← Book details Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ya fada mata komai.ta ce.to allah dai ya daidaita ku.ka tashi ka je kar ta farka.yanzu to me zaka bata na kari?ya ce,sai dai na je na ji daga bakinta,don ban san da me za ta karya ba.nan suka yi sallama ya nufi gida.kai tsaye cikin gida ya wuce,fatu tana kicin ya ce mata ina kwana?ta dago ta dube shi,aa yan abuja ne?sai muka ji aure.na ce kila dai don mu bamu da zanin zuwa abuja ne.yayi dan murmushi ya wuce.saura suka fito su ma dai ya gaishe su,amma sai sakin magana suke yi.dakin lnna ya shiga tana kwance,ga rushi a gabanta,ya zauna ya gai da ta.ta ce,sai kuma mamuda abokinka ya zo mana da labarin aure.ya ce,eh.abin allah ya kawo shi kafin a yi shiri.ya ce,to allah ya ba da zaman lafiya.mu da har muna cewa kila ka canza dangi ne.ya ce ba haka ba ne.ni ma abin ya zo min ne ba shiri.tana ciki ai tana barci.ta ce,to kuma a nan dakin za ku zauna?ya ce,eh,to sai dai yau zuwa gobe za mu fara neman daki.ya mike,bari in gani ko ta farka. ya sa makulli ya bude dakin.har lokacin bata tashi ba.ya kira mahmud yana tambayar sa ko hamisu ya tashi?ya ce tunda suka yi salla ya koma.ya bar shine ya dan warware gajiya tunda hanya zai kara bi. sai karfe goma da kwata,lokacin tuni lsamail yayi wanka,yayi shirinsa cikin shada mai ruwa siminti.yayi kyau yana ta kamshi.ta farka,mika tayi ta yi tsaki.ya ce,ai kamata yayi ki yi adduar tashi daga barci,ba tsaki ba.yanzu da kin bude ido kin gan ki a kabari fa?ta tashi zaune,da sai na fi murna fiye da in gan ni a dakin nan.da sauri ta shiga neman wayarta.ta dauka ta soma kiran layin khalil,ya katse.ya kira ta, lokacin ne yake fada mata ya taso daga zariya.ta ce, shi ke nan zamu yi ta waya har ka iso.ya ce,shi ke nan,sai na iso din. lsmail ya ce,wai da wa kike ta yin waya ne?ta harare shi,na ce ka daina yin min magana ko?ya ce,to ki tashi ki yi salla.ta harare shi,ta ja tsaki,ba zan yi ba.ya ce kina fashin salla ne?ta mike tsaye cikin mamakin wuce gona da irin. [01/10 10:35 pm] Abdul: (46)Na mutum,ta ce,cikin daga murya,zo ka matse ni ka duba ka ji ko?ta zare idanu a karshen maganarta. ya mike,mai da wukar.me za ki ci?ta sake hararar sa,kai har ka mallaki abin da za ka iya ciyar da ni?ta sauka daga kan katifar ta nufi jakarta wadda ta sa jakarta mai kudi a ciki.ta ciro ta zo zata zauna,sai ta ga malum-malum dinsa,ta sa kafa ta ture.ya ce,oho dai ta yi miki amfani. ba ta kula shi ba ta kwance kudin sadakin da aka bata a gefen gyalenta,ta zuba a cikin jakar,ta dauko karamin akwaiti cikin jerin akwatunanta,ta bude akwatunan tana zabar kayan da za ta sa.yawanci kananan kaya ta diba.ta bude wata jakar ta dauki kayan ciki da na shafa,sai takalmi daya ta saka jakarta mai kudi,ta rufe.ta sauka daga kan katifar.ya ce,wai ke ko fitsari ba ki ji ne,duk sanyin nan da ake yi?ta ja tsaki,ban ga gurin da zan iya tsugunawa ba.ya ce,mu shiga cikin gidan.daga nan sai ki gai da lnnata.tunda ya ambaci fitsari,sai ta ji ya matse ta har kamar zai zuba.shiru ta yi,sai ya dauko buta,mu je in raka ki.ta dauki mayafinta ta dan yafa.suka fito zaure a share fes.don tun kafin ya shiga wanka ya share.suna shiga tsakar gida,matan gidan suna ta aikace-aikacensu.ta sa gefen mayafinta ta rufe hancinta.ya ce,ki gai da su mana.ta zabga masa harara,ta ce,nuna min toilet ni kam.ya nuna mata,ta shiga da kyar ta yi yin fitsari saboda zarni da kuma rashi inda zata tsugunna.ba ta taba ganin irin wannan ban dakin ba,don ko na kauyen su dad da ta tsani shiga yafi wannan kyau.ta fito duk ta bata kafafunta.sai da ta fito ne take ta wanke kafarta,tana zubar da miyau.cikin sauri ta bar tsakar gidan.sai da ta je soro ta sauke numfashi ta soma kuka.matan gida suka yi ta kallon kallo.fatu ta ce,salo da yayi,wai kaza ta ji shikar dare.lsmail ya ce,ku yi hakuri ba laifinta ba ne,ba ta saba da ganin haka ba.suka sa dariya,gami da shewa,to a kai ta inda ta saba,ln ji fatu. shi dai fita yayi ya bar su suna ta habaici da kananan zagi. [01/10 10:35 pm] Abdul: (47)Ta shiga cikindakin ta dauki wayarta ta soma kiran khalil.ya ce,mun kusa ki ba ni minti talatin.gudu nake yi sosai,kin ji dear ta ce,to inda nake ne ko dakin karen gidanmu ya fi shi.ran lsmail a bace,ya ce karya kike yi.lna sake fada miki karya kike yi.ta ce,dakin karenmu akwai tayils,na fa? ya ce,dakina akwai alkurani da littattafan addini.ke nan dakina yafi naki ma,duk kyawunsa.ta sake bin dakin da kallo,tana tabe baki.ta ce,tsayawa yin musu da kai bata lokaci ne. ta sake mikewa ta zage wani zif din akwati ta ciro muhimman takardunuta,ta zage jakar da za ta tafi da ita ta zuba.ta zauna ta yi tagumi,jifa-jifa tana duba agogo,shi kuma ya kasa ya tsare ya ga inda za ta.
Chapter 16 · 0% Book details