← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 11

Sashe 11

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 13
.
"Malam daga ina ??"
Ta harbeni da tammbaya fuskarta na nuna alamun bata
taba ganina ba,
,
Karin mamaki ne ya mamayeni a sa'ilin data jefo mani
wannan tambayar,
,
Maimakon na bata amsar tambayarta
Sai natsaya ina kallonta kawai, kafin daga bisani na furta
"Haseena shin baki gane ni ba"?
,
"To ta yaya kuwa za'ayi na gane ka, wai shin ma a ina na
sanka, da har zan ganeka, naji ma har sunana ka sani?a
ina kasan sunana"
Bakinta kawai nake kallo yayinda take maganar sam na
manta da duk wani kalubale na rayuwa dayake shirin
tunkarata a sanadin wannan yarinyar, na manta irin tarin
wahalan da nasha don kawai naga na mallaki budurwan
sirri,
,
Karar tafin hannunta sune suka dawo dani cikin
hayyacina ,
Kamar wanda ya farka daga barci, na girgiza kai ina mai
cewa
"Sam haseena bai kamata ace kin manta da wanda yake
shirin sadaukar da rayuwarsa akan ki ba,kece..."
Magana ta ya katse a lokacin da gaba dayan cikin zauren
ya gauraye da hasken wutan NEPA,
Kunnuwana suka daukomani muryan yara suna cewa
NEPA,
Minal jinnati wannas, abun danake furtawa cikin zuciyata
kenan, kafin na furta "tabarakallahu ahsanul khaliqeen"
,
Duk ganin dana kewa haseena ban taba yi mata kallo irin
na yau ba, ayau ne nasan cewa haseena tauraruwar
matace,
Na lura da yadda jikinta yayi sanyi ba kaman da ba, lokaci
daya dukkan wani tsiwanta suka lafa, ita kanta ta zargu da
irin kallon dana ke mata,
Daga kai tayi sama, alaman tana son ta tuno da wani abu,
Ihu mai karfi ta saki sa'annan ta sulale a kasa
sumammiya,
,
Hankalina ya tashi da sauri na fadi a kasa kusa da ita ina
mai tallabo kanta hade da kiran sunanta
Da karfi nake kiran sunan nata,
Karar bangaje kofa naji daga bayana da sauri na duba
gefen da naji karar
,
Wata tsohuwace naga ta nufoni da gudunta, kallo daya
nai wa tsohuwar na ga suna dan kaman ceceniya da
haseena
Tsohuwar wacce ban san ko wacece ita ba tana isowa ta
kama hannun haseena kodubana batai ba, ta tallafo
wuyanta da kafafunta ta daga ta sama cak, tayi cikin
gidan da ita,
,
Tarin mamakinn da wannan al'amari ya bani shi ya sanya
na fara jin jiri na dibana, don babu ta yadda za'ayi yar
fingilar tsohuwar nan ta iya ciccibar budurwar mace
kamar haseena,
Na tabbata ko kosasshen akuya wannan tsohuwar ba zata
iya dauka ba amma sai gashi ta ciccibi budurwa
.
Na yunkura da nufin na tashi nima nabi bayan tsohuwar
cikin gidan,
Toh alokacinne wani babban al'amari ya afku al'amarin
daya sanya ni farinciki gaya,
,
Yun kura wata keda wuya na dumfari kofar shiga cikin
gidan,
Batare da wani shakku ko fargaba ba na bangaje kofan da
kafata sannan na antaya ciki,
'Lahaula wala kuwwata illa billahil azizul hakeem"
Na fada a bayyane yayin da idanuwana sukai arba da
abunda ya kusan zautani,
Shakka babu yanzu kam na yadda cewa Rayuwata a cikin
mafarki gaskiyane, labarin budurwan sirri ma gaskiyane,
sai de kuma kar ya kasance shima wannan karon
mafarkin nakeyi,
Tsintar kaina nayi cikin dajin da aka koya mani fada, a
gaban bukkar tsoho zaikid,
Nadai daure na isa gaban bukkan koda na tabbata
bukkarne sai na nufi cikinta sai de tun kafin na kai ga
shiga, naga ana kokarin futowa daaga cikin bukkar
Tsoho zaikid ne ya fito fuskarsa tana mai yimani
murmushi, abayan tsoho zaikid wannan tsohuwarce data
dauki haseena
Na saki baki cikin firgici ina kallonsu, anan take na fara
tunanin shikenan na sake jefa kaina gidan jiya,
"Dan saurayi Shuraihu! Taho ka zauna ba mafarki kake ba
"
Muryan tsoho zaikid ne ya ankarar dani daga dogon
tunanin da na fada
Ba musu kuwa na zo na zauna agabansu yadda kasan
wani mai daukan darasi, su kuma suna zaune akan wata
itace,
Tsohuwar nan ta bude baki ta fara magana
"Yaro hakika mun yarda da soyayyarka ga haseena, duk
munga irin halin daka shiga sakamakon ta, shakka babu
ka cancanci auran budurwan sirri,"
Tacigaba bayan taja gauron numfashi
"Kai sani cewa Haseena ita kadai ce ta tsira da rayuwarta
a yayin da ka dasa makaminnan, a garin bulzum ita kanta
haseena abu daya ne ya taimaketa,
Ta kasance a cikin kwayoyin halittar jikinta , rabin
kwayoyin halittar na Aljanu ne rabi kuma na Bil'adama
ne,
Toh a yayin da wannan makami ya fashe, sai ya kasance
kwayoyin jikinta na Aljanu sun mutu, da shike ALlah yasa
tana da sauran kwana sai kwayoyin bil'adama suka maye
gurbin wajen kwayoyin halittan,
Yanzu kam haseena ta zamo bil'adama sak irinka
Hakan ne ma yasa Zaikid ya dauketa daga duniyar nan ya
kaita duniyarku ta bil'adama domin ta samu
kyakyawawan kulawa,"
,
Bakina bude nake dubansu na kasa bambance shin farin
ciki zanyi na kasancewar haseena a matsayin bil'adama
ko kuma bakin ciki zanyi na komo wata duniyar da babu
Bil'adama,
,
Tsoho zaikid yayi murmushi a karo na farko yace "ina
sane na sanar dakai cewa haseena ta halaka, na kuma
koma da kai izuwa duniyarku, saide yanzu da kwai
matsala daya"
"Wata matsala kenan"
Na tambaya
Tsoho zaikid yace "matsalar shine haseena ta manta
dukkan wani abun daya faru da ita lokacin da take
duniyar nan, shi yasa ma da kuka hadu kaga bata shaida
ka ba"
,
"Amma mai yasata faduwa dazunnan"
Na tambaya ina kallon tsohuwar nan
"Dogon tunani ko kuma son tunano abun daya faru
lokkacin daya wuce"
,
"Ban fahimta ba"
"Aduk lokacin da haseena tayi yunkurin tunano
rayuwarta na baya toh hakane zai runga afkuwa da ita,
zata iya Suma, izan kuma abun ya yawaita zai iya shafan
lafiyanta, sai ka kiyayi yi mata duk wani abun da zai sanya
tayi kokarin tunano rayuwarta na baya"
Tsoho zaikid ya bani amsa
Tsohuwar nan ta dubeni da kyau tace
"Nasan kana tunanin koni wacece? Toh nice kakar
haseena, dun kuwa ni na haifi mahaifiyarta
Kafin Nuridden ya aureta alokacin mahaifinta ya rasu,
kuma ni bansan cewa nuriddeen Aljani bane, har ya auri
yata, suka samu karuwa da juna biyu, saide a yayin
haihuwar yata ta koma ga mahaliccinta,
Tun daga wannan lokaci ban sake ganin nuriddeen ba
bare har na gana da haseena, sai a kwanakin baya
wannan aljanin ya kawota wajena ina ganinta na ga
fuskar yata a tattare da ita , shine yayi mani bayanin
dukkan abun da ya faru "
Ta karisa zancen tana mai duban tsoho zaikid
'Baba yanzu a ina haseenan take"
'Tana cikin bukkata"
,
Na mike tsaye na dumfari bukkar wacce tun dana fara
zuwa Dajin har wa yau ban taba shiga ciki ba
,
Batarre da fargabar komai ba na tura kai cikin bukkar
Yadda nai tsammani hakan take babu komai cikin bukkar
sai wata tabarmar karau, sai wasu tarin tarkace a wani
saqo,
Idanuwana suka kai ga inda haseena take kwance a
saman tabarmar karau dinnan tana barci ,
Kallonta nake bana ko kiftawa har na kariso inda take
nakai hannu da zummar na taba saman goshinta cikin
mamaki sai gani nayi ta bude idanunta,
Da sauri na kauda hannuna , ta mike zaune tana dubana
sama da kasa tace
"Wanene kai ? Yanzu a ina nake"
"Zaki iya kirana da masoyi yake abar qaunata,"
"Masoyi!" Ta nanata sunan a bakinta
"Amma ina ji tamkar na taba ganin ka a wani waje
daban"
,
Ta fadi tana kallona
Nayi murmushi nace "eh tabbas kin sanni domin kuwa
mun sha haduwa dake cikin mafarki a matsayin Masoya,
masu begen juna, bazan taba mantawa da ranar da kika
furta cewa kina Sona ba, "
,
A dan firgice ta zazzaro idanuwa tace "da gaske ni na fadi
hakan"
'
"Eh kin fadi haka kuma har ma kika bani zobe a matsayin
Alkawarin aure a tsakaninmu, tun daga lokacin danai
arba dake a cikin mafarkina rayuwata ta sauya, a kullum
bana da buri sai na in sake yin mafarkinki, nakan raba
dare ina mai tunano da kyakkyawann fuskarki , abun
dayafi jamin hankali dangane dake shine murmushinki,
aduk lokacin dana tunaki sai inji farin ciki ya baibayeni,
duk irin kuncin dana ke ciki da zarar na tunaki sai ya
yaye, Akullum addu'ata shine ubangiji ya bayyana min ke
a zahiri, da shike Allah maji roqon bawansane, sai gashi
Allah ya hadamu,"
Haseena tayi shiru tana kallona ga dukkan alamu
kalamaina sun ratsa jikinta,
Cikin sanyin jiki ta kwantar da kanta kas
"Haseena" na kira sunanta
Ta dago kai a hankali batare data amsa ba
"Ina sonki, ina kaunarki, shin kina Sona"
Bakintane ya fara kokarin motsi alamar tana son furta
wani abun sai kuma ta fasa
,
Ta mike tsaye tsam ta fara tafiya cikin sanyin jiki , har ta
isa bakin kofan bukkar sannan ta juyo muka hada
idanuwa da ita
Duk da bana iya jure kallon cikin kwayan idon haseena, a
wannan lokaci sai na tsinci kaina ina mai kallonta batare
da kiftawa ,
,
Murmushi tayi yayin da gefen kumatunta suka lotse
wushiryarta suka fito, hakan yayi matukar kara fidda
kyawunta, daga nan sai ta fice daga bukkar a guje
,
Koda naga haka sai nima na tashi na fice daga cikin
bukkar........
ALHAMDULILLAH
Anan na kawo karshen Littafin BUDURWAN SIRRI
Sai kun jini cikin sabon littafi
,
Duk wani kuskure dana tafka Allah ya yafeni
Gefen ADABI kuwa,
Ashirye nake don karbar gyararraki, shakka babu ni kaina
nasan da kwai kurakurai da dama dana tafka,
A kullum burina shine na ga na kware wajen rubutun
hausa na adabi, DAlibi nake ba gwani ba
,
Dan koyo nake ba dan iya ba
Wannan shine takena
,
(c) Shuraih 99% 2018
BUDURWAN SIRRI
Publisher : (c) Shuraih 99%
Author : Shuraih Usman
Year : 2018
.
Wannan littafin na BUDURWAN SIRRI an fara
kasuwancinsa Okadabooks akan #300
,
Wayanda suke son karantawa sai su duba facebook ko
kuma su duba shafin Shuraih 99%
,
Masu neman Ebook sai suyi marmaza su garzaya
shafinmu na ebook mai taken Hausaebooks.cf
.
Nagode wa Allah mai kowa mai komai daya bani dama na
kammala littafinnan ,
Matukar godiya da jinjina ga ahalin ;
_____
PAGE
_____
Shuraih 99%
Triple Abubakar Hausa Books
Littattafan Hausa
Dandalin Abduluk hausa books
Zauran Labarai
Home of Littafan Yaki And Hausa
Novels
Hikayoyin Yaki
Hausa ebooks - pdf,txt and doc
_______
GROUP
_______
KINGBOY ISAH HAUSA NOVELS
FILIN LITTAFAN HAUSA NEW
TSANGAYAR MARUBUTA
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
HAUSA BOOKS
HAUSA NOVELS
Chakwakiyar Soyayya Hausawa DA Pulani
Donated By www.Hausazone.Com
KUZO MUYI NISHADI
Samee khairah novels group
DANDALIN HAUSA NOVEL
DUNIYAR MAKARANTA LITTATAFAN HAUS
360 Hausa Novel Books
FEENAT JA'AFAR NOVEL'S
HAUSA BOOKS NOVELS
Just Hausa Novels
kingarticle novels of abdul$bafferh
Zumunci Hausa NoveLs [ÝäzèèÐ]
HAUSA NOVELS ONLY
*FATIMA ZARAH NOVEL GRP(HAUSA)*
Hausa Novels by ASK
(GREAT HAUSA NOVELS BOOKS)
SOYAYYA RAYUWA CE
ZAINAB MUHAMMAD AND NUHU ALIYU
GUSAU NOVEL GROUP
Nagode sosai da yadda kuka nuna kulawarku gareni da
kuma bibiyar littafin budurwan sirri Allah ya barmu tare
Nine dai nakunnan shuraih Usman inkiya 99%
Chapter 11 · 0% Book details