← Book details Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta ko'ina abubuwa sun dauki zafi,domin ko can katsina tuni an daura auren zainab da alhaji lawal.an kuma kai ta gidan.matansa uku ga yara nan kwatsam. gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman,sai matarsa ta ukun,sai kuma dakin zainabu.a kasa matansa biyu ne da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wasu matan da suka fita. tunda aka kai zainabu take cikin kuka.bayan kowa ya kama gabansa,ta tashi ta datse dakin alhaji lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha.ya murda kofar amarya,ya ji ta gam.ya yi ta bugawa tamkar zai balla kofar ta ki budewa.ba zainabu ba,ina zaton duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa amaryar tasa.fadi yake,ni zaki kawo wa rainin wayo don ubanki?yar matsiyata, ba za ki bude ba?ln kika bari na balla kofar nan na shigo,sai na karairaya ki,ko in sa a daure iyayenki har sai su biya ni abin da na kashe.lta dai zainabu jikinta sai bari yake yi,tana ta kuka.alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba.sai da ya bar gidan,uwargidan ta zo ta buga,ta ce,bude yarinya ni ce,shi ya fita. matar ta shiga dakin,tana kallon zainabu cikin tausayi,ta ce,ALLAH sarki, ashe yarinya ce karama.ke ko me ya kai ki auren alhaji?cikin kuka,zainabu ta ce dole aka yi min.kudi ya nuna wa iyayenalna da wanda nake so,yake so na.ta ce,amma iyayenki ba su bincika ba ne?ta ce ni fa ban san komai a kan auren nan ba.ta ce,kai iyaye da yawa suna yin kuskure.da zara sun ga kudi,sai su tura 'ya'yayensu kawai,babu bincike. zainabu cikin tsoro, ta ce don allah hajiya me yake yi?ta ce,ba komai,kar ki damu.shawarar da zan ba ki,kar ki sake rufe masa kofa.duk abin da ya ce,ki yi,kar ki ke yi masa gardama hakan zai fi miki alheri,ke da iyayenki.ln kuma kin ki,to zai tozarta ku gaba dayanku. zainabu cikin kuka ta ce,na shiga uku!hajiya to ke 'yar uwarsa ce?aa,ni ce matarsa ta farko.ya aure ni tun bashi da ko kwabo.

'yayana goma da shi. zainab ta zaro ido,dama yaransa goma ya boye min?ta ce,nawa ke nan kadai 'ya'yansa ashirin da biyar,banda masu ciki uku. zainab ta ce ban gane ba. matar alhaji ta ce,matan da ya saka goma cif.ta karshen tana da ciki.sai sauran matansa biyu,duk suna da ciki.zainabu ta sake rushewa da kuka,tare da cewa,ita dai za ta gudu. matar ta ce kar ki fara!zai sa a kama iyayenki,kuma ba zai sake su ba sai ran da ya ji an ce an ganki,kin dawo dakinsa, ta mike, bari in sa a kawo miki abin kari. zainabu ba ta ce aa ba,dm tana jin yunwa,rabonta da abinci tun jiya da safe.koko ne da kosai,duk sun huce,yarinyar da ta kawo za ta kusan saarta.zainabu dai haka ta tuttura. da rana lnna yalwa ta zo, aminiyar lnnarsu ce.zainbu cikin kuka ta fada mata komai.lnna yalwa,ta ce,da allah can, duk karya ta fada miki,kika kama.kishiya ce har za ta ce miki ga laifin miji,ki hau kai?zainabu ta ce,lnna yalwa gaske ne.ga shi nan jiya sai zagi na yake yi dana rufe masa kofar.jiya fa na zo gidan.ln da mutunci bai dace yayi hakan ba.
[01/10 9:45 pm] Abdul: Laifinki ne.yaya zaki rufe masa kofa?lna kika taba jin haka? bayan tafiyar lnna yalwa,ba jimawa yaran gidan suka cika mata daki, wanda gado ne kurum wanda alhaji ya sa mai kyau ne,amma da gani ba sabo ba ne.wadda ya aura nan dakin yake kawo ta.ln za ta tafi kuma ta bar masa gadonsa. ya shigo tana sallar magariba.ya zauna bakin gado,yana ta huci,sai ka ce kumurcin maciji.tsoro da fargaba suka hana ta idar da sallar.sai yi take tana sallamewa.ta sallame ta sake mikewa.ya finciko ta, ni za ki zo mawa da salon salla?magariba dai rakaa uku ce.kuma nafilar da na sani bayan magariba rakaa biyu ce,amma ke da na shigo kike ta zabga salla ko?cikin tsoro da kuka ta ce,aa baba ba haka ba ne. baba?ya tambaye ta,cikin fushi.kuka ta ci gaba da yi. ya kashe ta da mari,nine babanki?to,bari in nuna miki cewa ni mijinki ne,ba ubanki ba! da karfinsa ya yi amfani,ya raba ta da tufafinta,ya jefa ta kan gadon.duk 'yan gida da yara suna jin ihunta.da ma ya yi mata nata shiri na musamman.don kansa ya bar ta,ba don rokon da take masa ba,ko don wahalar da ta sha.ya bar ta yashe ba kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta. khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya. bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba dole ne mahaifinta ya ji alat.

Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad.
Chapter 5 · 0% Book details