← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 11

Sashe 10

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

,
Dukkan wani na'uran sadarwa na jikina ya dena aiki, ahankali a hankali, kwalkwata tafara kawo wuta,
Tunanina ya fara dawowa,
"INna lillahi wa inna ilaihir raji'unn" shine kalman da bakina keta faman furtawa,
Na durkushe a kasa, yayinda kaina ke tsananin sara min,
"Haseena! Haseena!!" Sunan da nake ambato kenan har na bingire a wajen a sume,
*********
"Shuraih ina sonka ba zan taba Rabuwa dakai ba, me rabani da kai sai mutu...."
Nayi sauri na sanya tafin hannuna na rufe mata baki
"Ina fatan ko a Rayuwana bayan mutuwa na kasance dake, haseena"
,
Haseena kwance akan kafadana yayinda ni kuma nake shafa gashin kanta,
Ta janye jikinta daga nawa sannan ta mike tsaye, ahankali ta fara tafiya tana miko mani hannu alaman na riketa, cikin zafin nama na mike na nufeta da dukkan kuzarina domin na riqe hannunta,
Murmushi kawai take mani tana tafiya da baya, fuskarta na dubana,
Hankalina bai sake tashi ba sai a lokacin da na hangi a bun dake gabanta,
Wawakeken Rami ne, a gaban haseena wanda muddin ta kara gaba kadan toh zata fada,
,
Na sake kara karfin guduna domin na cimmata na rike mata hannu don kada ta fada cikin Ramin,
Amma sai naji kaman ana rikeni ta baya gudu nake sosai amma gani nake tamkar ina gudu ne a cikin Kogi,
,
kamu daya kacal ya rage na cafke hannun haseena, hakan yasa na daka salle nayi sufa ,
Alokacin ne kafarta daya ta fada cikin ramin nayi nasara hannuna ya taba nata kafin gaba dayan jikinta su dulmuya cikin wawakeken Ramin
,
"Haseena!haseena"
Firgigit na farka , ina mai sake kiran sunan nata a fili "haseena"
"Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun" na fada a fili yayinda nayi arba da abun da ya kusan zauta ni,
Kwance nake a kan tangamemen lallausan kujeran dake girke a cikin daki
.
Dube dube da kalle kallen dakin dana tsinci kaina a ciki nake,
.
Kamar yadda dakin yake a baya kuma yadda na barsa, babu abunda ya canja
Ina kwance akan dogon kujeran dake girke a cikin dakin, Dakina ne dana kwanta kwanakin baya, na farka na ganni a cikin dokar daji,
,
Karin tarin mamakina bai karu ba saida na kai dubana ga kayan dake sanye a jikina, kayan dana kwanta da su ne, a lokacin da na fito wajen Abasu kala don ya bani wayata,
,
Tunanika da yawa suka antayo mani a lokaci daya, anya ba mafarki nayi ba kuwa, kai tabbas wannan mafarkine , yo Im ba mafarki ba dama nasan babu ta yadda za'ayi wannan abu yafaru da gaske, ace wai daga kwanciyata a dakina na farka na tsinci kaina cikin dokan daji,
.
Nayi murmushi sannan nayi hamdala, yayin da dukkan tunanina ya raja'a akan dukkan wani labarin BUDURWAN SIRRI mafarki ne, addu'a na fara karaantawa lokacin dana mike na nufi kofan fita daga dakin
,
Na kama mabudin kofan na murza na yunkura da nufin na janyo kofan,
Jinayi an turo kofan da karfi, hakan yasa na dan ja baya don ganin mahalukin dayake shirin shigowa cikin dakin,
,
Tunanina ya hasko min Ganina na farko da haseena acikin mafarkina dana yi, bansan lokacin da lebbana suka saki tausasan murmushi ba,
,
Abasu kala ne ya shigo cikin dakin,
Yana sanye da bakar riga, wanda ake kira da jagaban, sai blue din jeans wandda aka yayyanka wani sashe na jikinta , da sunan Crazy, sabon style
,
"99%" ya fada yayin daya bani hannu muka tafa
Cikin dariyan shekiyanci ya miko mani wayana, na sanya hannu zan karfa kenan sai naga ya zabura yayi baya,
Walwala da annurin da fuskarsa ke dauke da ita ta juye izuwa tsoro da tsaban firgici
Yayi nuni da hannunsa izuwa jikina yana cemin"99 menene haka ya ji maka rauni a dantse, dubi yadda jini ya bata maka riga"
Nima cikin mamakin maganarsa na dubi dantsen haguna saide banga komai ba,
Na sake juyo da dubana ga dantsen damana toh a sannan ne hankalina ya tashi, sakamakon abunda idanuna yaci karo da shi
,
In har ban manta ba, wannan rauni anyi mani shine a garin Bulzum, kuma wannan al'amari ya farune cikin mafarki,
Toh wai dama in har abu ya faru dakai a mafarki, kuma ka farka wannan abu zai kasance a jikinka?? Na tambayi kaina
Tambayar da bansan amsarta ba,
,
Na kai hannuna na taba wajen,
Ihu mai karfi na saki sakamakon wani radadi daya ziyarci hannun
,
Karar ihun ne ya ankarar da mutanen Gidanmu akan halin dana ke ciki,
Cikin sauri suka shigo dakin,
Dukkansu sun firgita da halin da suka tsince ni a ciki,
na yi kokari da taimakon Abasu kala na cire doguwar rigan dake jikina,
Cire rigan keda wuya sai naji mutanen da suka shigo dakin suna salati suna salallami
,
Ban san akan me suke salatin ba amma tunanina yabani kodai suna mamakin yadda akayi har naji wannan babban rauni ne,
"Shuraihu wayannan tabon da suke bayanka na menene, yaya akayi har kaji wayannan tabobin??"
Na tsinkayi muryan mahaifiyana tana tambayana
,
Salati nayi kafin mahangar tunanina ya hango mani ta yadda akayi har na samu wayannan tabon,
Alokacin da tsoho zaikid yake koya mani fada yakan ji mani rauni a jikina,
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" na fada a fili
Mafarki na neman ya zama gaskiya akaina
Abun daya faru dani a mafarki na farka na ganshi a jikina,
Anya kuwa wannan mafarkine, tun da nake a rayuwata ban taba jin wani labari makamanciyar nawa ba, wai ace kayi mafarki kaji rauni, kuma ka farka ka ganka dauke da raunin,
Anya mafarkine nayi kuwa,????
.
Tambaya
Mafarkine ko Gaske
.
Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta
Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,,
Its 99% awakening from three 3 days sickness
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 12
.
........
Bayan Wata Uku
*
"Shuraih!! Shuraih!!! Ka tashi dare yayi fa"
Na tsinkayi muryan abokina Abdulhamid a cikin kunnuwana,
Na mike cikin magagin bacci nace "karfe nawa yanzu"
"Goma da rabi ne yanzu"
Ya bani amsa
Da saauri na mike tsaye, cikin kankanin lokaci na wartsake daga magagin baccin dake dibana,
Na zuri takalmina na fice daga dakin
Abdulhamid ya bini da gudu yana mai kiran sunana,
"Shuraih ka tsaya mana baka ga garin akwai hadari bane, kuma kafin ka kai gida ruwa ya tsinke,"
Na danyi nazari kadan kafin na jijjiga kaina nace
"Ai gwara ruwan ya tareni a hanya akan na tsaya har shabiyun dare yai mun anan angwan naku"
"Toh Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen " nace sannan na cigaba da tafiyana
,
Darene mai dauke nannauyan hadari wanda akowani lokaci ruwan dake tattare dashi na iya zubowa, in banda hayaniyan mutani, da karan wucewan iska, babu abunda kake ji a angwan,
Karar aradu ne ya ziyarci kunnuwana wanda hakan ya sanya na kwararo addu'o'i
,
Ina tafiyanne sauri sauri gudu gudu, na matsu na ganni a kofan gidanmu, sabida bana son wannan ruwa ya riskeni akan hanya, duba ga yadda naga ban dade da dawowa daga asibiti ba,
'
Tunanin abubuwan da suka faru a baya ne suka fara dawo min cikin kwalkwata tamkar a majigi (video), nayi murmushi a sa'an da hoton surar haseena suka baiyana cikin kwalkwata,
Yau watanni uku kenan, tun bayan lokacin dana hadu da haseena a cikin wata rayuwa wadda na kira da mafarki, hakan ya janyo mani abubuwa da yawa, ciki kuwa har da daukana da akai a matsayin mahaukaci, sakamakon labarin dana sanar ma iyayena,
Wannan yasa suka tarkatani sukai asibitin kwalkwalwa dani, watanni na uku acan ina karban magani da Allurai, babu yadda banyi ba dun na ganar da iyayena cewa ina cikin hankalina amma abu ya faskara,
,
A shekaran jiya ne aka sallamoni daga asibitin kwalkwalwa,
Na saki murmushin kuna lokacin dana tuna wanda ya makala mani hauka,
"Shuraih anya kana cikin hankalinka kuwa, taya za'a yi wannan abu ya faru a rayuwan zaahiri,sai kace wani wasan kwaikwayo (film)"
Na tuna lokacin da mujahid ke fadin haka a gaban iyayena yayin dana basu labarin duk abunda ya faru dani da yadda akayi har naji ciwo a dantsena
"Da gaske nake wallahi babu karya a cikin labarin dana baku" nafada ina kokarin baiyana masu gaskiyana
"Baba ya kamata mukaisa asibitin kwalkwalwa su dubasa bana tunanin yana cikin hayyacinsa"
Mujahid ya fadi yana duban mahaifina
"Toh naji amma kafinnan bari mudan fara dana gargajiya tukun,ko ya kuka gani" mahaifina ya fadi yana dubansu
,
In gajarce maku sanda aka gaiyato malamai sunkai Goma sukai saukan qur'ani a gidanmu, maganin gargajiya kuwa babu iriyar wacce ba'a dankara mani ba, tun ina bi a hankali inayi masu bayanin cewa nifa lafiyana kalau, har takai sun tunzurani wata rana na kama wani mai magani da aka kawosa wai ya bani magani na lakada masa dukan tsiya,
,
Toh a sannan ne aka wuce dani asibitin kwalkwalwa, ko kuma ince asibitin mahaukata
,,,
Barkewan da ruwaan saman yayi tamkar da bakin kwarya shi ya sanya na fara gudu, ina neman mafaka, cikin wani lungu nake wanda ma ban gama sanin hanyan ba,
,
Gani da nayi ruwan na neman ya kara karfi bisa kan na da, ya sa na fara tikan gudu, banyi nisa da gudun ba Ruwan saman ya fara saukowa da karfi,
,
Nayi tunanin muddin na cigaba da tafiya cikin ruwannan zan iya kamuwa da mura, ko zazzabi
Sai a sannan nayi dana sanin zuwana angwan Tofa wajen Abdulhamid,
,
Na fara waige waige ko zanga wani mafaka don in samu in fake har sai an iddar da ruwan , sannan inyi tafiyata
,
Wani Zaure na hango daga nisa kadan da ni,
Batare da na tsaya yanke wani shawara ba na afka cikin zauren da gudu,
Shakka babu da nasan abun da zai biyo bayan shigana cikin zauren da banyi, kwadayin shiga ba
Shakka babu da nasan cewa shiga na cikin zauren zai tono wani babban rauni a zuciyata ya kuma sake bude wani sabon babin Rayuwan mafarki a rayuwata, da banyi gangancin shiga ba
,
Ina tsaye a cikin zauren yayin da ruwa keta kwarowa a waje,sautin karan zuban ruwa a rufin gidajen jama'a shi kadai ne abun da jama'a ke iya saurara,
,
Zauren yana hadene da Gida saide kofan gidan a kulle yake ta ciki saboda yadda naga babu kwado a jikin kofan,
,
Na dau lokaci a tsaye a cikin zauren, yanzu kam an dan sarara da ruwan, sai de dan yayyafi da ake yi, wannan yasa na fara himman wucewa gida,
Har na yuunkura da niyyar in mike daga tsugunon danayi, sai naji ana kiciniyar bude kofan Gidan
,
Na tattara hankalina gaba daya ga kofan don ganin wanda zai fito,
Duk da darene amma ina ganin komai shar shar da taimakon hasken farin watan daya ke sararin sama
,
Kofan gidan ya bbude a lokaci daya, dishi dishin mutum idanuwana suka fara hangowa saide ban iya banbance namiji ne ko mace ba,
Mutum din ya nufoni wannan karon kuwa na gane cewa macece, duba da yadda naga tana tafiya, da kuma yanayin surar jikinta,
Sai da tazo daf dani sannan Numfashina ya tsaya cak, kwalkwata ta tafi hutun rabin lokaci
Zuciyata ta dawo bugawa sau hudu a second daya,miyaun bakina ya kafe, da kyar na samu na sassaita kaina,
Cikin dakewa na lalubo harshena na furta
"BUDURWAN SIRRI" a rude na furta kalman
,
Tana tsaye a gabana, kamar yadda nasanta komai nata nanan, babu wani canji daya ziyarceta,
Kayan dake jikinta sun jike da ruwa kuma bata sanye da hijab, hakan ya taimaka wajen baiyano da kiran jikinta,
,
Wani kallo ta makamin mai taken daga ina kake?????
,,,,
Kai fans anya ba mafarkin na sake yi ba
Chapter 10 · 0% Book details