← Book details Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 32

Sashe 2

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"mero!!" wanda ya mayarda hankalin akasarin mutanen dake parlor akanta,da sauri mero tazo tace "Lele ya akai?" zumburo baki tayi tace "Dayake kinfison mutanen nan dani shine kika barni da yunwa tun dawona nake jiran abincina,ni ki zubamun to" kallon ta mero tayi tace "Dady ne ya sakani aiki kiyi hakuri mezan saka miki?" duk abinnan dasuke a gaban idon shammaz ne, ko kallonta batayi ba ta saka alawar datakesha a baki ta hau tsotsa sannan ta hard'e hannayenta gu daya,ganin haka mero ta gano rigima takeji yasanya ta dauki plate ta saka mata snacks da papaer chicken ta juyo ta miqa mata, karb'a tayi sannan ta kifar da abincin a wurin cikeda raini da shagwaba tace "ni wannan nace dake ina so? Shreded chicken zanci" batayi auneba taji saukar lapiyayyen mari wanda ya kusan zautar da ita,dafe wurin tayi ta saka kuka kowa a parlor din ya taso ana baiwa Shammaz haquri ita kuwa mero tazo da sauri ta riqe hafsat tana rarrashinta,wani kallo shammaz ya wurgawa mero, cikin fada ya furta " Maryam zan mareki wlhy kema,maza ki saketa ta clearing wannan mess datayi" jikinta har rawa yakeyi ta duqa ta soma tattare wurin tana sharar k'wallah tana gamawa yace " se kinci wannan din yar rainin hankali da zaki wani zo tana tambayarki kina iya shege sannan yanzu an zuba miki ki kifar an gaya miki a qasa ake haqowa" juyawa tayi zata haura sama da plate a hannu tana kuka yace cikin daga murya

"Maza zo nan zaki zauna ki cinyeshi a gabana" dawowa tayi ta janyo kujerar dining daya tana kuka tanaci harta cinye tatas,momy dai batace komai ba amma harga Allah bataji dadin abinda shammaz yayiwa Hafsat ba agaban mutane,kumama tsabar rashin tunani daga dawowarshi duk wanda yaga yayiwa qanwarshi wannan abin aiseyaga tamkar baya san tane..........

Mom Nuaiym ce
[1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci:         *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin.            wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                 02

Hawa saman tayi bayan ta kammalawa cinyewa taje rufe kofar d'akinta tasaka wani uban kuka tanata faman shura qafa,duk abinda ta samu seta fasa ita adole zuciya,su momy sunzo juyin duniya sunyi akan ta bude kofar d'akin amma fir taqi se dad'a sautin kukanta takeyi Aunty surayya ma datazo tayita fadan amma yau ko gezau,surayyace takira Yaa shammaz yazo bakin k'ofar yace cikin daga murya

"Hafsat Allah idan har kika kuskura na sameki a d'akin batare da kin budeshiba ranki ne zeyi matukar b'aci anan" cikeda fargaba ta bude kofar d'akin ta qura masa ido jan hannunta yayi sukayi waje sannan yakaita b'angarensa,zaunar da ita yayi suna fuskantar juna yace

"ke har yanzu Hafsat girma da hankali basu wadace kiba? Mero sa'an kice sannan yanzu wannan uban borin dakikeyi a daki ke kadai wa kikewa shi? Sarai kinsan halina tsaf zan zaneki karkiga kamar yanzu na dawo zaneki zanyi sosai,kuma idan na kuma ganin kina wannan kukan ko hawaye daya na gani a idonki sena zaneki yanzumma kece da kanki zaki gyara barnar dakikayi a dakinki,sakaryar yarinya kawa,kuma daga yau duk bayan kwana biyu kece zaki riqa zuwa kina gyaramun wannan bangaren nawa,ki share ki goge da komai kina jina?" da sauri ta daga masa kai a ranta tace "Ina kammala exam zan gudu gidan Abba wlhy bazan zauna wannan mugun ya kashe niba" a fili kuma godiya ta masa sannan ta fita daga dakin.....

*Washe gari*

     Yaa shaam na zaune a a daya daga cikin gujerun da aka qawata ht dake farfajiyan gidan dasu yana karatun news paper hannunsa daya na riqe da cup na hot meantleaf coffee yana kurba a hankali,ganin Hafsat ta fito ya sanya da sauri kuma cikeda mamaki ya mayarda dubanshi zuwaga wrist warch dake hannunshi,dagowa ya kumayi yaga driver yazo ya bude mata tashiga gidan baya ta zauna,driver din ya kwallawa kira yazo ya da sauri ya durqusa yana jiran cewar sa,kamar baya sanyin magana yace

" Ina zakujene k'arfe tara da rabi na safe?" kanshi a qasa yace "Yallab'ai Haj qarama zankai makaranta?" Haj k'arama ya nanata a ransa sannan a sarari yace

"yaushe yakamata ace kana fitowa kaita makaranta?"

"yallab'ai dama da safene kullum k'arfe bakwai anan gidan yakemun,hajiyar ne bata fitowa se sanda taga dama" cikin mamaki yace "Ita hafsat ne setaga daman zuwa skul zataje? Maza jekamun kiranta" koda friver ya sanar mata tana fitowa mota kuka ta saka ta kwasa ciki aguje,miqewa shima yayi a fusace yabi bayanta,daddy da mommy na zaune  a dining taruga ta fada jikin dady,kan wani cikinsu yayi magana sega yaa shaam ya shigo a fusace,momy ce tayi saurin magana

"shaam lapiyanka kuwa meya sameka kaida qanwarka haka taketa kuka" daddy ya kalla yace "Amma daddy sabida Allah kuna kallo se yanzu hafsat zataje makaranta qarfe goma saura fa?? Wannan wane irin tarbiya aka mata ba kwab'a ba komai ace yarinya se sanda taga dama zataje skul wannan ai ba soyayya aciki" shiru daddy yayi saboda yasan gaskia shaam ya fada momy ce tace cikin quluwa "Kaga shammaz nafa kula tun dawowarka jiyannan ka takura yarinyarnan,hafsat baccin safe ne da ita kamar me ya kakeso muyi? " kallon momy yayi rai a b'ace yace "wannan ai rashin sone idan naga zatayi rashin hankali na barta,wannan ba takura aciki tsantsar soyayya ce nake mata,kuma ita jakar inace bata ma tsoron duka irin wannan mugun lattin ai dole setasha duka kullum"

"makarantar mahaifinku take zuwa,se abinda taga dama takeyi ba wanda yake takura ta wlhy"  tsaki yaja yace "wlhy ba wanda ya isa ya b'atamun qanwa ina numfashi haba mana daddy ni haka kayimun? Ni bansan wannan wane irinn qata kuke nunawa hafsat ba sekace a kanta kuka fara ganin 'ya'ya wlhy ni idan suka gama wannan jlce din sauya mata skul zanyi" momy zatayi magana daddy ya hanata "duk yanda kayi  daidai ne shammaz na tsame hannuna a lamuran hafsat tunda magajinta yazo haj kema naki idone lallai idan kina taka masa birki zakija masa raini a gunta kuma kinsan ya isa da ita sannan kuma ke karan kanki nasha sanar miki zaki ruguza rayuwar hafsat ne idan kina biye mata,yarinyar nan tanada kokari sosai zama mu iya cewa gifted idan bakya nuna mata muhimmancin karatun watsarwa zatayi" shiru momy tayi badan ranta yaso hakan ba  daganan daddy ya daga hafsat ya bar gidan gaba daya,a gaba shaam ya saka hafsat har wurin mota yayi kiran driver din yace

"Daga yau ita zata riqa bude mota da kanta tashiga sannan karna kuma jin kace mata wata hajiya karama,kuma ita zata riqa gayar dakai ba wai ka gaidata ba,yarinya sa'ar y'arka zaka zauna kana wa biyayyah kuma kullum idan tawuce 7/30 batazo kun wuce skul d'in ba kazo ka sanarmu" tana kuka tawuce suka je.......

*Bayan wata daya*

     Tun bayan da yaa shaam ya dawo gaba daya rayuwar poojah ta sauya ko a makaranta sun fahimci hakan,sabida tazamo so quiet a rayuwarta ta tsani yaa shaam kuma masifar tsoransa takeji matuqa,zuwa yanzu duk wani abu dazesa yamata fad'a tofa gudunsa takeyi kuma idan tana parlor d'n k'asa ya shigo yanzu zata gudu shi kanshi ya kula da hakan kuma harga Allah baya san rashin walwalarta a kusa dashi danya kula momy ma ta sauya masa ba kamar daba gani takeyi tamkar yana cutar mata da yarinya......yauma kamar kullum hafsat na zaune a parlor tana kallon wani catoon series na barbie yaa shaam ya shigo ko kallonta beyiba ya zauna tana ganin haka ta miqe zata gudu yace yana danna wayar hannunshi " Hafsat zo" kawai seta soma hawaye dawowa tayi ta tsuguna a gabanshi tana sharar k'wallah,kan yayi magana phone nashi ya soma ringing d'agawa yayi ya kurawa hafsat data sadda kanta ido,mamaki yakeyi me aka mata take wannan hawayen ,cikin sanyin murya yace

"Haleema na ya akayi?" a d'aya bangaren seji yayi tana kukan shagwab'a "Haba mana boo me kwana biyu kana cikin garinnan amma sam bakazo ka ganni ba Allah yau idan har bakazoba ni gobe da sassafe zan wuce wana sokoto kuma Allah bazan dawoba sekaje da kanka" k'arayin kasa da murya yayi

"Haba leemah dear,zanzo yau dinnan inshaa Allah kuma ma yaune alqawarin new phone nakifa nama isa naqi zuwa,u expect me anything 7:pm inshaa Allah" daga nan sukayi sallama akan se yazo kallon hafsat yakumayi yace

"Lele zoki zauna kusa dani" da mamaki ta d'ago ta kalleshi amma bata taso d'inba sanda yakuma cewa "zomana ki zauna anan,magana zamuyi" yafada yana nuna kusa dashi d'in, jiki a mace tazo ta zauna kusa dashi ya kalleta yace " haba lelen dady kukan kuma na menene eye? Ba abinda zan miki,nifa yayan kine uwa daya uba daya,me zaisa kina tsoro na har haka daga yauma mun zama best friends kinji" murmushi tayi tace "To na gode" a sanyaye

"Dama zancen school ne,zakice premier kuma interview din gobe ne,ss1 zakiyi interview nasu" girgiza masa kai kurun tayi sannan tace "Zanje nayi sallah se goben" ta miqe

" ki shirya zamuje dake wurin yayarki yawo,ko bazakiba?" fara'arta fa fadada tace "Zanje mana gun matar dazaka aura ko yaa shaam Aunty leemah?" murmushi yamata yace "ea can 6:45pm kina sallame magrib ki sameni mota,bana karbar uzurin african time?" juyawa tayi tana murmushi tana kuma mamakin sauyawar yayan nata lokaci daya,dukkuwa dayake ta hango sosai ba wasa a lamuransa musamman akan karatu".....

Mom nuaiym.
[1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

Vote me on wattpadd@68billygaladanchi.

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

03

Hafsat kyakyawar yarinya ce fara qal me tsayin gashin kai,siririyace samb'al sedai fa ba gaba ba baya duk da yake bazamu yankewa surarta hukunciba kasancewarta yarinya y'ar shekaru goma sha hud'u wanda har yanzu bata gama hada girman jikinta ba,tana da dogon hanci me tsayin gaske da manya manyan dara daran fararen idanu masu wani d'igon zaiba zaiba aciki koda wane lokaci idanun zaka gansu a lumshe tana da d'an mitsitsin baki amma lips nata suna da dan kauri sedai ba cancanba,sosai takeda gashin gira dana girar ido baki wuluk,sannan kuma suman kanta yazo har k'asan goshinta kwance luf luf gwanin ban sha'awa......
Chapter 2 · 0% Book details