Sashe 25
Duniya Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ahankali motar data kwaso mutane kusan goma sha hudu ta God is good take tafiya sabida yanda motar ke over heating, passengers din cikin motar sai tsaki suke suna korafi daga Abuja da suke, yanzun nan suka baro Abuja Benin zasu amman shine tun yanzu sun tsaya yakai sau uku wanan wani irin abune, daidai sun shiga MURTALA MUHAMMADU BRIDGE dake nan hanyar lokoja gaban motan yafara hayaki hakan yasa dole direban yayi paki tareda tsaki yafito, bude kofa passengers sukayi dan sufito sudansha iska indamai fitsari yaje yayi, wata matace dake rikeda yarinyar da at least zatakai 7yrs ne tace "Mummy I want to ease myself" kallon Bridge din matan tayi duk titine ga maza kuma itama fitsarin takeji agaban su zasuyi tunanin hakan yasa takama hannun yarta tarike tareda rataya Jakarta akafada suka sauka daga Bridge din zuwa kasa, sauka sukayi suna tafiya, tanacikin tafiya taji ana tafiya da sauri matar ta juyo ganin wata yar matashiya yasa da sauri matashiyar tace "me to I want to piss madam, sorry if I scare you" juyawa matar tayi tace "no problem" sauka sosai sukayi suna dandarawa har zuwa gaban ruwan da ake cewa anan River Niger da river Benue suka hade, cirema yarta wando tayi tace "tsugunna kiyi, bari indan matsa ta chan is like na pupu dey worry me sef, since ba yanzu motar nan zatai cooling down ba gwara nai kayana our journey still fa, if u finish just stand here I dey come" gyadamata kai yarinya tayi itakuma Maman ta shiga cikin ciyayi sabida yadan kareta, yayinda itama dayan budurwa tashiga cikin ciyayi kowa yashiga biyan bukatun sa. Wani irin ihu da yarinyar ta kwala ba matan kadaiba har mutanen dake chan wajen mota saida yay calling attention nasu. "Mummmmmmyyyyy!" azabure uwar ta tashi ko kashin bata wanke ba tafito tanajan pant dinta sama same with dayar budurwan, da sauri Maman tai wajen yarta dake tsaye tana kallonta tace "wat is it Engozi?" daidai dayan budurwan itama tazo tace "wats the matter why are you shouting beautiful girl?" duk suka tsaya kan yarinyar suna tambayarta ganin yanda take shaking, ahankali tadaga hannunta tamusu pointing 👉 rafin duk suka juya suka kalli inda take pointing atare maman da budurwan suka hada baki suka kwala wani irin ihu. "ahhh hhhhhhhhhh hhhhhhhhhh!" within 1min suka hada mutane wajen ciki harda direban su dan ihun yay yawa sun zaci macijine ma ya sarezu, yanda yan tafiye tafiye sukaga direbobi na sauka kasa ana ihu yasa aka shiga parking mota ana sassakkowa dan anzaci hatsari ne kafin kace me mutane sunfi dari dayan kai awajen, matsar da mataye biyun akayi dake rangada uban ihu, daya daga cikin mazan da duk suka tsaya suna kallo yace "are you sure this one is alive" daya daga cikin mutanen wajen ne yace "acirota please wanchan bishiyan daya rike mata riga ne da yanzu ruwan yakara sweeping nata away" wani ne yace "waya iya ruwa dan Allah anan?" daidai lokacin wasu rundunan mutanen sun iso wajen daya daga cikinsu yace "na iya na iya" da sauri matan wajen sukahau cewa "oga pray o, this river they chop people wey no be from here" murmushi kawai mutamin yamata yace "this na my work in my state" kayanshi yatube agabansu yarage dagashi sai boxer yamikama wani dasuke tare dayake nan kaman kaninshi kawai yay iyo cikin ruwan, mutane akahau salati masu kiran jesus nakira masu ciro waya na video nayi, cikin hukuncin ubangiji mutumin yakai inda take sanan yafito da kanshi hamdala akahau yi, karasawa yayi wajen ichen daya rike riganta sanan ya damke rigan kafin yazare daga jikin icen, yakarasa wajen yarike ta gangan ajikinshi yashiga iyo da ita yana zuwa baki bakin rafin maza kusan shida suka saka hannu suka karbeta aka cirota ana ihu mutane fam awajen wasu na cewa she don die, this one don die, wasu na cewa na Mamy water, kwantar da ita akai akasa aka danne cikinta amman batai aman ruwa ba, babu wani abu da ba'a mataba, wani direba ne da yanadaga cikin wayanda ke kanta yace "please waye likita anan ko nurse koda na gargajiya ne? Yakamata asan ko tana raye kota mace gashi kanta a fashe yake gabaki daya ta baya please in akwai Dr yazo" yay maganan yana ihu sabida aji hakan yasa aka shiga passing information din har zuwa kan titi inda tulin mutane suke tsaye dan basu samu wurin shigowa ba sabida acike, ciki ikon Allah aka samu wata mota da Dr keciki da sauri aka sauko dashi akai making mishi way har zuwa kan wacce aka tsinta a ruwan tsugunnawa yayi akanta gabanshi na faduwa yace "kai anya wanan bil adama ce?" yay maganan shikadai saikuma yace "ta zubar da any ruwa" atare duks samarin sukace "mum mata komi amman bata fito da ruwaba" soyake ya daga dogon gashinta dat is lying akasa dayaga yakai har cinya ta amman harga Allah tsoro yake baison abinda zai hanashi bacci, tunda yake a Nigeria baitaba ganin mace mai gashi hakaba, hannunta yakama yarike danyay feeling pulse dinta, almost 3min yana saurara amman baiji komiba yana shirin zare hannunshi yaji pulse dinta but very slow and weak a dimauce yace "sh.....she's alive" wani irin kabbarta wajen yadauka. "Allahu Akbar" kiristocin sukahau cewa. "thank you jesus" tashi yayi yace "amman a kaita any nearby hospital this girl or whatever she is need to be saves quick inba hakaba za'a iya loosing nata, machine za'a sata dazai zuko ruwan" da sauri wani yace "wayasan any nearby asibiti?" shiru duk akayi duk asibitin da za'a fadi nacikin garine saikuma wani tsoho yace "ku kaita WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED ko tsintuwa fa akayi gwamnati ta halatta mana kai abinda aka tsinta awajen, akwai asibiti da kwararrun likitoci a gidan, kana zuwa za'a karbeta, banda haka asibitin ne kadai zaku kaita ko sisi baza'a chajeku ba sanan kubarta awajen baruwan ku sune zasu dauka daga wajen, in nemo iyayenta ne inma menene duk su zasuyi, kuma ma ai babu wani nisa yana nan hanyar fita daga Abuja zakuga dankareren gini wane University ga sunan baro baro ajiki ga sojoji" addu'a akahauma tsohon maza suka dauketa wani bawan Allah dazaiyi Abuja yay volunteer motarshi mutane uku suka bishi sabida zamanin nan ba'a yarda da kowa tafiya kusan minti hamsin yakaisu gaban WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLES, sojoji suka taresu saida aka duba motan tsaf bayan sun nuna abinda suka tsinta sanan sukai ciki har asibitin aka kaita soja biyedasu.
Suna shiga sukai parking gaban dankareren asibitin dako wani asibitin cikin gari albarka, already nurses harsun gunguro gado dan sojoji sun riga sun sanar dasu, daura ta mazan sukayi akan gado nurses din na kallonta suka gungurata ciki, Sojan daya biyosu ciki yace "we will take it from here thank you" yanuna musu motarsu, komawa cikin motar sukayi sukabar orphanage din.
Wanan kenan!!!
Suna shiga sukai parking gaban dankareren asibitin dako wani asibitin cikin gari albarka, already nurses harsun gunguro gado dan sojoji sun riga sun sanar dasu, daura ta mazan sukayi akan gado nurses din na kallonta suka gungurata ciki, Sojan daya biyosu ciki yace "we will take it from here thank you" yanuna musu motarsu, komawa cikin motar sukayi sukabar orphanage din.
Wanan kenan!!!