Sashe 12
Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta,gami da zagi.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka hawaye.na'ima ta kai yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami da nuna miki kauna kamar da.
Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara.
Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce,
[01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin zata gane ba ta da wayo.