← Book details Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Dawowa Salima tayi ta tsaya akanta, karasa soke daurin tayi Ilham tamike ta kalli Salima ganin ta daddaure fuska yasa tawani fada jikinta tareda rungumota tace "dalla na face miki sorry please karki damu anjima zan baki labarin Dr kinji ni yanzu kiyakuri dan Allah" yanda duk takaiga fushi saida tai murmushi tace "shikenan" tace "kinga yanda kikai kyau kuwa kaman bakeba Ilham" murmushi tayi tace "yi sauri muje naga Dr dina" hannunta Salima takama sanan tabude kofan suka fita sau daya tasaci kallonshi ta sunnar da kanta kasa ganin bashi kadai bane, shi hankalinshi ma nakan wayan hannunshi yana danne danne yay wani irin kyau da saida taji gabanta yafadi hakanan taji wani kishi yataso mata yanzu duka matan dasuka cika gidan nan su ganshi ahaka, da kyar ta iya ta danne kishin suka cigaba da sauka daga stairs ahankali, Hasim ne da Abdul suka tashi suna murmushi "wow, Amaryan Ya Waleed" karasa sauko da ita Salima tayi tana musu murmushi sanan takaita harkan kujeran da Waleed ke zaune two sitter ta xaunar da ita a gefenshi tace "Dr ga amaryan ka nan nakawo maka yanzu kwa barni nahuta" maganan dayaji yasa yadan dagokai ya kallesu sanan yadauke kai, juyawa Salima tayi tai waving su Hasim tace "bari naje waje" da sauri Abdul yace "bari muma mubiyoki mubama love birds some space" dan dagokai Waleed yayi ya watsa musu harara suka kyalkyace da dariya suka fice abinsu falon yarage dagashi sai Ilham dake zaune kusada shi dukansu sunyi shiru.

Almost 5min suna zaune basucema junansu komiba sanin zasu iya kwana ahaka bai cemata kalaba dan tasan magana wuya takemai yasa ahankali tamika hannunta dayasha lalle ta daura kan hannunshi daya ijiye kan laps dinshi ta kama hannun gam, atare suka dagokai suka kalli juna, tasake matse hannunshi dat feels so soft kaman hannun mace smiling, ahankali tace "Dr is our wedding are u not excited? I feel so happy because am getting married to love of my life, I love you so much Dr Waleed Warbai" tai maganan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, dauke kai yayi da sauri he don't really know abinda ma zai cemata, ko 1 single feeling baidashi akanta, ganin baice mata komi ba yasa cikeda son janshi zance tace "waye best friend din naka cikin wayan nan da kazo dasu?" ahankali yace "bayanan, this are my siblings" murmushi tayi tareda lumshe ido tana bala'in son jin yana magana, maganan shi dadi sosai wlh, voice dinshi bala'in dadi, murmushi tayi tace "yana ina shi? Maisa baizo tareda kaiba?" dan dagokai yayi ya kalleta suka hada ido sanan yace "I left him in the office you will see him later" gyadamai kai tayi cikeda sonshi tace "kayi kyau sosai" dauke kai yayi yace "thanks" yadanyi shiru saikuma yace "you look beautiful as well" wani irin cikakken murmushi tasaki cikeda jin dadi sosai tace "nagode Dr" sukai shiru, agogon hannunshi ya kalla sanan yadago kai ya kalleta hada ido suka sakeyi dan idanunta na kanshi har lokacin, hannunshi yatura cikin aljihu yaciro duka rapan kudin daya taho dasu ya ijiye mata akan cinya yace "use it for anything you need, will see you later" gyadamai kai tayi ya mike tsaye tashi itama tsaye tayi itama batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi tsam tsam murya chan kasa tace "thank you Dr, sai anjiman kaji" sanan tasake shi d sauri yajuya yafita daga dakin batare daya kalleta ba yafita daga gidan.

[10/20, 11:40 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

✍️ M SHAKUR

3️⃣

FREE PAGE
Wuraren 4 yafito daga office dinshi ko kallon office din Waleed baiyiba yasauko yay wajen hadaddiyar motarshi ya shige yaja motar yadau hanyar barin gidan marayun, agaban wani gida dan madaidaici mai kyan gaske yay parking ya sauko, shiga gidan yayi yabude gate din sanan yakoma mota yaja motar zuwa cikin gida, parking yayi sanan yafito yaje yamaida gate din ya kulle yana bin tsakar gidan da kallo dayasha flowers ga interlock akasa dudda gidan baida wani girma sosai but yanada kyau, karasawa yayi ya shiga flat babba kwara daya da shi kadaine atsakar gidan, bude kofa yayi ya shiga falon da babu kowa ciki sai TV dake aiki gawasu hadaddun setin kujeru dasuka zagaye falon suka karama falon haske da kyawu, wucewa yayi ya shiga wata yar corridor da dakuna uku ke ciki, ahankali yake tafiya har yakai gaban dakin dashine last room din corridor yabude kofar dakin ya shiga, dakine mai kyau sai kamshi yake, ga Royal bed aciki sai kujera daya 3sitter komi na dakin fari harda curtains din dakin, wani babban frame na hotonshi ne ajikin bango, rage kayan jikinshi yayi yawuce yashiga bathroom din dake cikin dakin, wanka yayo yafito ya shirya cikin wata yar 3quater da farin singlet yazauna kan gado, wayarshi dayaga tana dan kawo wuta yasa yagane anyomai message, mika hannunshi yayi yadauki wayar ya danna, sako yagani daga Waleed.
"Where are you My P.A🤣?" yay emojin dariya agaba alamun tsokana yake, tsaki Arham yayi ya cillar da wayan yay kwanciyar shi akan gadon tareda lumshe idanu yana sauke ajiyan zuciya.
Chapter 4 · 0% Book details