← Book details Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce
[01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan. shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa zai amsa su ba.

Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka?
[01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya fice.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi siyan mai.

Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala alhaji ya soma takawa,shi ma ya bi shi.ya waiwayo ya yi masa alama da kai. suna shiga alhaji ya kalli usaina, kira min MIMI.hajiya binta ta ce,alhaji wai me kake nufi ne?momy nafisa ta ce,kana nufin wannan ne mijin? usaina ta shiga ta same su da hasana ta ce,sis MIMI dad yana kira.da sauri ta mike,kanta babu dan kwali,ta fito a firgice.duk zatonta zai ce ta koma gidan mamanta ko gidan hajiya binta.tana fito ta kalle shi,ga ni dad.ya ce,ki shirya ga mijinki nan za ku wuce.ta zaro ido,tare da fadin dad me ka ce?na shiga uku!dan da nan sai kururuwa,ta zube kasa.su hajiya binta suka nufe ta, suka daga ta suna salati.

Momy nafisa tana fadin sam alhaji ba zai yiwu ba. tsaki ya ja,kar ki bata min rai nafisa.ku yayyafa mata ruwa ta farfado da wuri.ku hada mata komai nata, katsina ba nan ba ce.ya kalli lsmail,wanda tsabar firgici ya hana shi magana, ya ce,kai kuma daga yau na sallame ka daga aiki.
[01/10 10:34 pm] Abdul: (36)Kuka MIMI ta saka. momy nafisa ta shiga cewa, ai ni kuma na shiga uku,watan kuma nawa ne tunda na'ima ta auri abbas, amma ia na ga dai ita MIMIN ba son shi take yi ba. ta ja tsaki,ta fice fuu.su hasana ne suka shiga shirya wa MIMI kayanta na sawa da irin abin da ya danganci na karatu.tana ta kuka alhajin ya sake sawowa lokacin hamisu ya dawo.ya shiga har dakin MIMI ya ce,ta ba shi katinan ATM duka.ta ba shi tana kuka tana rokon sa.ya amshi duk wani abu da ya danganci dukiya. gwalagwalanta kuma hajiya sauda ta amsa. hasan suka ce hajiya da kin bar mata.ta ce,duk ku rufe min baki.suturun MIMI ma ba duka suka dibu ba.an dai cika duk akwatunanta. takalma da kayan shafa duk an diba.sai lokacin ta tuna da wayarta.jakarta kuma da kudi,ta kalli hasan, ina jakata?hasana ta fita falo ta dauko mata.sai ta tura ta cikin wata jakar bayan ta cire wayarta wada take a silent.miss call din khalil ya fi hamsin.kuka ta soma.a zuciyarta ta raya yanzun kam babu makawa za su gudu.
Chapter 13 · 0% Book details