Sashe 6
Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin in-ina ya ce,mene kika ce lnna?ta ce,zainabu ta yi aure.allah ya sa ba rabonka ba ce.kodayake laifinka ne. tunda baka kawo ko da sallama ba.lsma'il ya ce, inna don allah kar kiyi min haka.da shirina na zo.sai an sa bikinmu zan koma.ta ce assha!ai ka bar shiri tun rani yaro.tana gidan alhaji lawan.ba tare da jiran sake ji daga gare shi ba ta koma ciki. lsma'il ya tsuguna,ya dauki wayarsa jiki babu karfi,zuciyar na tafarfasa,ya nufi gidan yaya amina.da kyar ya kai. sai ganin mutum ta yi babu ko sallama.kan tabarmar da ya gani a shimfide ya zube zaune tare da dora kansa a guiwowinsa.cikin fargaba ta ce,lsma'il lafiya?ta tambaye shi fiye da sau biyar,ya dago kai da kyar ya ce,lafiya lau.ta ce ina fa lafiya,dube ka fa?me ke maka ciwo?ya girgiza kai, babu. ya sake dosa kansa a kan hannuwansa wadanda suke sarkafe a guiwowinsa.ya ce,yaya ashe zainabu ta yi aure?ta ce,au da ma damuwar ke nan?ta sake tausasa murya,ka yi hakuri.allah ya rubuta cewa zainabu ba matarka ba ce.nan ta shaida masa abin da ta ji game da auren. ya ce,mahmud bai kyauta min ba.me zai sa muna waya,amma yaki sanar da ni?ni na san da a ce ina nan ba yadda za a yi a raba ni da ita.sam mahmud bai cika alkawari ba,kuma bai rike min amana ba.yaya amina ta ce kar ka ga laifinsa,domin a boye duk aka yi komai.sai daurin aure aka ji.lsma'il ya sauke ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka zubo kan kumatunsa.ta ce,haba don allah lsma'il,sai ka ce ba namiji ba?kamar baka da ilimi.ka fa san komai mukaddari ne.ka yi hakuri,zainabu ba rabonka ba ce.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (7)Allah zai baka wadda ta fi ta komai.lsma'il ya ce,shi ke nan yaya na gode.ya ciro dubu uku daga aljihunsa, ga wannan yaya.ta amsa tana fadin, har da kudi haka.ya ce,ba yawa.lna ganin gobe ma zan juya kawai,da ma da kyar alhajin ya bari na taho. ta ce,haba dai ka dan kwana biyu mana?ya ce,aa ba zan iya zama a garin nan ba,ina tuna zainabu.lna bukatar cire ta daga raina. ya mike a kasalance,ya dauki ledar wayarsa ya ce,to ni sai na dawo.ta ce, ba zaka biyo ba gobe ke nan?ya ce sammako zan yi. da kyar ya isa gida.tunda ya bude kofarsa ya fada kan katifa,bayan rufe kofar ya soma kuka.shi kansa bai san yana tsananin son zainabu haka ba sai da ya rasa ta.ya yi kuka sosai,ya dangana,ya fita cikin dare yayi alwala.gurin allah ya yi ta kai kukansa.bukatarsa allah ya cire masa son zainabu,ya ba shi dangana ya sada shi da mafi alheri. daga bisani ya dauki alkurani,yana karantawa.