Sashe 8
Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ana saura sati daya bikin ne,alhaji bishir ya zo katsina.bai ko sanar da zuwansa ba.barcin rana take yi lokacin da ya iso. yaran suka yi masa sannu da zuwa.kai tsaye ya nufi dakinsa,ya bude ya shiga.ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. shi kuma ya zauna a bakin gado.hasna ce ta shiga dakin hajiya sauda ta tashe ta,tana sanar mata zuwan dady.ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya isa.ta kalli husna,shi ne ya ce ki kira ni?husna ta ce,aa ya shiga dakinsa ne kawai.sauda ta ce,to je ki ina zuwa.har ta mai da kanta ta kwanta,a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.amma sai wata zuciyar ta ce, mijinki ne kina kasansa ki je. ta same shi yana cire safar kafarsa.ta yi sallama, ta shiga.daga bakin kofa ta tsaya tana fadin,sannu da zuwa.alhaji a ciki ya amsa da cewa yawwa.ta zauna a hannun kujera,na ji mamaki,ba ka ce min kana zuwa ba,kamar yadda ka saba.ya dago ya dube ta laifi ne?ta lumshe ido,cikin takaici ta ce,aa babu laifi.ta mike tsaye,me kake bukata?ina nufin abin da zaka ci ko sha?ya mike, alhamdulillah ba na bukatar ko daya.ta ce,har wanka?ya dan yi tsaki,kin ga na yi datti ne?ta kautar da kai gefe.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (12)Ameen.me kuke bukata a cikin bikin ke da yaranki? ta ce,ba ma bukatar komai bikin da ba a nan za a yi shi ba.mu ma fa yan gayyata ne.ya ce,ba na son kina fadin haka.ba za kuyi ashoben ba?ta ce,aa ba za mu yi ba.ya ce,don me?ta ce,ba za mu samu dinki ba kar ka damu.ya ce,shi ke nan.ya kwana,washegari ya wuce malumfashi.ya koma abuja saura kwana biyar biki.kuma ranar ne aka yi jeren amarya a gidan angonta. lsma'il ya isa abuja yammacin magariba. maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki.ya ce, malam kai ne ka dawo?ya ce,ni ne daga kiran sallar lsha'i ne,alhaji ya bukaci ganin lsmail a kebe.bayan sun gaisa ne alhaji ke tambayar lsma'il lafiya ya dawo da wuri?lsmil bai boye masa komai ba.ya fada masa abin da aka yi masa,ya ji ya tsanin garin katsina.alhaji ya ce, kar ka damu.allah yasa haka ne mafi alheri a gare ka.lsmail ya ce,amin na gode
[01/10 10:34 pm] Abdul: (11)Ta yi dan huci,ta mike. har ta kai bakin kofa,ta kasa jurewa,ta dawo,alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min.ya kalle ta,baki san kin yi laifin ba ko?ta ce,wallahi ban sani ba.ka sanar da ni mana.ba sai in baka hakuri ba.ya ce, ban zaci zan ce ki yi abu ba,amma ki ce min ba za kiyi ba.ni ne na ce kiyi wa MIMI fada kan ta bi zabin da nayi,amma kika ce min ba za kiyi ba,karshe ma sai kika zuga ta ta katse shi,na zuga ta kuma?ln ji ta ne ta ce na zuga ta?shawara na ce zan bata,kuma na bata. ka tambaye ta wace irin shawara na bata?zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina.a tunanina mun kai matsayin da zaka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba.don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.haka kuma in an fadi wanda ba za ka iya ba,zan ce sam baza ka iya yin haka ba.kansa yana kasa,yayi shiru,domin ya san cewa gaskiya ta fada.can ya dago kai,me kika ce mata?ta mike ta koma kusa da shi.bayan ta dauki wayarsa ta soma latso lambobin ta kai kan lambar MIMI ta dannan kira,ta latsa handsfree sai da ta soma ringing ta mika masa,ina son ka tambaye ta,mu ji.kafin ya ce,aa,har MIMI ta daga,muryarta ta ratso,inda ta ce,hello dad.ya ce,MIMI,in tambaye ki?ta ce, eh dad.ya ce,me mamarki ta fada miki game da auren abbas?ta ce,wace maman,momy nafisa?ya ce, mahaifiyarki.ta tura baki,dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so,ko don irin kaunar daka nuna min.wai shawara ta bani.ya ce,shi ke nan. yana kashe wayar sauda ta mike.ya kamo hannunta, kar ki yi fushi matata,ki yi hakuri,na fahimce ki.bai-bai ta dan yi jim,ta ce,shi ke nan ya wuce.ya ce,to zauna muyi maganar auren MIMI.ta ce bani da ta cewa game da auren MIMI,face allah ya bada zaman lafiya. yanzu ka hakura zaka ci abincin?ya girgiza kai,aa sai in kin zauna.ta lumshe ido, ta zauna.ya ce,ni ma na yi miki laifi ban fada miki komai ba.yau saura kwana bakwai.kuma za a yi bikin ne a can abuja.sauda ta ce,babu damuwa. allah ya sa a yi lafiya.ya ce ameen.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (13)Washe gari saura kwana hudu biki,amarya ta sha gyara jiki,ita da na'ima.duk abin da aka yi mata,an yi wa na'ima.mai gyara ta musammam momy nafisa ta dauko.an zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance amarya ba.kawayen MIMI su mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.yammacin laraba za su yi family night. na'ima tayi zaton zuwan 'yan katsina,amma shiru.
MIMI bata damu ba,don ta san ita ba zama za tayi ba. rashin zuwansu ma zai fi mata.a ranar alhamis kuwa za su yi 'mothers day, wanda momy nafisa ta shirya.kuma a ranar ne MIMI suka shirya guduwa,ita da khalil dinta.amma momy nafisa a nata tsarin sai daren jumaa,in an dawo daga kumbo,an yi kamu ke nan sai ta sa MIMI ta tubure.daga nan sai ta tura na'ima ta ce wa dad din su ita ta yarda a daura da ita.
An yi mothers day lafiya an tashi ana ta daukar hotuna,MIMI ta daga wayarta ta kira khalil ta ce su zo,shi da wani abokinsa kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su.da mota suke,don haka ta shige.kai tsaye gidan su MIMI suka koma.babu kowa,duk ana gurin biki,amma dad yana nan.da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya.tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake,amma daf da babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi.
Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (15)Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na'ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa.