← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 11

Sashe 4

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

duniya ban taba ganin dan Adam lokaci daya naji sonsa ba saikai, hakan nema yasa yau dinnan zan fada maka sirrin dake tattare dani ina sonka shuraih so ,kuma ina muradin zama abokiyyar zamarka na duniya da lahira, Jina nake tamkar wanda akaiwa kyautar Aljanna domin kuwa a wannan lokaci na tabbata babu wanda yakaini farin ciki "Haseena kiyi sani cewa nima ina sonki , kuma babu abunda bazan ma don na mallakeki, nasan cewa kina shakkun wannan gasa ta fidda gwani ne, toh ki sani muddin akan ki ne sai de na mutu awannan gasa don kuwa bazan bari wani daban ya sameki ba, ki kudurta a zuciyanki nine mijinki" Hannu ta saka ta dauki wani tuffa ta mai gaza daya, har zata kai na biyu sai nayi sauri na karbi tuffan daga hannunta ina mai yimata wani irin murmushi na zolaya, sannan nima na gaza daidai wajen da ta gaza Anan muka luluka izuwa duniyar soyayya domin kuwa hira muka shiga yi sosai yadda take bani labarin garinsu, sosai naji dadin wannan lokaci . Muna tsaka da hiran ne wani lokacin izan ta fadi abun dariya sai mu dara , wata kakkausar murya ce ta katse mu da fadin "BUDURWAN SIRRI bata bil'adama bace, . Dukkanmu muka juya don ganin mamallakin wannan murya,,,,,, . www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Gajeran labari Marubuci Shuraih Usman @hausaebooks page @shuraih 99% Page 6 . Gabjejen katone mai kirar mutanen farko yana da tsayi wanda na tabbata yayi ni Uku a tsayi don sai dana daga wuyana sannan nai nasarar ganin Fuskarsa a turbune fuskar yake babu alaman murmushi ko kadan a tare da shi, kwayan idanunsa jane, gashin kasumba ya rufe mai baki yayin da ya hade da gashin gemunsa wanda ya zura ma wani zobe ya kulle . Yana sanye da riga falmara mara hannu hakan yasa na samu nasarar ganin kwanjinshi, gaba daya jikinsa a mummurde yake, ga jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdum burdum kai kace igiyace . Hannunsa na dama yana rike da gashin gemunsa wanda ya rike daidai wajen da ya zura zoben yana dan liliyawa ,fuskarsa na yatsinewa wanda shi a zatonsa murmushi yake, Shi ba mummuna ba haka kuma shi ba kyakyawa ba, amma kallo daya kadai nai masa na gane cewa wannan dakare ne, domin kuwa akuibin cinyoyinsa hagu da dama akwai wasu takubba manya manya cikin kufensu , wayanda na tabbata in aka ce na daga daya cikinsu bazan iyaba . Cikin firgita da tsoro na saki baki galala ina kallonshi har ya kariso garemu, Abun daya daure mani kai shine sam babu alamun firgici a fuskar haseena A zuciyata nace yo ta ina zata firgita bayan itama yar uwarsu ce, na sake maimaita wannan suna da naji ya kira haseena da shi a cikin zuciyata BUDURWAN SIRRI . Yana tafiya takubban dake jikinsa suna dan kara sakamakon yadda yake tafiyar din . Ya kariso wajen da muke zaune Neman waje yayi ya zauna sannan ya harde kafafuwa irin zaman da yayi sai ya tuna mani da lokacin da nake makarantan Allo, fuska cikin fuska ya dubeni sannan ya takarkare da mahaukacin dariya mai matukar amo, ba shiri na sanya yan yatsuna na toshe kunnuwana sakamakon yadda naji dodon kunena na neman agaji . Sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya dubi haseena yace "Budurwan sirri, wai dama wannan dan tsakon ki ka je kika samo, ai nayi mai girma ina laifin ki samo dai dani, " Ya nuna ni da yatsa batare daya kalleni ba sannan yacigab da magana da muryansa mai kama dana jaki "Ina mai tabbatar maki da cewa nine zan aureki ,kuma nine nan zan lashe wannan gasa wacce zamu kara wata mai zuwa ni da wannan dan kwaron " . Duk da cewa ina jin tsoron wannan basamuden aljani wanda bansan sunansa ba , ai koda naji irin kalaman dayake furtawa ga haseena sai na fahimci cewa shine SALMAN, nan take na nemi tsoron dana ke mai na rasa cikin kunan rai na daka masa tsawa "Kai Aljan mutun bisa kanka, girman jiki bashi bane ke nuna cewa mutun yana da karfi, to kayi sani nidin dai daka raina da yardar Allah sai na baka mamaki" ai sai dana gama furta maganar sannan nayi nadamar furtawa Domin kuwa alokacin fuskar aljani salman ta yamutse , yadda kasan an aiko masa da sakon mutuwa, . Badon ina da dauriya ba da babu abunda zai hana ban tsiyayo fitsari ba kasancewar irin kallon danaga yana yimin Cikin kunan zuciya ya daga girjejen hannunsa mai kama da tabarya da nufin ya zabga min mari, rufe idanuwa na nayi don kuwa nasan babu makawa zai aikata, ko kadan banyi kokarin kare kaina ba ta hanyar rufe fuskata don nasan muddin hannunsa ya taba jikina to take zan baje a kasa sumamme ko matacce . Cikin sauri haseena ta daka masa tsawa wanda ya sanya shi tsayawa cak tace "salman izan ba kana son kaaga fushina bane toh ka gaggauta barin wajennan , in kuwa ba haka toh zakayi daana sani wanda ba zai maka Amafani ba, " cike nake da tsoro kamar ace kyat na ruga na dubeshi a yayin da ya dunqule hannunsa ya naushi kasa , a hassale ya tashi sa'annan a dubeni yace "ka shirya nan da wata daya bil'adama maza bisa kanka," yana gama fadin hakan sai naga manyan fuka fukai guda biyu sun fito daga bayansa cikin kankanin lokaci ya tashi sama ya luluka cikin gajimare Na dawo da dubana ga haseena tambayoyi fal bakina . Murmushi tai min wanda shine ya mantar da ni dukkan wannan tambayoyi dana ke shirin jera mata su Tace "nasan ka tsorata da Al'amarin Salman amma karkadamu akwai wanda zan kaika wajensa ya koyar dakai fada da kuma yaki" . "Toh" kawai bakina ya samu fadi a yayin da muka cigaba da hirarmu in ka ganmu sai ka rantse mun yi shekaru da ita, na saki jiki sai zuba zance nake
Chapter 4 · 0% Book details