← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 11

Sashe 6

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har magriba ta gabato banga alamar tsohon nan zai fito ba hakan ya sani ta shi na kwankwasa kofan bukkar daga ciki muryan tsohon naji yace "ya akayi ne"
"Yun wa nake ji ,kuma gashi dare ya fara yi baka bani makwanci ba" na fada
Sautin dariyarsa naji alamar dariya yakeyi
"In tambayeka mana" ya fada
"Ina jinka "na bashi amsa
"A rana sau nawa kake cin abunci"
"Sau uku"
"Toh daga yau ka sanya a ranka kuma a jikinka baza ka sake cin abinci ba sai bayan kwana daya,kuma ka sani baka da abunci sai yayan itace"
Sosai na girgiza da jin batun tsohonnan
"To shi kuma makwanci fa"
"A nan zaka runga kwana kuma ka tabbata asubar fari ka farka yanzu dai ga ruwa kayi alwala kai sallah," ya jefo min wani batta na ruwa
Na karba nai alwala nai sallah daga nan na zube wajen durkushe duk da yanayin wajen yana da kyau kuma ko kadan babu kwari ko wasu muggan dabbobi masu cutarwa a cikin dajin domin kuwa tunda muka shigo dajin kawo izuwa yanzu bamuyi gamo da wani abu mai rai ba
.
Haka na kwanta akasa kan ciyayin dajin masu tsananin laushi duk da ya kasance ina rawar dari saboda sanyi da nake ji, bai hana bacci daukata
Ba
.
A fiirgice na farka sakamakon jin an kwara min ruwa da nayi waige waige na fara yi don ganin mahalukin daya kwara min ruwa dan tsakurkurin tsohon ne dai a gabana ya bata rai yana rike da wasu mayan mangala guda biyu
Ya ce"shin jiya ban sanar dakai cewa asuban farko taimaka a farke ba, shine ka shagala har asuba ta biyu baka tashi ba"
Bai jira cewana ba ya jefo mani mangalolin nan masu dan karen nauyi da kyar na iya cafe guda daga cikinsu
Yacigaba "maza maza ka tashi ka tafi wancan kogin yai nuni da hannunsa zuwa wani gefe dabam, ka debo ruwa ka runga zubawa anan ya nuna mani wata katuwar rijiya wadda tun zuwana wajen ban lura da ita ba
.
A kasale na tashi na rarumi mangalalolin na nufi inda ya nuna mani nayi tafiya mai dan karen nisa kafin na iso bakin koramar na zauna kan daya daga cikin mangalolin nan ina hutawa bayan nagama hutun ne na cika mangala daya da ruwa sannan na kinkimeta da kyar da sidin goshi na dorata akaina irin nauyin danaji akaina yafi kama da na Mota ko wani katon dutse a daddafe da kuma ikon Allah har nakai bakin rijiyar na zuba ruwan na sake komawa rafin kai in takaice maku sai wajejen la'asar na idda kai ashirin din daya ce na zuba, na samu waje na baje a kasa ina numfashi sama sama alamar na jikkata naji karar budewan bukkar tsohon ya zo ya tsaya daidai gabana sannan ya bushe da dariya yace "kai amma bil'adama da ragwanta suke yanzu wai dan wannan aikin shine har da numfarfashi sai kace wanda yai aikin azo a gani, maza ka mike tsaye"
A daddafe na mike tsaye don kuwa tun da nake a rayuwata ban taba yin wani aiki mai wahala daya kai wannan ba
.
Yanzu kam da sauki tunda dai na dan rage nishin da nake tsoho zaikid ya shige cikin bukkarsa yadan dau lokaci kafin ya fito rike da sanduna guda biyu, sandunan dogayene sosai don kuwa sunyi tsayina biyu
Ya jefo mani guda daya duk yanda naso na cafe ta amma na gagara saboda irin saurin zuwan da tayi sai gashi sandan ta wuce ni tamkar walkiya , ta sauka nisa dani tsoho zaikid yayi murmushi "
Maza kaje ka daukota"
Ba musu na nufi wajen da sandar take ina zuwa na sanya hannuna da nufin na rabata da kasa amma sai wani nauyi ya ziyarci hannuna ji nai tamkar na ina kokarin daga katon dutsene na daddage na tara karfina har ina nishi na daga sandan daga kasa na kafata tsaye , sai nishi nake haka na fara jan sandan a kasa har na kawota wajen tsoho zaikid,
"Da alama wannan tayi ma nauyi toh bani ita ka amshi tawa"
Ya karfi wannan daya bani ya kuma mika mani nashi da sauri na karfa don dama ni nasan kuskure yayi wanda ya kamata ya bani shike hannunsa , ai mugun nauyin danaji shi yasa na saki sandar ta fadi a kasa don kuwa hartafi waccan dinma nauyi tsoho zaikid yai kasake yana kallona kafin yace "muddin zaka runga yimasu irin wannan daukan toh baza ka taba iya rike koda daya daga cikinsu ba"
"Yaya kake so na dauka toh"
"Kasanya a ranka cewa zaka iya , sannan kana nan ne kawai don BUDURWAN SIRRI, haka kuma ka cire tunanin duniyarku daga ranka ka dauka tamkar a gidanka kake, sannan ka tausasa zuciyarka, a natse zaka ji mamaki ainun don kuwa ba wannan sandan ba hatta wancan tsaunin zaka iya yin gamo a dora maka shi"
Nai kasake ina kallonsa yayin da na kalli tsaunin daya ke nuna mani a zuciyana nace "toh ko nine ILYA DAN MAI KARFI sai haka"
.
Na nufi sandan nayi tamkar yadda yafada na rufe idanuwana na shafi sandan da hannuna na kama na daga cikin matukar mamaki sai naji tamkar na dau fallen takarda don kuwa ko kadan sandan bata da nauyi yanzu na juya na dube shi yai mani murmushi yace "shin yanzu ka yarda da magana ta"
"Shakka babu na yarda"
Daga nan ya fuskanceni yace "daga yau zamu fara darasin mu na koyan fada , da kuma yadda zaka kare kanka,
.
Ya koyar dani abubuwa da dama a wannan rana don kuwa in ba sallah ba babu abunda yake tsaida mu, da shike ina da saurin daukan abubuwa , har magariba tayi ya ce mani "je kai sallah ka kwanta kuma gobe ka tabbatar kafin safiya ka gama diba ruwanka nai godiya sannan nai wucewata izuwa inda na kwanta jiya
*******
Kwanaki suna ta wucewa tamkar yadda takarda ke zukar ruwan biro yau saura kwana daya wata daya ta cika,
A cikin wayannan kwanakin na koyi a bubuwa da dama, dun kuwa ji nake babu wanda ba zan iya tunkara ba yanzu batun tsoro kuwa babu ita ,
Tunda kuwa ni da kaina nake fada da manyan zakuna da kadoji kuma na kai su kar
.
Shi kansa tsoho zaikid yana mamaki ainun da saurin daukan fada na, kaman kullum yauma muna filin koyon fadanmu ni da tsoho zaikid sai fafatawa muke in ka ganmu a lokacin sai ka rantse wasu a bokan gaba ne domin kuwa kowannenmu burinsa shine yaga ya cutar da dan uwansa, ni dai na dage sai kare hare haren tsoho zaikid nake wanda shi kuma ya kufula ainun ganin sam bana kawo hari, sai da muka shafe wasu sa'o'I kafin ya samu nasarar buguna da sanda akafa nan take kafana ta gurde amma saboda juriya irin nawa sai na dake na kama kafar na murda ta sai ta dawo dai,a lokacinne na fusata na fara kaimai hari ba kakkautawa kan kace kwabo sai ga tsoho zaikid a kasa wanwar sakamakon bugunsa da nayi da sanda akansa
.
A gigice na nufeshi na tallabo kansa ina mai bashi hakuri yayi murmushi sannan yace "lallai na yarda yanzu kam ka kawo karfi ina son ka shiryaa don kuwa gobe BUDURWaN SIRRI zata zo ta dauke ka"
Na gyada mai kai ina susa keyana
*******
Washe gari tunda sassafe na iddar da debo ruwana don kuwa yanzu ji naake tamkar zan iya diba kai dubu ma,
Nai sallah sannan na taho kofan bukkan tsoho zaikid na tsaya ina nan tsaye a wajen har gari ya waye,
Tsoho zaikid ya fito daga bukkar hannunsa rike da sanda guda, na dubesa da mamaki don kuwa a kullum da sanduna biyu yake fitowa ya zauna kusa dani yace "shuraih ka tashi lafiya"
"Lafiya lau"
Daga haka ban sake magana ba
Kaman a mafarki sai naji muryan haseena tana gaida tsoho zaikid na dago kai na dubeta da mamaki don kuwa shi kansa zaikid bai san lokacin da ta zo ba iyaka dai jin muryanta yai har kasa ya rissina ya gaiisheta sannan ya nuna ni da hannu yace "ranki shi dade yanzu matsoraci kuma ragon bakon ki ya juya izuwa jarumin saudauki wanda sam baya jin tsoron komai gaba dayan tsoronsa sun juya izuwa naciya da juriya"
Tai murmushi wanda ya sake fitta kyawunta ta matso kusa dani ta kama hannuna da mamaki sai naga hawaye akan idanunta
"Shuraih kayi hakri nasan cewa na cuci rayuwarka na sanyaka a kunci sakamakon son zuciya da sonkaina, kana zaman zamanka a duniyarku na daukoka na kawo ka nan gashi yau a kaina ka...."
Na yi sauri na dora hannuna na rufe mata baki sannan nace "yana daga cikin rukunan imani yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, wannan mukaddari ne bayin ki bane kuma ki sani muddin ina numfashi a doron kasa ba makawa sai na aureki bana tsoron mutum bare Aljan, ni kawai abunda nake bukata dake yanzu shine mu tafi izuwa filin wannan gasa domin na nuna ma salman cewa DAN ADAM HATSABIBI NE,
Babu abunda baya sarrafawa komai girmanta koya takai da cutarwa"
Chapter 6 · 0% Book details