasu ciki sanan yamaida kofar motar yarufe yajuyo ya kalli Waleed dahar lokacin kallonshi yake, sanan yace "muje daman akwai maganan danake so namaka" juyawa Waleed yayi yace "am going to the clinic now to check my patient nafito mayi maganan" ganin kaman ran Waleed din yabaci yasa yace "muje to naraka ka clinic din" yabi bayan Waleed din, clinic din suka shiga da basuda much patient that are on admission saidai out patient wayanda kawai zasuzo suyi complain kazakaza na damunsu adubasu abasu magani sutafi, dakin da Widad take direct Waleed yayi Arham biyeda shi suka ya shiga, tana kwance akan gadon an lullubeta da bargo fuskarta ne kawai awaje da gashinta da akai parking tana bacci, idanunta har wani nama nama sukayi tsabagen bacci, karasawa gaban gadon yayi Arham biyeda shi, Arham yace "for the past 3month now kullum yarinyar nan nazo dakin nan bacci take saikace wacce take a coma" stethoscope yadauka yana makalawa a kunne yace "she's not in a coma, babu ranan duniyan dabata tashi, yawanci sau daya take tashi, amata brush abata abinci suma duk tanaci tana gyangyadi tasha magungunan ta, I was the one that increase her dose, duk wanda yakeda damage a brain need absolute rest, yesterday nakara mata MRI da CT scan I was happy with the result, fluid din yaragu sosai wanda yarage baifi an atom size ba, yanzu shi nabashi 4days, dazaran kwanakin sun cika zan sake running test din inhar babu saina godema Allah, tagama da magungunan zan mata transfer zatabar hospital takoma hostel, dudda haka I will be monitoring her ina bata magungunan that help with the memory lost" yay maganan yana zare, stethoscope din daya daura kan kirjinta duk Arham na kallonshi, dan tabe baki yayi yace "tamayi kokari kusan watan ta 9 akan gadon asibiti, sai yanzu ma nake dana sani daban karanci medicine ba nima nadawo likita kaman kai nawani kama ina karanta engineering, kumako kasan inda na karanta medicine dafa nafika kwarewa" yay maganan ahankali hankalin shi nakan wayanshi dayake dannawa yana kokarin turawa Ilham message kartace baikara nemanta ba, dan juyowa Waleed yayi ya kallai jin maganan yamai wani iri aka, ganin wayama Arham din ke dannawa yasa yagyara mata bargon yace "let's go" yay gaba shikuma Arham yamaida wayan aljihunshi da sauri yabishi suka fita, office din Waleed suka shiga, Arham yaja kujera ya zauna Waleed ma yazauna yana gyara zaman takardun kan table dinshi sanan yace "yes ina jinka kace akwai maganan da kakeso kamin blood"
Chapter 43 · 0% Book details