← Book details Babban Goro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 19

BABI NA GOMA SHA BIYAR__15

Babban Goro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ta faɗa saman gado tana kuka,ta tsora ta sosai da yadda taga Saif irin wannan ranar take gudu, daman hausawa suncd rana dubu ta ɓarawo,ɗaya ta mai kaya.
Wayarta dake saman kujera ta baɗo mata a rai,cikin rawar jiki taje ta ɗauka, ta shiga neman number Mummy. Sai da tayi mata kira biyu sannan ta ɗauka,


“Dan Allah Momi kizo gidan nan yanzu ki ceci raina”


Cikin kuka take maganar tana gurfane a kasa kamar mai rokon gafara. banji mi akace mata ba na dai ga tana girgiza kai


“Eh Momi Saki zaiyi dan Allah kizo yanzu”


Nan ta kashe wayar, ta faɗi kasan carpet gana kukan dake zuwa mata har cikin ranta, ko kaɗan Huda bata son taga Saif yayi fushi da ita, musaman yanzu da take fushin nashi har a fuska, Saif mutun ne mai hakuri duk abunda take masa yakan shanye ya kyale ta idan har taga fushinsa a fili toh lallai ranshi ya ɓace sosai.


Cikin mintuna Ashiri da wani abu Momi ta iso gidan,Huda najin tsayawar Motar ta ta fito da gudu daga ɗakin ta nufo downstairs, Saukowarta yayi dai-dai da shigowar Momi falo, faɗawa Huda tayi jikin Momi tana kuka


“Faɗa min mi kikayi masa miya haɗa ku?”


Momi sai Tambayar take abunda ya faru,ita kuma ta kasa magana sai kuka take, duk hankalin Momi ya tashi,


“Saif ɗin yana nan ne?”


Daker ta iya ɗagawa Momi kai sai wani kara narkewa take kamar wadda akayi mutuwa


“Saifullah! Saifullah!!”


Kira Momi take kwala mishi kamar zata tada gidan,
Yana daga kwance ya soma jin kiran bai amsa ba dan bai ɗauka Momi bace duk da yaji kamar muryar ta, Sai da yaji kiran ya tsanan ta sannan ya tashi a kasale ranshi kuma aɓace ya nufi kofar fita,
Tsaye Yayi bakin Stairs ɗin yana kallon Momi da ke lallasar Huda tana harararsa, haka ya nufo downstairs yana mamakin abunda ya kawo Momi yanzu a gidan dan ba kasafai take zuwan gidan ba. Wata zuciyar tace masa Huda ce ta ta kira ta, Baki ya ɗan tsosa a ransa yana zata iya tunda ba kunya ne da ita ba,


Har ya Karaso Momi bata daina Harararsa ba, cikin girmamawa ya gaisheta


“Momi ina wuni”


Bata amsa masa ba sai kawai ta haushi da masifa,


“Mi Huda tayi maka da zaka sake ta?”


Zaunawa yayi saman kujera yana maida numfashi, ganin hakan yasa Momi ta katsa masa tsawa kamar wani karamin yaro


“Ba da kai nake magana ba kayi min shiru ko nima shashancin zaka yi min?”


D'agowa yayi ya kalleta,


“Momi..-”


Sai kuma yayi shiru, Kallonsa Huda tayi da jajayen idanunta kamar munafuka wani ɓangare na zuciyarta tsoron abunda zai fito bakinsa take dan tasan Momi ma bazata raga mata ba sai tayi mata nata faɗan,
Ido cikin ido ya kalleta yana magana da Momi


“Momi matsalar mu ce da kika sani ta baya Huda ba zata taɓa chanajawa ba sam,nayi faɗa har na gaji bata ji ni kuma na gaji gaskiya da halinta kuma nasha faɗa miki tun baya yau ba”


Zaunar da Huda Momi tayi saman kujera sannan itama ta zauna tana kallonshi


“Saboda ba kasan Miye Aure ba ko? Shiyasa kake son saki a rayuwar ka nayi bakin cikin jin haka daga gareka Saifullah ban taɓa sanin cewa bakan mutucin Aure ba sai a yau,
Duk abunda zaisa Namiji ya saki matarshi Babban abun ne, Amman kai ka ɗauke shi ba komai ba miyasa kake son maida kanka wani irin kalar mutun ne?”


Gashin kansa ya shafa daman yasan indai faɗa ne sai Momi tayi masa musamman yanzu da take ganin Huda bata daɗe da dawo ba. ɓangaren Huda kuma daɗi takeyi tana hamdala da Saif bai faɗi dalilin faɗan nasu ba, ita kanta tasan tayi sa'ar miji dan ba kowa ne Namiji ne zai iya ɓoye sirrin matarsa ba, duk da a koda yaushe Iyaye sukan faɗa mana idan faɗa ya shiga tsakanin ka da Iyalinka toh ka barshi tsakanin ku, dan idan kuka faɗa ma Iyaya koda ku kun shirya kanku ko an shirya ku zaku iya manta abun ammman Iyaye basu manta ba.


A hanlaki ya furta,


“Momi bafa sakin ta zanyi ba kawai ina bata tsoro ne wasa nake mata”


Nan Momi ta saki baki


“Wasa kuma au shi sakin har wasa ake dashi? kasan mi kake faɗa?”


Salon faɗan da take masa sai ya chanja, Shi dai kanshi na kasa har tayi ta gama sannan ya shiga bata hakuri


“Naji duk abunda kika faɗa Momi kuma hakan ba zai sake faruwa ba In'sha Allah Allah ya huci zuciyar ki”


Tashi tayi tana faɗin,


“Kowa dai yayi na gari dan kansa kuma duk abunda kayi wa yar wani sai anyi ma taka, ya dai kamata kayi ma kanka faɗa kasan ciyon kanka ka rika Y'ar mutane da mutunci ba ka wulakanta ta ba”


Juyowa tayi gurin Huda,


“Ke kuma duk abunda kika san yana kawo miki matsala da mijin ki ki daina ki guji ɓacin ransa idan zaki iya kunga tafiya ta”


Bata tsaya jiran mi zasu ce ba tayi tafiyar ta suna mata a sauka lafiya,
Bayan Fitar Momi Huda ta nufo Saif da nufin masa magana ,sai kawai taga ya tashi tsaye yasa hannayensa aljihu ya nufi upstairs,
A hankali ta jingina da kujera tana kallonsa har ya shiga bedroom ɗinsa.


Yana shiga sai yaji duk wani haushi na Huda da yake ji ya karu, ba damar ya sake mata faɗa yasan kiran Momi zatayi ta faɗa mata shi kuma sam baya son Momi taga kamar bai ji maganar ta ba. Can guraren Azahar ya shirya cikin manyan Kaya ya ɗauki makulin motarsa ya bar gidan.


***** ***** *****
Bai shigo ba sai dare. a falo yaci karo da ita kwance saman doguwar kujera sanye da wata rigar bachi mai ɗaukar hankali, baibi ta kanta ba duk da tayi masa sannu da zuwa, haka ya nufi ɗakinsa ba tare daya amsa ba.


WASHE GARI.................
Tun takwas da rabi ya bar gidan dan kwata-kwata baya son huda ta sashi a ido danshi fushi yake da ita bilhakki.
Huda kan bata ma san fitarsa ba dan bata tashi ba sai goma na safe, tana tashi ta nufi kicin ta haɗa masa karrin kummalo dan a zaton ta yana nan tunda bai saba fita da wuri ba. Bayan ta kare ta nufo ɗakinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta feshe jikinta da turare, sannan ta nufo ɗakinsa,
Haka ta fito sululu kamar hawainiya ta koma ɗakinta idon cike da ruwan hawaye, Tana shiga ta faɗa saman kujera tana share hawaye, wunin ranar wuni tayi cikin ɗaki, Sai kusan La'asar ta fito koshi dan yuwar da taji tana matsa mata lamba ta nufi dinning,ruwan tea ɗazun ta zuba tasha ta sake koma wa ɗakinta.


***********
Saif bai shigo gidan ba sai da ya tabbatar da ta isa yin bachi, rashin ganinta a falo ya tabbatar masa da hakan. wutar falo ya kashe ya wuce ɗakinsa,
Washe gari ma haka yayi mata koda ta tashi ya ficewarsa duk da yake ta tashi da wuri yau, abunka da wadda bai saba ba sai duk tabi ta shiga damuwa, sam baya son Saif ya fita safgarta dan ya riga ya saye mata jiki da zama tare dashi,daga iya zuwa yau duk ta wani chanja ta koma wata kala har da yar ramar rashin cin abincin da take dan iya karta ruwan tea,
Tunani take tayi yadda zata filloma lamarin, Dan tasan haka ɗin da Saif yake mata ba karamin fushi yake da ita ba, kuma shawo kansa sai ta shirya, bayabda saurin fushi kan amman kuma idan yayi yayi kenan sai kuma wani ikon Allah.


***** ***** *****


MINAL............


K'is! k'is!! k'is!! kake ji taunar cingan ɗin da Minal take tana danne-dannen wayar dake hannunta, Kairat na zaune kusa da ita tana rubuce-rubuce jin abun yayi yawa yasa taja tsaki,


“Haba Minal dan Allah ki jefar da cingan ɗin nan tun ɗazu kin damu mutane da taunar cingan kamar wata tsohuwar karuwa”


Harara Minal ta watsa mata,


“Wadda ya raina tsayuwar wata a hawa yake ya gyar idan zai iya ko idan kuma bazai iya ba sai ya zuba ido”
Kairat zatayi magana Talatu ta shigo Gardem ɗin tana faɗin


“Minal ga abokin ki can harabar gida yace a kira ki”


Da sauri ta tashi tana faɗin,


“Toh nama bar miki wajen ci tsinci abinda zaki tsinta”


Tsaye ta tararda shi jikin Mota yana dannar waya, Rumgume shi tayi kamar yadda ta saba,


“I miss Deen?”


Lumshe ido yayi naɗan mintuna ya buɗe ya shafa kanta,


“I miss you too Deen you look so pretty”


Murmushi tayi ta sake shi,


“Thank you ina ka fito?”


“Gida nayi miss ɗin fita dake ne kwana biyu bamu fita ba”


“Oh Deen shekaranjiya fa muna tare”


“Eh but a gida ba waje ba yawo fa nake nufi”


Hannayenta ta ɗaga sama


“Fine indai wannan ne karya dame ka shiga mota muje indai yawo ne”


Murmushi yayi ya buɗe Motar ya shiga, ita kuma ta zagaya mazaunin gaba ta shiga ya kunna motar suka kama hanya.


#Oneheart
_SHOW ME WHAT I WANNA SEE YOUR VOTE AND COMMENT AND DON'T FORGET TO SHARE_
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


NA


KHADEEJA CANDY


_Another one for you ROSY LURV my shinkafa jallof_


WATTPAD @khadeeja_candy
Chapter 12 · 0% Book details