← Book details Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Budurwan Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

******
.
Washe gari tunda sassafe wayannan yan mata uku suka sake zuwa kirana sai de yau dukkansu sun canja kayan dake jikunsu irin kayan dana sanya jiya shi na sake sakawa duk da ban san wanda yake kawo mani kayan ba hakan bai hanani sakawa ba
.
Wannan karon ba yalwataccen lambunnan muka nufa ba wani bangare ne daban wanda kallo daya naiwa bangaren nagane cewa mutane ba su cika shiga wajen ba duba da yadda naga wajen yayi kura, kuma yanan gizo gizo duk ya gauraye rufin wajen,
.
Muka iso bakin wata kofa mai kauri wacce aka sana'antata da zallan bakin karfe daya daga cikin matannan ce ta ciro wata tsohuwar kubba daga jikinta ta zura a cikin dan siririn ramin dake jikin kofan sannan ta murda
Dan karamin dakine mai dauke da kayan tarkace iri iri , a karshen bangon dakin muka hango ta naayi mamaki kwarai da ganinta anan
.
Na kariso ni kadai a yayin da yan mata ukunnan suka tsaya a bakin kofan dakin rufe kofar dakin sukai
Na budi baki zanyi magana haseena ta dora yatsanta a kan lebbana alamar nayi shiru ta nufi wani kusurwan dakin daban wata tsohuwar tayan keken doki naga ta daga, ta kama wani katako ta murda shi
.
Nan take jiri ya fara dibana sakamakon yadda naga dakin yana juyawa da sauri haseena ta ruko hannuna sannan itama ta rike wani karfe , kafin kace kwabo sai dakin ya runga juyawa dukkan tarkacen nan suka fara tashi sama suna haduwa da junansu, baki kawai na saki ina kallon ikon rabbi, sai da gaba dayan tarkacennan suka gama hadewa waje guda suka dunkule kaman dunkulin magi
.
Sai da suka gama dulkulewa tukunna sai kuma dunkulin ya fara fitarda yar karamar kofa, kan kace kwabo har wannan dunkulin ya canja siffa izuwa na Kofa,
Babu abunda zai baka mamaki ma kaman yadda kofan ta kasance sai haske take tana daukan idanu
.
Adai dai lokacinne dakin ya daina juyawa komai ya tsaya cak sai a sannan haseena ta ce "wannan shine babul hajir, ta cikin wannan kofa zaka iya tafiya ko ina a doron kasa, tun daga kan duniyarku har zuwa wasu duniyoyinma,"
.
Shiru kawai nayi na saki baki ina kallonta ni yanzu ma har na saba da abubuwan mamakinsu koda na gani ma banayin mamaki sosai kamar yadda nake a baya
.
Ta ja hannuna wanda hakan yasa nima nabi bayanta bakin kofan muka zo muka tsaya ta sanya lallausan hannunta ta bude kofan sai a sannan dukkan wani mamakina ya karu domin kuwa babu komai a gaban kofan banda hazo daya ke gittawa lokaci lokaci, banga alaman wani abun ba
.
Haseena ta jani muka shiga cikin kofan ai sai dukkanmu muka ji kamar mun fado daga saman wani katon tsauni ne, saboda tsaban firgici kulle idanuwana nayi yayin da muke fadawa kasa iska sai gittani yake ta ko ina hakan yasa na saki wata kara
.
Kamar daukewan wutan nepa sai mukaji mun fado a cikin wani rami, abun da ya kara dauremin kai shine da kafafuwanmu muka fado kuma ko dan zogi banji kafata tayi min ba
.
Haseena tai murmushi "tace haka ka iya ihu dama ban sani ba, ai kuwa sai ka tanadi wani ihun da yafi wanda kayi a baya, domin kuwa yanzu ne za'afara ainahin tafiya" cikin sigar zolaya ta fada
Na sosa keyana "ai ni kaina ban san lokacin da na saki ihun b....."
Wani kara ne ya katse mani maganata karan kuma daga kasan inda muke yake fitowa sai a sannan na daga kaina na kalli sama
Gani nai tamkar mun fada cikin rijiya gaba dubu ne
Ban gama wannan tunanin ba kasan wajen ya wawake take muka fada ciki amma wannan karon a tsaye muka fada kuma ahankali muke sauka kasa,
Cikin wani daji mai yawan guntayen bishiyu muka sauka , sosai yanayin dajin ya burgeni dukkan wasu ganye na dajin jane maimakon kore mun danyi gajeriyar tafiya da kafafunmu sannan muka riski wani Bukka irin na mutanen da shi kansa bukkan da jajayen itace aka sana'anta shi, bakin bukkar muka tsaya sannan haseena tai sallama, wata tsakurarriyar muryace ta amsa sallamar, daga bisani sai wani dattijon Aljani ya fito daga bukkar yana sanye da dogon yar shara har kasa sam sam fuskarsa bata nuna alamar tsufa ba ,zai yin kama da saurayi mai jini a jika
Har kasa ya zube yayi gaisuwa wajen haseena ta durkusa ta dagoshi tace "baba zaikid nasan dai basai na maka bayanin abunda ya kawoni wajenka ba, amma duk da haka zan sake maimaitawa, wannan shine Mijin nawa In Allah ya yarda ina so a cire masa dukkan wani tsoro na jinsun mu kuma ka koya masa dukkan wasu dabaru da salon yaki, nan da wata daya zan dawo na daukeshi"
Murmushi tsoho zaikid yayi "an gama ranki shi dade"
Ni dai na cika da mamaki ainun jin cewa wai ni za a cire ma tsoro sannan kuma wai za a koya min yaki da dabarun fada
Haseena ta dubeni a lokacin da fuskarta .......

Kwana biyu kun jini shiru
Bani da lafiya ne shi isa
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 7
.
Haseena ta dubeni a lokacin da yanayin fuskarta ya sauya , ta kankame hannuna sosai tace" shuraih muddin muna son mu rayu har abada amatsayin mata da miji toh dolene ka koyi wasu abubuwa na yaki, da kuma ka kuma cire tsoro a zuciyarka, ina matukar sonka irin son da baki ba zai iya fasaltashi ba, hannu ba zai iya rubutashi ba ko na dakika daya bana son rabuwa dakai, amma dole na na barka anan domin ka koyi yadda zaka kare kanka daga sharrin Salman"
.
Har na budi baki zanyi magana sai ta sanya yatsanta a akan lebena alamar nayi shiru ba musu nayi shirun duk da irin tarin tambayoyin dana ke shirin jefamata
Ta dan ja baya kadan sannan ta soma tafiya har tayi nisa idanunawana suna kanta ta juyo muka hada idanu ta sakarmin murmushi daga haka ta cigaba da tafiyarta har ta bacemin da gani ina nan tsaye a gun
.
Tsono zaikid ya dubeni da kyau yace "yaro shin meye sunanka"
"Shuraih" na bashi amsa batare dana kallesa ba haryanzu idanuwana na kan hanyar da haseena ta bi
Tsoho zaikid ya sha gabana sannan ya turbune fuska yace "shuraih kake ko wa to bari kaji Abunda kazo yi nan shi za kamai da hankalinka gareshi , domin kuwa in kai wasa toh kana ji kana gani ta rabu da kai kenan"
Sosai hankalina ya tashi da maganganun wannan tsohon
Batare daya jira amsana ba ya juya ya shige cikin bukkarsa yana cemin" ka dai shirya don kuwa daga gobe zamu fara atisaye "
....
Chapter 5 · 0% Book details