← Book details Babbar Sakayyah Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 11

Sashe 1

Babbar Sakayyah Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

BABBAR SAKAYYAH

*SADAUKARWA AL,UMMAR MUSULMAI*

Godiya

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai tsira da aminci Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya.
De

* inagodiya da gudummawar da kuka bani har nakawo wannan kan matsayin danake kai ayanzu,ina godiya ga uncle usama,Allah ya bar zumunci,ina godiya musa baffa,Allah ya baka abinda kakeso duniya da lahira,ina godiya ga mahaifiyata abarkaunata,Allah ya sanya ki a aljanna madaukakiya, daduk wanda bansamu damar ambaton sunan shi/ke ba suma ina matukar godiya Allah ya bar zumunci.

NOTE

Wanan littafin mai suna babbar sakayyah narubutashine badan komai ba saidan gera ga al,ummar musulmai,domin fadakarwa , nishadanvtarwa,ilimantarwa,duk acikin wanan littafin mai suna babbar sakayyah kamar yadda rayuwa,da duniya , ta juyamata Baya ,duniya ta ko mamata tamkar ma kabarta a zuciyarta,duk asanadin so' jama'a kada ku bari abaku labari'' kutsaya ku karanta domin sanin me ya aykata mata.

KIRKIRA

Wannan littafin kirkirarran labarine,ban rubutashi dan na muzan ta wani ba kodan na bayyana sirrin wataba, no ba hakabane, littafina kirkirarsa nai kuma nasan hakan tana faruwa, amma duk wadda taga yayi shige da labarin rayuwarta, arashin sanine.

GARGADI

Ban yarda wata tajuyamin littafinaba, kokuma adinga siyarmin da littafi batare da saninaba, banaso, banyarda wani ko wata sukarantamin book ba batare da iziniba muddum kinsan basaya kikayi ba ,wannan littafin paid book ne.

Ban amince wani ko wata akaranta min littafi ,ayi adio dinsa batare da izinina ba sannan ban yarda a sauyamin littafi ko adau wani bangare na jikin littafina ajuyashi ta kowace sigaba馃槨ngd

BABBAR SAKAYYAH

Pege 1

*"UMMA Dan Allah ki dauke ni daga gidan Inna wallahi banason zama da su basa sona musamman ma baba kabiru kullum saiya dakeni" "itakuma Inna bata barina ina yin bacci kullum duka Dan Allah kidawo Dani gurinki"

"Uhm kiyi hakuri nafisa duk abin da kukaga yafaru da mutum to Daman can Allah ya ruga da yatsara zai faru dashi, kicigaba da hakuri watara na sai labari inan insha Allah Zan zo natafi dake" cewar wadda aka Kira da umma,

Kuka yarinyar ta fashe dashi tare da zuge bayan zif din rigarta tace" Umma fa Kinga dukan da Baba kabiru yayimin Sabi da munyi fada da auwal ya fasamin Kai ya gudu,shinefa nazauna Ina kuka , shikuma Yana fitowa ya shiga marina da dukana Wai na tasheshi daga bacci hadda cewa Akuyarsa tafini hankali"

"Yan zu nafisa menene har ya hadaki da Dan,uwanki kukayi fada yajimiki ciwo,eh ke bazaki hankali ba ,ke macece fa ba namiji ba ki daina kinjini "kuma kiyi hakuri INSHA ALLAH idan nasake zuwa gida zan taho dake"

"Kodai na biyo su abbaty Kuna tahowa tun daga dorayi har kawo a kafa kinji ke macace ba namijiba"

"To umma idan fa inaso naganki Babu Wanda take bani kudin mota shiyasa nake biyosu mutaho a kafa"

"To nidai nace kidaina Babu kyau mace tadinga yawo a kafa guri me nisa..

"Insha Allah bazan sakeba umma na,Ina ikiram tayi bacci ne" uhm a,a batayi ba kafafunta keyi mata ciwo ,kinganta can sai dai a kwantar a tashar" ayya Allah ya bata lafiya to kunje asbiti"? Eh munje Amma duk Abu dayane sun kasa gane menene matsalar, har sheka mukaje gurin me gyran targade ba adaceba ,kafarma Kara sumtuma tayi"

. "To yanzu yakenan za,ayi Ina zakuje yanzu?" Akwai wani megyra a can kwandila anace Masa sarkin dauri,gurinsa zamu kaita ..

"Tom shikkenan umma Nima Bari natashi mutafi kada Inna Tace nayi dare tasa baba kabiru ya zaneni,
.

Tana Gama fadar Haka ta dauki hijabin ta Wanda ya kode ya yage tasaka sannan tayiwa mahaifiyar ta sallama suka tafi gida...

*To bayan sun koma gidane kowannensu jiki sai rawa yakeyi musamman ma nafisa da tasan Basu fada ba suka tafi, kowannen su takalmi yacire suka shiga .sanda harsuka Shiga cikin gidan, wani Dan karamin daki suka shiga suka zauna ayko suna zama,kamar ance su dago saiga baba kabiru atsaye dauke da zangamemiyar bulalarsa a hannunsa , tsawa ya daka musu yace" ki Dan kutumar ubanku Ina kuka je" baki narawa nafisa Tace uhm uhm" bamagana nake mukuba Ina kikaje?" Kuka tafashe dashi tace"gidan ummana naje" "gidan umman ki Kuma dake dawa kuka tafi wakuka tambaya? Babu kowa " uban wa yabaku kudin mota?" A,a Babu Wanda ya bamu wallahi akafa mukaje" Dan Allah kada kadakemu" kwafa baba kabiru yayi yace "wallahi duk ranar da kuka sake irin Haka saina tattaka ku"kutashi ku bani guri"ay ko dama' kamar jiran kadan suke aguje suka Mike harda ruge ruge...

Nafisa na fita Ta nufi gurin fanfo ta kunna sannan ta daura alwala bayan ta idar da alwalar dakin innarta tashiga ta yi sallah ,data idar bata tashiba sainaga ta zauna agurin ta daga hannunta sama idanuwanta n'a zubda hawaye, To dama ita nafisa idanuwanta ba farare bane jajayene kamar meciwon ido sannan ita ba fara bace sannan bazaka kirata da bakar Macé ba,hancinta bashi da tsayi hasalima babban hancinea da ita sannan idonta kananune gasu sunshiga ciki in takaice muku dai nafisa ba kekkewar bace Amma tana da nata Kyau da Allah ya bata.

Bayan tadaga hannunta samane naji tana fadar wasu kalmomi Wanda zuciyata yasa ta karye ace yarinya karama kamar me shekarun nafisa da irin wannan jarrabawar, kuka take tana cewa" ya Allah ni baiwar kace banada kowa aduniya sama dakai gabaki daya kowa baya sona"nasani kaine me jaraftar bawa da kowacce irin kaddara sai dai ni nakasance me rauni zuciyata tagaza daukar wannan abin da ake min"meyasa kaddarata tazo a Haka sunsa natsani kaina "meyasa sunsan gaskiya suke takewa meyasa suke jifana da kalmar yar shegiya bayan mahaifiyata ta tabbatarmin da ni ba yar shegiya bace saï da Aka shafa Fatiha tukunna Aka sameni" shin meyasa abbana zaiyi Haka ?"idan ni yar shegiya ce to kanina fa meza a kirashi" bayan shi Naga bawan da yake tsangwamar sa ,ko dai an boyemin wani abu game da rayuwa tane" Ya ubangiji Ina rokonka da kakiyayemin imanina kada naje na aykata irin abin da ake tunanin tanan aka sameni" tana kaiwa Nan ta shafa tare da goge hawayen idonta , innar ta dake tsaye Tana jin abin da take cewane taji duk jikinta yayi sanyi karasawa tayi kusa da ita ta zubamata ido ganin yadda fuskar nafisa ta kunbura, ga hancinta ya Kara girma ,hannunta Inna ta Kama tajanyota jikinta tashiga jijjigata tana cewa" kiyi hakuri nafisa kinji ki kwantar da hankalinki kidaina yarda da maganganun mutane"kome yafaru da bawa hakuri shine Mafita"nafisa ce ta hadiye azababben yawun da ya tarar mata a Baki jikake kutt sannan Tace" Inna Wai dagaske ni ba ta hanyar aure Aka haifeni ba?" "Uhmm! Nafisa sonwa kikeson n'a fadamiki cewa ke ba yar shegiya bace"kedin da aure Aka haifeki da hannuna n'a damka mahaifiyar ki agidan mijinta " "to idan dai hakane Inna Ina mahaifina sannan suwaye a halinsa ?" Hmm! Nafisa dogon lanari banaso kidinga min wadannan tambayoyin mahaifinki yadade da rasuwa a lokacin da yarasu shekarar ki Uku a duniya sai Kuma kaninki Auwal da aka Haifa bayan rasuwarsa" zumbur nafisa tayi ta tashi Tace"kull karki soma Inna har aba da bazan taba Yar da da wannan karyayyakin da kuke ta yimin ba domin indai har da waliyi aka daura auren ummana Dole zaikasan ce za a samu shaida ko mutum ukune ballema nasan zasufi Haka "karyane akwai abin da ake boyemin da tahanyar aure Aka haifeni duniya bazata dinga min kallona amatsayin shegiya Mara ubaba!! Tana kaiwa Nan amaganar ta tashi ta fito waje Nan sukayi karo da baba kabiru,wata uwar tsawa ya daka mata yace ke ina zakuje?"uhm uhm zanje gidan su Fatima ne " to bazaki jeba dake da fatiman kunci ubanku shegiyar yarinya kedai burinki kijamana zagi ko to Bari kiji bazaiyuwu murinka Tara shegu a gida ba Dan Haka koma ki zauna wayasani ma ko kunyi zaku hadu da saurayinki banzar yarinya shashasha kwai" Ay Allah ya wadaran mace irinki ke ni da haihuwar irinku adangin mu ay gwara barinku" yayi tsaki ya huce, runte idonta nafisa tayi zuciyarta namata zafi da tumuki ace awadan da zasu cimaka zarafi harda kanin mahaifiyar ka wannan Wace iriyar kaddarace" ya Allah blesska nunamin BABBAR SAKAYYAH akansu.

*DOGUWA*

*innalillahi wa'inna ilaihirraju un"umma dagaske wai baba ya mutu"Dan Allah kada kicemin yatafi inda ba,a dawowa umma umma kimin magana Mana help me"

Umma wadda ke zaune idanuwanta a kakkafe bata ko kiftawa sai dai ruwan hawaye wan da yake zarya a kuncinta hannunta kuwa sai rawa yake kamar mazari.

Wata matashiyar buduwar wa ce wadda akalla shekarunta zasuyi 16 dakin tashigo aguje tare da durkusawa agaban ummansu ta fashe da kuka wan da ya tashi hankalina matuka magana takeyi bakinta harrawa yake zuciyarta na tukuki da zafi ,hannu tasaka ta rike makogoron ta Dan jitake kamar ana saka wuta ana soya Naman cikin makogoronta ,kuka take tana cewa, "umma kije za a tafi da baba shikkenan bamuda gata umma mutuwa tamana yankan kauna munshiga uku wallahi umma asirinmu ya tonu an bankademu yanzu wazai taimaka Mana bamu da kowa aduniyar Nan sai baba shima gashi mutuwa tamana yankan kauna"tana kaiwa Nan amaganar ta Kara rushewa da kuka,

Gefe guda Kuma wasu yarane azaune mata da maza Kai Kana ganinsu kaga yaran mutum daya kuma buzaye irin usul Dinan.

Wata budurwar ce Takara shigowa ta nufi gurin wadannan yaran tana kallonsu idanuwanta na zub da kwalla, da alama dai Tasha kukan har tagaji inda yaran suke ta nufa ta zauna ta saka hannu ta dakko "yarkaramar yarinyar "Yar shekara 4 da rabi. A kafadar ta ta dorata tare da rungumeta tsam Tana jin tsausayin RAYUWAR su na Kara shigarta ,ahankula ta juya ta kalli dukkan kannenta da mahaifiyar su yadda sukeyin kuka abin tausayi runtse idonta tayi a kasan makogoronta tace. ,"Wayyo ni Amra meyasa rayuwa zatamana haka"
Chapter 1 · 0% Book details