← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 11

Sashe 9

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shuraih dafatan ka gama duk wani shiri naka da zakai don zuwa garin bulzum"
Na gyada kai alaman eh
Maimartaba ya dubi wani ba'askare ya daga mai hannu,
Ba'askaren na ganin haka sai ya dauko wani jaka dake bayansa yazo ya aje a gaban sarki ,
Nasarudin ya kai hannu kan jakan ya bude yaa fiddo da wani bakin mulmulallen dutse,
,
Ya mikawa salman mulmulallen dutsen yace "kayi masa bayanin duk yadda zaiyi ya dasa makamin da yadda zaiyi ya tasheta"
,
Salman ya karbi mulmulallen dutsen sannan ya dubeni yace "shuraih"
Na amsa yayinda gabadaya hankalina ke ga mulmulallen dutsen wanda babu ko kwarzane a jikinsa sai yanzu na fahimci ashe dutsen din shine makamin da zanje na dasa a birnin Bulzum
,
"Izan ka isa birnin bulzum, sai ka samu wani waje ka dasa makamin, yadda zaka dasa kuwa shine izan ka fiddo makamin sai ka ajjiyeta a kasa ka hada mata wuta toh cikin dakika daya zata fashe, dukkan wani aljani dake wajen zai zama hayaki yabi iska, gidajen su kuwa da dukiyoyinsu zasu baje su zama Ruwa
**********
Ina tsaye cikin kwale kwale wacce zata sadani da birnin Bulzum ,
Wani aljani ne ya hakimce sai tuka kwale kwalen yake,
Akalla yanzu nakai sa'a daya da barin garin Lujaj
Na nufi garin bulzum
Shakka babu da nasan abun dake shirin faruwa dani toh da babu abunda zai sanya na bar garin lujaj
Wannan tafiyan da nayi itace
Tafiyar da ta wargaza mani farin ciki na,
,
Bana tunanin komai sai na haseena , yanzu kam na tabbata da gaske ne haseena bata kaunata duba ga yadda har na bar garin lujaj batayi mani magana ba,
,
"Bako mun iso" na tsinkayi muryan matukin kwalelen cikin kunnuwana
Sai asannan na lura da daina motsin da kwale kwalen tayi, ashe wai har mun iso bakin gaba
Na sauka daga cikin kwale kwalen ina mai kallon cikin dajin dake gabana,
"Kayi sauri ka dasa makamin ina nan ina jiranka"
,,
Na nufi cikin dajin gadan gadan batare dana bashi amsa ba,
Na yi tafiya mai dan karen nisa kafin na fara hango ganuwar birnin Bulzum, da taimakon Taswiran da Salman ya bani
,
Har na kariso birnin ban ci karo da wani Aljani ba,
Abun daya bani mamaki shine ganin babu wata kofa ko wani hanyar da za'a shiga birnin ta ciki,
, nan fa na fara zagaye birnin ina neman hanayar shiga, sai da na zagayeta kaf banga wata hanyar shiga ba hakan ne yasa nayi kudirin in kwana a bakin birnin kafin gobe da safe na sake neman hanyar shiga
,
Waje kawai na share nayi kwanciyata batare da fargabar komai ba, har dare ya tsala, toh a sannan ne naji saukan wani abu a jikina,
Cikin sauri na farka don ganin menene wannan
Anan na tsinci kaina a cikin RAGA, an nanna deni, wasu munanan askar na Aljanu suna jana a kas,
Banyi wani yunkurin kwatan kaina daga hannunsu ba ina kallo suna zuwa dani sai wani abun mamaki ya faru don kuwa wani banagarene daga katangan garin ya tsage da kanshi, nan suka jani muka shiga cikin garin din, muna wuce wa katangar ya hade kansa tamkar bai taba tsagewa ba,
,
Gaba daya Aljanun garin sai bina da kallo sukeyi yayinda nima nake kare masu kallo sama da kasa, tun danake ban taba arba da munanan Aljanu irin wayannan ba, domin kuwa ko acan birnin Lajuj a siffan mutane aljanu suke rayuwa,
Sai da muka zo wani fankacecen fili, wanda girmansa yakai eka dubu,
Sannan wayannan samudawan aljanun suka saki igiyoyin dake tattare da ragan dana ke ciki, sannan sukai tafiyansu,
Toh a sannan ne Rana ya fara gasani irin gashin da wuta yakewa dankali,
Kaina yafara amsawa, gaba dayan jikina ya jike sharkaf da gumi, sai a sannan na lalubo harshena daga cikin bakina na fara karanta ayoyin Alqur'ani mai girma
,
Ina fara karatunne naji jikina yayi sanyi tamkar wanda aka sanyashi cikin kankara, gaba daya ji nai na daina jin zafin ranan dayake damuna
Sai a sannan na tuna da wata guntuwar Wuka da salman ya bani lokacin da zan hawa kwale kwale
,
Na zaro wukan daga kubenta cikin zafin nama na hau ragar da yanka
Cikin kankanin lokaci nayi kaca kaca da ragar na fito na tsaya akan kafafuna,
Na lalubi aljihun wandona don jin haryanzu makamin da nasaruddin yabani yana nan,
Jin hannuna ya tabo wani kululun abu shi ya tabbatar mun da haryanzu makamin yana nan
,
Na falfala da azababben gudu domin na isa wani waje da muka wuce dazu naga ana kera takubba
Har na iso wajen kiran askarawan birnin basu ankare dani ba,
Aljanun dake kera takubban suka daga kawunansu suna kallona mamaki dauke akan fuskokinsu, kafin wani daga cikinsu ya mike tsaye, ya nufoni hannunsa rike da makekiyan barandami na tsaya ina kallonsa cikin kota kwana,
Yana isowa dab dani ya kawo mani sara da barandamin dake hannunsa duk yadda nayi don na kaucewa saran nayi, amma sai da ya samu nasaran yankana a dantse wajen ya dare jini ya fara kwarara,
Ina ganin haka na daka tsalle na dira akan wuyansa kafin yayi kokarin bambareni har na murda mashi kai nan take ya fadi akasa matacce
,
Yanuwansa suka tashi kowannensu yana rike da takobi a hannunsa,
Nan fa suka far mani, suna masu kawo mani sara da suka , ni kuma na wanzu ina mai zullewa da gocewa kaifin takubbansu, a na hakane na hango wasu askarawa masu tsananin yawa sun dumfaro inda muke wannan artabu,
Nan hankalina ya tashi, na ga muddin askarawannan suka kariso toh kashina ya buushe, ina gama ayyana haka a zuciyata sai nayi sauri na fidda makaminnan daga aljihuna, na falfala da gudu, izuwa cikin makeran
Ina zuwa bakin wani murhu inda naga garwashin wuta sai na jefa makamin a ciki,
Da jefawata sai makamin ya bada wata kara Fus alaman fashewansa,
.
Wani hayakine ya ziyarci idanuwana wanda ya sanya na fara gani dishi dishi,
Bansan me ke faruwa ba sai tsintar kaina nayi a cikin wani kungurmun daji, na dubi dajin dakyau sai naga ashe dai wajennan ne da haseena ta kawoni aka koyamin fada,
,
Na nufi wani bangare da zai sada ni da sansanin tsoho zaikid,
Haryanzu hannuna yana yimin zogi da tsananin zafi, na daiyi nasaran tsaida zuban jinin ta hanyar daure wajen
Ina cikin tafiyanne sai naji kaman wani abu nayimin yawo cikin aljihun wando, na zura hannuna cikin aljihun cikin mamaki sai ji nai hannuna ya tabo mani wani takarda
,
Na damki takardan sannan na ciro hannuna don ganin takardar menene
,
Abun da naci karo da shi a rubuce a bayan takardan shi ya haddasa wani girgizan kasa cikin zuciyata
Daga Haseena Masoyiyarka
,
Zuciyata na zumudi na bude takardar na fara karantawa kamar haka
"Assalam masoyina shuraih kuma gwarzona,
Nasan cewa kallon mayaudariya kake yimin, gani kake tamkar yaudaranka nayi
Kasani cewa tunda nake a doron duniya babu wani namijin dana taba jin sonsa in banda kai,
Alokacin dana fara ganinka, sai da zuciyata ta buga, ina matukar farin ciki da nishadi aduk lokacin dana ke tare da kai, duk da nasan na bata maka amma kayi hakuri ina sonka so na gaskiya
Allah yabaka sa'a a wannan tafiya da zakayi yakuma dawo dakai gareni lafiya"
Tsaban dadin danaji ya ziyarci zuciyana yasa na kurma ihu, ina fadin alhamdulillah,
A haka har na iso bakin bukkar tsoho zaikid,
Na sameshi a zaune kan wasu itatukan da muka sassaka a tare a matsayin kujeran zama,
,
Sam baiyi mamaki da ganina ba sai ma gani nake tamkar ya san da zuwana,
Nayi masa sallama ya amsa cikin tausasa murya
Cikin farin ciki na dubeshi nace "baba " sunan dana ke kiransa da shi kenan
"So nake ka maidani garinsu haseena "
Ina fadin haka sai naga kwalla ta gangaro daga fuskan tsohon ganin hakan ya rikita ni ainun
Na matso ina mai tambayarsa" me ya faru ne baba"
,
"Haseena,nasaruddin da dukkan ilahirin Aljanun da suke birnin lajuj sun HALAKA"
Abunda bakin tsohon ya furta kenan
,
Kirjina ya buga dumm gabana ya fadi Na dubeshi cikin rashin fahimtar inda zancensa ya nufa nace "kaman yaya sun halaka baba, nifa ban gane zancenkannan ba"
,
"Shuraih su Nasaruddin sunyi kuskure babba, wajen amfani da wannan makamin don hallaka birnin Bulzum, tabbas da sun san illan da makamin zaiyi masu toh da basu kwatanta amfani da shi ba gashi yanzu dukkansu sun hallaka birninsu ruwa ya mamayeshi"
Tsoho zaikid ya fada yana mai tashi tsaye kafin ya cigaba
"A ka'idan wannan makamin guda daya ake sana'antawa, in angama amfani da shi sai a sake sana'anta wani,
Amma su nasaruddin sun sana'anta guda uku daga cikin ukunne suka baka daya kaje ka tayar a birnin bulzum abunda basu sani ba shine, muddin aka tayar da makamin ya gama aikinsa sai hayakinsa ya bazu a duniya a duk inda yaci karo da irin makamin sai ya tayar da shi, toh hakanne ya faru bayan ka tayar da daya a birnin Bulzum daya gama hallaka mutanen birnin sai hayakinsa yabi iska ya je har birnin lujaj ya kuma ci karo da irin makamin hakanne yasa ya taada su, toh kaji kuskuren da su nasarudden sukayi, sai ka shirya na mayar dakai duniyarku"
Ya karashe maganar yana mai nufan bukkansa
,
Daskare nake a tsaye tamkar gunki, numfashina ya tsaya cak, inbanda bugun da zuciyata take sai ka rantse gunki ne ni
,
Tsaban rudewa ne ko tsaban firgici,
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 11
.
Chapter 9 · 0% Book details