← Book details Babbar Sakayyah Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 11

Sashe 3

Babbar Sakayyah Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Dan giman Allah baba kataimaka Mana wallahi bansan inda zamuje ba idan ka koremu bamu dakowa, "katai maka mana duba kagani mahaifiyata bata da lafiya bazan iya daukar taba ga kannena yara duk ina zan kaisu Dan Allah kaji tausayin mu Kai ma wataran wannan kaddarar Bata wuce ta fada kanka ba"

"Dakata karkimin baki ,da uban wayasa iyayen naki sun san basa da shi Amma suka bude gindi sukai ta haihuwa ay ga irinta Nan anbarki da raino da kula da gida,ke ayanzu mutuncin ki kenta kina gidan aurenki amma gashinan sanadiyyar iyayenki kin kare agida bautar yara metseeeeew "yayi tsaki yajuyar da keya.

Wani matashin saurayi ne n'a hango Yana karasowa inda suke tare da cewa "malam lafiya kasa yarinyar mutane agaba tana rokar ka kamar Wanda zaka Bata aljanna?"

"To uban iya kudina zasu bani idan kuma Kai zakabiyani bisimillah" "nawane kudin naka"? dubu biyar ne" oky ya saka hannu a aljihu yaciro sabbin kudi naira dubu biyar yabawa baba "shiko baba bayan ya karbi kudin juyawa yayi yace "Allah ya taimakiku Amma wallahi da yau saikun barmin gidana da ansan baza a iya kula dakuba uban wayasa a haifeki" yakarasa fadar Haka Yana tafiya.

Itakuwa Amra kallon sama tayi Tace "ya Allah kaganmu Kuma kasan halin da muke ciki Allah ka dubemu nasan cewa bawai baka sonmu bane yasa ka jarrabemu da kaddara irin wannan,yo ya Allah Allah kada kasa nashigar da kaina wata hanyar da badaidai ba domin nasamu kudi" tana gama' fadar Haka tadago ta kalleshi idonta cike tab da hawaye Wanda sukai mata gaja gaja afuska, kekkewar fuskar Tata medaukar hankali duk tayi wani irin Sabi da tsananin tashin hankali.

Kallon kekkewar fuskarsa tayi Tace" Abdul kayi hakuri da abin da zanfada maka nasani cewa kana Sona Kuna taimakon mu, lokaci yayi dayakamata muyi bankwana da junanmu Abdul inasonka bawai bana sonkaba Amma kaje kanemi wadda take da gata ba Irina ba ka aure wanan shine kadai halaccin da Zan iya maka kayi nesa da rayuwarmu Nima Zan dauke "yan'uwana muje muyi rayuwarmu aduk inda Allah ya kaimu' tana maganar tana kuka kamar ranta zai fita.

Shiko Abdul da tunda amra ta fara maganar yaji jiri na dibansa kansa Yana juyawa yace"Dan Allah amra karkimin Haka wallahi inasonki kingafa saura kadan nasamu ayki Wanda za adinga biyana dubu dari duk wata uku kingani zai ishemu muzauna harma nakula da mahaifiyar ki da "yan'uwanki koya kikace"! Uhm! Abdul kenan naso ace nima yargata ce Dana yarda n'a aureka domin samin namiji kamarka saï antona Kai daya tamkar da dubu addu,ar da zanmaka Allah ya baka mata tagari wadda zata soka fiye da yadda nake sonka ,inason kasaka aranka kobayan natafi nayi nisa da Kai bazantaba mantawa da kaiba sanan zansaka a Raina komai daran da dewa zamu sake haduwa, Abdul kazo garinnan karatu ne inason tun daka kammala karatun ka to ka koma gida domin ka cigaba da sana,ar ka acan nabarka lafiya ",tana Gama fadar Haka batajira amsarsaba ta shiga gida aguje ta fada bandaki domin batason kayaya mahaifiyar ta ko kannenta suga tana kuka ko damuwa sabinda suma karsuji damuwa,hakan yasa ta durkushe a bandakin tashiga rusa kuka kamr ranta zai fita " bayan ta gama kukanne yasa tayi Zaman dirshen a bandakin tashiga tunanin abin da yakamata tafara kan kudin hayar da abdul yabiya ya kare musu, anane ta yanke shawarar zata dinga fita titi tanayin sana,ar Awara domin ta dinga ciyar da "yan,uwanta , tashi t'ai zata futa daga bandakin kawai saï kannenta NINEE da NABEHA suka fado mata Arai jitai ajikinta kamar basa cikin koshin lafiya ,Can Kuma sai ta girgiza Kai alamar a,a domin tanada tabbbacin ABBO FAHIMNA zata ruke "yan'unta da kyau.

Tun da Amra ta juya tabar gurin ABDUl ya tsirawa macacciyar kofar gidan Ido ,sosai yake kallo cikin gidan da kewawan idanunsa masu Kama Dana mage masu daukar hankalin duk wata mace da takalli abdul sai tasake kallonsa duk da kana kallonsa kasan Akwai rashin kwanciyar hankali atattare dashi garashin aykinyi me karfi Amma duk da Haka tsantsar kewun da Allah ya Masa be fasa bayyana a gareshi ba.

Zuyawa yayi tare da runtse idonsa ya furzar da iska daga kekkewan bakinsa zuwa waje cikin zuciyarsa kuwa indakasa garwashi Dan tafasa ,gabaki daya yaruga da ya dauki son duniya ya mikawa Amra gashi Kuma yadda Allah yayi da rayuwarsu yanzu kenan yazaiyi bayan Amra ita takasance rayuwarsa ,bashi da wani zabi Wanda ya wuce ya koma kasarsu ta hayhuwa wato CEMARU .

Tom tun da dare ya farayi Abdul yashiga kiciniyar hada jakar kayansa domin tafiya gida .Babu laifi Abokinsa Yusuf yayi mamakin jin tafiyarsa domin ayadda sukayi da abdul yace indai zaibar doguwa to file zaitafi da amaryarsa Amra , numfasawa Yusuf yayi daga saman gadon su wada suke kwana subiyu yace" ABDUl inazaka je kardai kacemin gida zaka tafi?" "Yes kafadi gaskiya gida zankoma kuma yau Dinan bakeso binjirgin asba banason nadada ko awa 4 ne a garinnan " "what Abdul lafiya kuwa meyayi zafi haka" "Babu komai kawai sonake naje Naga gida " "a,a Abdul kada ka boyemin wani abu mana ki Babu komai mu ayanzu munzama daya to meyasa bazaka iya fadamin matsalar kaba?" Uhm! Abdul yayi kwafa sannan ya zauna tare da numfasawa yace" Yusuf Amra " "to meyasami amran ko dai wani abune yafaru da ita ban Sabi ba?" "A,a Babu abin da yafaru da ita "ananne ya kwashe duk yadda sukai da amra ya fadamasa Sannan yakara da cewa" Yusuf kafi kowa sanin cewa inason Amra sannan bani da wani Buri wan da yawuce na aureta domin Naga rayuwarta ta inganta sai dai kash wannan kaddarar ta gifta agaremu duk da bansan me ubangiji ya tsara game da muba Amma ni Abdul inaji ajikina Amra matatace "idan ko bansami amra ba nayi wa kaina Alkawarin kamar yadda Amra zata zauna Babu sure domin faranta ran mahaifiyar ta da "yan,uwanta to ni ma bazanyi aure ba harsai najirata duk ran da suka girma ta aurar dasu kannenta maza suka gurma suma suka fita daga karkashin kulawarta wallahi Yusuf indai alokacin Amra rana Raye ko shekara 100 tayi batai aure ba iban ina jiranta bazan aure ba" innalillahi wa'inna ilaihirraju un Abdul kanka daya kuwa "bazakai aureba saï kajira Amra to idan katafi ta Ina zaka Kara ganin ta har da kake irin wannan furucin abakinka?" Uhm ! "Yusuf kenan amra rayuwata ce!!! Menene dalilin dayasa Amra ta hakura zatazauna Babu aure domin takula da "yan, uwanta ?" Uhm talauci mana da rashin gata "yusuf yafada, "to indai hakane duk inda zanyi duk wahala duk rintsi sainafitar da su daga wahalar da suke ciki, Kai dai abokina addu,a kawai nake bukata daga gurinka sannan zandin ga kiranka kobayan natafi kanafadamin halin da suke ciki" Tom shikkenan abokina insha Allah Zan tayaka da addu,a Allah yasa mudace Ameen.

*ADAMAWA*

*Tun da gari yayi duhu har wajen karfe 10 NINEE bata dawo daga tallaba gashi NABEHA na kwance tun Rana sai yanzu tafarka tun da ABBO FAHIMNA tasake ta Haryanzu "Yar,uwarta NINEE bata dawo gida ba ,hankalin kowa agidan idan kagani a kwance amma ban da hankalin NABEHA gaba daya hankalinta ya tashi sai baza ido take don ganin "Yar,uwar ta Amma takasa ganinta lokaci daya jikin NABEHA yayi sanyi domin duk lokacin da NINEE tatafi talla karkari karfe 5 tayi mata agida Amma gashi yau har karfe goma shadayama tana neman Yi , abu fa kamar wasa NINEE har 2:00 na dare Babu ita Babu alamarta NABEHA tayi kuka hartagaji gashi "yan gidan gaba daya duk Sun kwanta basu da wata damuwa , mikewa tayi jiki a sanyaye ta Shiga dakin ABBO FAHIMNA çan ta hangota a kwance ta hurga kafafu ta baje tana zub da yatun bacci ,jiki Babu kwari NABEHA ta karasa gaban gadon tashiga bubuga gefan gadon tana cewa" ABBO , ABBO kitashi "kamar amafarki ABBO FAHIMNA taji ana Kiran ta,zumbur tayi tamike carab sukayi ido hudu da NABEHA wadda fuskarta tayi kaca kaca da hawaye, cikin masifa ABBO FAHIMNA Tace " ke uban mène kika tasheni da daren nan Haka?" ABBO haryanzu ADDA NINEE bata dawoba" ta yi maganar kamar zatai kuka , "to sai me idan Bata dawo ba ni menene nawa aciki metseeeeew idan kika kara tashina saï naci ubanki kuma wallahi nalahira saï yafiki jin dadi" "wayasani ma ko tanacan gurin kwartayenta dallacan fuce kibani guri "matsiyata kawai"
Chapter 3 · 0% Book details