← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 11

Sashe 3

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ci a zuciyata, Ban yi aune ba sai gani nayi mun iso wani kayataccen fada wanda aka kawata da kayan ado irinsu, zinare,zubarjadi,lu'u lu'u da yakutu domin kuwa daben wajen ma da yakutu akayi shi, Ga bayi da hadimai sai zirga zirga suke tayi amma da zarar sun ganmu sai su russuna su kwashi gaisuwa sa'annan su wuce, Mun danyi tafiya mai dan nisa kafin mu iso bakin wata kofa wacce aka sana'antata da zallar farin zinare sannan akai mata ado da lu'u lu'u sai dai wani abun daya daure mani kai da kofar shine ganin wasu macizai danayi guda biyu nan na de da juna a jikin kofan, . Cikin mamaki naga haseena takai hannu jikin kofan ta kama macizan nan duka ta murde musu kayika, sai gashi kofan ta bude, nan muka shiga ciki har hanzu hannuna na cikin na haseena, dakin da muka shiga ya fi kowanne daki kayatuwa a cikin fadan don ni dai tun da na shigo banga wajen daya kai nan kayatuwa ba, . Sai a sannan na lura da wasu kirda kirdan mutani sanye da kayan karfe, suna rike da makamai a hannunsu, kallo daya nai masu na gane cewa Dakarune masu tsaron gidan, nakai dubana ga gabanmu inda muka dosa toh a nan ne naga tarin mutane suna zaune bisa wani dogon kujera wanda ya kusan kaini tsayi, . Wayannan kujerun suna jere ne, layi biyu kowanne kujera yana fuskantar daya, mutanen sunyi shiga ta alfarma wanda da gani kasan ba kananan mutane bane, mai karatu kar kaji nace mutane ka dauka ko bil'adama ne wayannan mutanen , a'a dukkansu Aljannune amma a siffar mutane suke rayuwa, sai kuma wayansu fuka fukai dake bayansu, . Wani dattijon aljani na gani kyakkyawa da shi, yana sanye da fararen kaya masu daraja, zaune yake akan wata karaga ta sarauta, wacce aka sana'antata da zallar lu'u lu'u aka kuma yi mata ado da takubba na farin yakutu, a gefen karagar sa wayansu sadaukan samudawan aljanu ne su goma cikin shirin kota, fuskarsu a murtuke tamkar wayanda aka aiko ma sakon mutuwa, ko motsi basa yi sai kace Gumaka kwana kallo daya nai ma samudawan aljanun nan na kau da kai don kuwa muddin na cigaba da kallonsu toh zan iya Sumewa wajen wayannan aljanu muka nufa ni da haseena muna zuwa gabansu haseena ta durkusa sannan ta kalleni tai min Alama dana durkusa ba musu nima na durkusa, kawai sai ji nayi haseena tana magana da wani irin yare wanda ni ban taba jin sa ba, bayan ta gama maganar ne wani daga cikin Aljanun nan yace mar habanki dake da wannan bako, yake gimbiya daga nan sai haseena ta mike tsaye ta karasa gaban wannan dattijon mai fararen kaya ta rungumeshi sannan ta tsaya a gefensa, dattijon aljanin ya dubeni har yanzu ina durkushe ban dago ba, . Yafara magana yakai wannan bako kuma masoyi ga yata kai sani cewa muna marhaban da zuwanka, kuma a sannu zamu sanar da kai dalilin daya sa muka kiraka izuwa wannan duniya tamu amma kafin nan yanzu za mu bari ka huta tukunna, aljanin yana zuwa nan a zancensa sai ya dubi wani wani bafaden aljani yace mai zirwanu ka kaishi masaukinsa dun ya huta nasan ya debo gajiya, wanda aka kira da zirwanu ya russuna angama ranka shi dade, ********** Ina zaune a cikin dakin da zirwanu ya kawo ni , nayi tagumi bana tunanin komai sai na gida, Yanzu a wani hali iyayena suke nasan dole su shiga wani irin hali izan har ya kaasance basu ganni ba, . Nan take naji bana marmarin komai sai gida dun kuwa nima ina so na gansu ko hankalina ya kwanta, sai de ba anan gizo ke sakar ba, aduk lokacin dana tuna cewa ina da zukekiyar budurwa kamar haseena sai inji zanma iya yin shekaru hamsin muddin zan zauna da haseena . Tunane tunane kala kala suna ta zuwanma kwakwalwata, ina cikin wannan hali ne sai na fara jin wata zazzakar waka tana tashi daga bayan dakin danake, cikin zumudi na nufi taga na bude don naga wacce keda wannan zazzakar muryar, Wani kayataccen lambu ne yaiwa idanuna maraba acikin wannan lambu kuwa yan mata ne su ashirin, suna rike da kayan kida sai kidi sukeyi, dukkan matan nan kyawawane na gaban kwatance domin kuwa in ka dauke haseena har yau banga macen da ta kaisu kyawu ba, A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, ...... . . Kuyi hakuri da rashin post nawa akan lokaci rashin wadatuwan lokaci shi ya janyo haka , Ni dinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% Daga:- www.facebook.com/hausaebooks BUDURWAN SIRRI Marubuci:- Shuraih Usman @hausaebooks.cf @shuraih 99% Page 5 . A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar muryarta ne kawai yake tashi, Zuciyata ce ke fisgata irin fisgar da ruwan kashe gobara yakeyi yayin fitowa daga cikin bututun ruwan . Ni kaina ban san lokacin dana je na bude kofar dakina ba da nufin nayo waje naga ko wacece wannan mai wakar, har na saka kafa na fita kuma sai nai wani tunani , Ayanda nake jin ana labarta min cewa nan duniyar aljanu ce , na tashi na nufi wajen wayannan kyawawan matan, kila ma aljanu ne ban sani ba, Wannan tunanin dana yi shi yasa na dawo da baya nai kwanciyata cikin dakina, Dakyar na samu nasarar yin bacci sakamakon wannan zazzakar wakar dake tashi daga waje, aduk lokacin dana runtse idanuwana domin nai bacci sai na wannan zazzakar murya ya farkar dani, Har takai da saida na samu wasu yanki na toshe kunnuwana da su sannan na dena jin wannan waka . Washe gari na farka a gajiye na tashi na nufi dan wani kofa dana gani a cikin dakin wanda tunanina ya bani cewa bayi ne, kama yadda na zata dun haka yake dun kuwaina budewa na shiga na samu ruwa cikin wata randa na zinare batare da bata lokaci ba nayi wanka da wannan ruwan sai de abun daya daure shine a duk lokacin dana debi wannan ruwa sai naga ya karu Har na iddar da wankan na fito daga bandakin na nufi kan gadona domin na saka kayan dana cire ajje , Amma kayan sai sukace daukanmu inda ka ajje, na neme su sama da kasa na rasa, can na bayan na gaji da nema sai na dawo kan gadon na zauna nayi tagumi, wani haske naga dan kashe mani idanu, na kai dubana ga wajenda hasken ke fitowa sai naga ashe ma a gefena ne, nakai hannu don ganin menene wannan yake wannan haske, cikin mamaki sai gani nayi hannuna ya tabo wasu lallausan abu duk da ban ko menene ba sai na daga abun sama toh anan ne aka samu mishkila abun ya kubuce daga hannuna ya fadi a kasa ai yana faduwa sai naga ashe ma kayane riga da wando irin na sarautar mutanen garin Cikin tu'ajjibi na dauki kayan na sanyasu a jikina sannan na nufi wajen madubin dayake dakin nayi mamaki ainun alokacin dana irin zunzurutun kyan danayi, kai alokacin sai dana koda kaina nace ashema ni kyakkyawane haka, , Karar Kofan dakin ne ya katse ni, lokacin da ake kwankwasawa, na nufi kofan nabude su ukune kamar yadda na fara ganinsu, har yanzu babu wani sauyi atare da su, yan matan jiya ne daya daga cikinsu ta dubeni tace "ran ka ya dade gimbiyace ta turomu mu tafi dakai wajenta don kuyi kalaci" "Wacece kuma gimbiya" na tambaya "Wacce ta kawo ka nan garin" "Wai HASEENA ki ke nufi" Na lura da cewa wannan kalma danayi na karshe yasa dukkansu sun tsorata duk da bansan dalilinsu na tsoratan ba, "Eh itace , amma yallabai kasani duk fadin kasarnan babu wadda yake kiran ta da sunanta hatta mahaifinta ma, " "Saboda me ba'a kiranta da sunanta" "Wannan kuma wani sirrine na gidan sarauta" Na jinjina kai sannan nace masu "Toh muje " Suka juya suka fara tafiya ni kuma na take masu baa . Mun danyi tafiya mai dan nisa sa wacce takaimu izuwa wani kayataccen lambu wanda ya yalwatu da yayan itatuwa, su kansu bishiyoyin dake cikin lambun ababen sha'awane, domin kuwa bishiyoyin dukkansu yana yinsu daya ne, tsayinsu da komai na su, Furannin lambun kuwa sun kasance a duk bayan dakika daya suna dunkule wa waje guda, Muka nufi wani waje daban a inda muka bi ta kan gada, wannan gadan de an kerashi ne da zallar itace da igiyoyi aduk lokacin da muka taka gadan sai kaji wani kara na tashi . Tun daga nisa na hango kyakkyawar fuskarnan nata sai sheki yakeyi, farace kyakkyawa gata da dirarriyar jiki domin kuwa shape dinta na kwalbar cokacola ne, Ta mallaki tsastsaikan fuska wadda ke dauke da dara daran idanu, wayanda jure kallonsu, dan mitstsin bakinta wanda idan ka lura da kyau alokacin data ke magana zakaga tamkar baya so ya bude, . Ayau tana sanye ne da irin kayan duniyanmu kuma irin na kasarmu, riga Atamfa da sikert, abun ya bani mamaki ainun, ni danake zaton babu irin wannan kaya a wannan garin, sai de dana tuna da abu guda sai nama dena mamaki . Ayau tafi kowanne lokaci kyau fuskarta sai sakin tausasan murmushi yake a gareni, ai ban san lokacin dana kura mata idanu ko kiftawa bana yi ba, Muka kariso wajen yan matan nan sukayi saurin russunawa akasa zasuyi magana kenan ta dakatar da su ta hanyar daga masu hannu sannan ta sallamesu, sukai tafiyarsu . Ta dubeni tai wani murmushi wanda yake zuzuta wutar kaunarta a zzuciyata, "ka kwana lafiya" "Lafiya lau" Ta riko hannuna , awannan lokacinma sai da naji shocking ya ziyarci kwakwalwata, har nayi dan kara karami, ta jani muka karisa gindin wata bishiya, inda naga an shimfide gaba dayan wajen da wani babbar tabarma, a tsakiyar ta barmar ga abubuwan ci da sha nan birjik, Takalmi na cire alokacin da nake shirin hawan tabarmar, Wani laushine ya ziyarci tafin kafafuwana ,ko kadan wannan baiyi kama da tabarmar dana sani ba mai uban gurza-gurza Haseena ta zaunar dani itama ta zauna kusa dani yanda muna iya jin numfashin juna "Shuraih tun da nake a
Chapter 3 · 0% Book details