← Book details Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Canjin Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kafin wani lokaci,salama ta sauka a zuciyarsa.sai da yayi sallar asubahi,ya soma jin barci. yana dawowa daga masallaci ya kwanta.ba shi ya farka ba sai goma saura. shi ma kwankwasa kofarsa aka yi ya farka.ya tashi da kyar ya zare sakatar.mahmud ne,don haka ya dawo ya zauna. mahmud ya shigo,shi ma ya zauna. lsma'il ya ba shi hannu suka gaisa.ya ce,na yi ta kiran wayarka a kashe. mahmud ya gyara zama.ina sane na kashe,domin bana so ka rike ni a ranka.na san dai zuwa yanzu kaji komai.lsma'il ya tsura ma bakin kofa ido,kamar mai kallon wani abu a gurin. mahmud ya ce,ka yi hakuri allah ya kaddara ba matarka ba ce.lsma'il ya ce,duk da haka mahmud,kai ma na ga laifinka.me zai sa ba ka kira ni ka fada min ba?na tabbata zainabu dole aka yi mata,don tana so na.mahmud ya ce,fada maka ba zai kare ka da komai ba.a lokacin da na samu labarin kwana kadan suka rage a daura aure. amma ka yi min afuwa.lsma'il ya ce,ni yanzu zan shirya in koma abuja.malam yana nan kuwa?mahmud ya ce,yana nan.na dai bar shi a gida. haba dai ka ce yau za ka koma?ya ce.tun jiya katsina ta fita daga raina.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (8)Mahmud ya ce,allah yasa hakan shine mafi alheri.amma ya kamata ka dan yi kwana biyu.lsma'il ya ce,in na zauna babu abin da zan yi.da a ce na san da wannan matsalar.lallai da ba zan zo ba.mahmud ya ce,shi ke nan allah ya kai ka lafiya.ko wanka lsmail bai yi ba,ya hada nasa-ya-nasa ya shiga cikin gida yin sallama.fatu ta ce, lsma'il sai ka ji batun auren zainabu.bai san lokacin da murmushi ya sauka a fuskarsa ba.ya ce,zainabu ta yi aure.fatana allah ya bata zaman lafiya.fatu ta yi 'yar dariya,ka dangana ke nan?bai tanka ta ba,ya wuce abinsa dakin lnna.ya shiga ya sanar mata cewa zai koma,ya kawo dubu biyu ya bata.ta amsa tana godiya.ta ce ko ka hadu da yan uwanka?ya ce mun gaisa da asuba a masallaci,amma ga wannan ki basu.ya mika mata dubu uku.ta ce,an gode.allah ya saka da alkhairan.sai kuma kaji wannan yarinyar da kake nema ta yi aure ko?ya ce eh na ji lnna.allah bai yi dani ba.ta ce,duk da haka ma sun so yaudararka ne.ka je ka amshi duk abin da ka san cewa naka ne,lna nufin wanda ka bata.ka kuma lssafa kudin da ka bata, tallar nan duk a amso su,ya ce,lnna a bar wannan maganar kawai.ban bata don in karba ba.ya mike,ya fito,ta ce,to shi kenan allah ya tsare hanya.nan su ma matan gidan ya basu dubu daya,ya dauki jakarsa.

Bayan ya ba mahmud dubu biyu,mahmud ya ce, kudin mene ne?ya ce,kudin albashina mana.dana yi niyyar gabatar da abubuwan aurena har zuwa a sa rana.amma tunda babu zancen,gara in yi alheri in samu lada. mahmud ya ce,na gode sosai.gidan su mahmud suka je,inda ya ba malam dubu uku.ya goya shi a mashin dinsa.har za su wuce tasha,ya ce,kodayake ka kai ni gidan alhaji bishir in gaisa da hajiya sauda.sai da suka je kofar gidan,ya kira layin hajiyar ya ce mata ga shi a waje,ta turo abdullahi suka shiga tare.lsmail bai boye mata komai ba game da MIMI na kin karatu ba.ya sanar da ita halin da yake ciki.ta ce,ba komai kar ya damu da batun MIMI tunda aure za ta yi.yanzu ya koma ya ci gaba da abin da yake yi,a kan zainabu kuma tace kar ya damu,
[01/10 9:45 pm] Abdul: (9)Kila ita din ba alheri ba ce a gare shi.ta ce,in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma lslamiyyar ya ce,shi ma tunaninsa ke nan a yanzu suka yi bankwana,bayan ta ba shi wani turare mai kamshi.ya fito mahmud ya kai shi tasha.bai samu motar abuja kai tsaye ba,don haka sai ya hau ta kaduna. suka miki hanya,zuciyarsa da rauni,bai san lokacin da zai warke ba. hajiyar mardiyya,matar alhaji lsa mani,abokin alhaji bishir ita ce ke kwada sallama a falon hajiya sauda.hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce,sannu da zuwa maman su nabila.ta ce,yawwa hasina,hajiya fa?ta ce,bari in duba ta.nan hajiyar mardiyya ta zauna kan kajera.hasina ta fito ta ce, tana wanka ne.hajiya mardiyya ta mike,bari in shiga cikin dakin.kawaye ne sosai,har yanzu ba su yada juna ba,don sun fi mazan nasu zumunci,har da matar alhaji kabiru,hajiya ramatu, abokansa na tun ana talakawa. kan gado ta zauna tana 'yan dube-dube. ke kullum aka zo dakinki kal,sai ka ce amarya.daidai lokacin ta fito tana cewa, me kika ce?hajiya mardiyya ta maimaita.sauda ta yi dariya,to ni ke gyra dakina da kaina.ku ko kun fi son na 'yan aiki.ta ce,to meye aikinsu in ba shara da wanke-wanke ba?sauda ta ce,ku dinga duba masu. kullum ina fada muku,suna yi kuna dubawa,kuma gyara musu. hajiya mardiyya ta ce,ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki baki fada min biki ba,sai dai in ji a gurin alhaji.hajiya sauda ta yi tsaki,kin san allah,ban san komai a kan bikin nan ba.ke in takaice miki,yanzu alhaji fushi yake yi da ni.hajiya mardiyya ta ce,a kan me?ta ce,kin san bata son auren,shi ke so.ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so.sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni?to ni shawara zan ba ta,tursasawa ba.kar ki dada,kar ki raga.daga wannan shine laifina.wai ni ce ke zuga ta.har yau bai sake ce min kala a kan bikin ba.na'ima take fada wa su hasana ta waya wai nafisa ta je dubai siyan kaya.an kawo lefe,an yi kaza,an yi kaza.
[01/10 9:45 pm] Abdul: (10)Hajiyar mardiyya ta ce, amma alhaji bai kyauta ba. ko da keke zuga ta.ai kamata yayi ya baki hakkinki na haihuwa.sauda ta ce,ni ma dai shi na gani. don haka nasa musu ido.ya maki zuwa garin nan sam. ko kira waya yayi.sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije. hajiya mardiyya ta ce, amma da kin yi masa magana da kanki,ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren 'yarki. sauda ta ce,kin san allah ba zan kula auren nan ba.kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga MIMI ba.mu je a na zuga tan.ita ma ba halin kirki gare ta ba.so nake su gane kurensu,dukkansu shi da ita.mardiyya ta ce,shi ke nan,allah ya kai mu.mu dai za muje biki.ln abuja din ne,in nan ne ma dai duk da mu za a yi,allah ya taimaka, in ji hajiya sauda.
Chapter 7 · 0% Book details