← Book details Babban Goro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 19

BABI NA GOMA SHA UKU___13

Babban Goro Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

“Wai kina nufin bachi zakiyi.?”
Idonta a lumshe ta ďaga mishi kai alamar eh,
“Toh karma ki fara kwana biyu fa haka kike min kina barina online gurin za6a miki Cake har biyu na dare kina sharar bachinki kuma yanzu kice bachi zakiyi ai nine n chanchanci haka”
Maganar yake yana wani shafa bayanta ita Kuma tana kwance saman cinyarshi, ďaga kai tayi ta kalleshi
“Anjima kuma zaka za6a min rigar da zan saka da takalmi”
Murmushi yayi,
“Lallai yarinya daďi yayi miki yawa kiji daďin sake yin bachi ki barni ko?”
Zatayi magana wayarta dake kan flat table tayi ringing, da sauri ya ďaga ta daga jikinshi ya nufi gurin da wayar take, juyowa yayi bayan ya duba wayar yace
“Number ba suna”t
Tana jin haka tayi saurin tasowa kamin ta karaso ya danna picking ya kara a kunne,
Yanayin fuskarshi naga ya chanja alamar mamaki,
“Wanene.?”
Da sauri naga ya kalli wayar ya kalleta
“Muryar naji wai hello Dear nace wanene ya kashe wayar”
Faɗuwa gabanta yayi da sauri ta karɓi wayar ta shiga dubawa,
“Ni ban ma san mai number ba ina jin wrong number ne”
Kafaɗunshi ya ɗaga ya rik'a fuskarta ya sakar mata kiss a goshi,
“Bari naje shirin aiki karna zama doja akai karata gurin Dad ok?”
Kai ta ɗaga mishi yayi mata murmushi ya nufi ɗakinshi,
Da kallo ta bishi sai da ya shige sannan ta dafe kirjinta ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kicin tana dannar wayar,
Yana shiga ya cire kayanshi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya shiga shirya kanshi,
_DiLLL_ wayarshi tayi kara alamar sako, kallon wayar kawai yayi ya ɗauke kai sai da ya gama shirinshi tsaf sannan ya ɗauki wayar ya duba,


``` HELLO Mr. S. B_B


Minal Alhasan ce bansan kallaman da zanyi amfani dasu wajen gode maka ba na sani cikin farin cikin da ban taɓa mafarkin shiga ba na gusar min da duk wani bacin rai na, ka sami nida Mahaifiyata cikin farin ciki mun koma kamar yadda muke a da na gode sosai Saif Allah ya saka maka da Alheri bazan taɓa mantawa da kai ba.


FROM MINAL!```


Murmushi yayi yasa wayar aljihu ya fice,


“Wai mi kike ma murmushi ne?”
Kairat ta tambaya,
Murmushin ta sake yi ta mika mata wayar,
“Duba da kanki”
Ba musu ta karɓa tana dubawa,
“Oh Sis yanzu ki rasa irin text ɗin da zaki tura Mishi sai irin wannan ?”
Fuskar mamaki tayi “Mi kike nufi?”
“Toh yanzu dan Allah miye abun burgewa cikin wannan massage ɗin sai kace wata yar kauye”
Tsaki taja ta fisge wayarta ta tashi da nufin barin ɗakin,
“Aikin banza daman ai ni ban taɓa yin abu kika yaba min ba kullum ni ban iya komai ba”
“Matsalar ki kenan ba ada ikon faɗa miki gaskiya sai ki hau tsakanin da Allah ni banga abun burgewa cikin wannan message ɗin ba abu kamar ba wace tayi karatu a waje ba”
Tsakin ta sake ja a karo na biyu ta watsa mata harara ta fice tare da jan kofar ɗakin da karfi,
Dariya kawai Kairat tayi ta cigaba da dannar wayarta.


*******************


Bashi ya dawo gidan ba sai 9:30pm a gajiye ya shigo, kai tsaye ɗakinshi ya nufa ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito jallabiya ya ɗauka ya saka tare da ɗan short jean sannan ya fito ya nufi ɗakin Huda,
Zaune ya tararda da ita laptop na gabanta tana faman duba wasu riguna, ko sallamar da yayi bata amsa mishi ba,
Kusa da ita ya zauna bayan ya sakar mata kiss a kunci yace
“Dear mi kike yo haka baki masan na shigo ba?”
“Wallahi ina ɗan duba wasu riguna ne da zan saka ya aikin?”
“Alhamdulillahi aje wannan aikin muje muci abinci yunwa nake ji”
“Nima fa yunwar nake ji daman kai nake jira ka dawo”
Hannunta ya rik'a
“Toh na dawo tashi muje downstairs”
Kallonshi tayi “Take away fa nake nufin kayi mana dan tun abincin rana ne da Larai ta dafa kuma faten doya kasan kuma baka sonta ni kuma ban samu na dafa komai ba”
“A'a wasa dai kike ko?”
“Wallahi da gaske nake ba kaga abunda nake ba tun ɗazu nake Online ban samu kayan da suka yi min ba”
Sam bai yarda ba tashi yayi ya nufi downstairs,
Sai da ya duba ta tabbatar da gaske take sannan ya sake nufo ɗakinta rai a bace, bakin kofa ya tsaya fuskar shi a ɗaure,
“Huda wannan wane irin wulakanci ne ace ni da gidana amman bana da halin jindaďi kamar sauran maza wannan wace irin rayuwa ce?”
B'ata fuska tayi “Haba dear wai miyasa baka ganin tausayi nane wai aikin gidan nan kace baka son kowa yayi sai ni tun safe fa nake ta kai da kawo cikin gidan nan ga wannan aikin dake gaba na shin dame kake son naji dan Allah kuma wannan faďan ma kasha yinshi kaga bazan iya wani abun ba tunda gidan mu bamu saba da aiki ba akalla yanzu nayi shekara biyu gidan nan kullum abu ďaya ya kamata ka ďaga min kafa mana”
Wani murmishin jin haushi yayi ya kađa kai kawai ya fice,
D'akinshi ya dawo ya faďa kwance saman gadon yana ta tunanin magagganun da Huda tayi mishi da kuma hali irin nata ,lokaci lokaci yakan ya tsaki yana gwaďa kai hannunshi na hagu na saman cikin shi,
Jin yunwar ba zata barshi ba yasa ya tashi ya ďauki keys ďinshi ya fice.


ROYAL KING HOTEL............
Minal ce a tsaye kusa da reception, sanye da doguwar riga ta farin material mai kyali da yar hula sai kalle kalle take kamar bakuwar gurin,
Juyowar da zatayi ta hango tafe, tun kamin ya karaso ta rika sakar mishi murmushi, shi kan baia san tana yi ba dan hankalinshi kwata kwata baya jikinshi,
Ganin zai wuce ta yasa ta kira sunanshi,
“Saif...”
Juyowa yayi yana neman mai kiran sai a lokacin ya lura da ita, murmushi ya sakar mata
“Minal mi kike yi a nan?”
“Ai kaine ya kamata nayi ma wannan tambayar”
“Ni ai kinga Namiji ne Take away nazo yi ke da wa kika zo nan?”
Hannu sata a baki kamar wata karamar yarinya
“Ni da Mummy tana gurin biyan kuďi”
Hangen Mummy tafe yasa ta karaso kusa dashi tana nuna ta
“Gama ta nan zuwa”
Kallo đaya yayi ma Minal ya ɗauke kai ya kalli Dr. Salamatu da ta k'arasa kusa dasu,
“Good evening Dr. Salamatu”
Fuskarta a sake ta amsa mishi
“Evening Saif ya kake?”
“Lafiya kalau ya hak'uri ya abubuwan?”
“Da godiya na gode sosai Saif Allah ya saka maka da Alheri”
Da sauri ya tari numfashi ta
“Oh ai babu komai Allah ya tsare gaba”
Minal ce ta amsa da 'Amin' ta rik'a hannun Mummy suka nufi kofar fita shi kuma ya kunna kai cikin Hotel ɗin,


WASHE GARI..........
Tunda Minal tayi sallah asuba bata koma bachi ba sai kawai ta nufi kicin, abubuwan duk da tasan Mummy naso gurin breakfast su ta shiga haɗa wa cikin taimakon Allah kuwa ta kammala komai in time,
D'akinta da dawo ta cire kayan bachin dake jikinta ɗaura tawul ta shiga bathroom, bayan tayi wanka ta fito bata tsaya shafa komai ba tana tsane jikinta ta nufi wardrobe ta saka dogon wando jean da riga T shirt green color ta ɗauki wani guntun ribon ta ɗauke gashin ta sannan ta nufo ɗakin Mummy,
Bata tararda kowa ɗakin ba, motsin ruwan da taji ya tabbatar mata da tana bathroom guri ta samu ta zauna tana kallon kofar banɗakin har ta Mummy ta fito,
“Mummy good morning”
Da murmushi Mummy ta amsa
“Morning Minal how are you har kin tashi?”
“Eh tun ɗazu ai nima na haɗa breakfast”
Zaunawa Mummy tayi kusa da ita tana shafa kanta
“Allah yayi miki albarka Minal ya kara miki lafiya ya shirya min ke”
Hannunta Minal ta rik'a “Amin Mummy tashi muje kici abincin”
Ba musu Mummy tashi suka fice,
Downstairs suka nufo, kamin su k'arasa saukowa Minal ta hango Kairat zaune tana breakfast, aiko ba shiri ta saki hannun Mummy ta nufo Dining area da gudu, Kairat na ganinta ta tashi da sauri ta zagaya ta baya tana dariya,
“Minal am so sorry inajin yunwa ne kuma tsohuwa tace min ke kika girka da kanki shine naci naji idan yayi daɗi”
Dariya Mummy tayi ta kalli Kairat
“Nan kika kwana ne?”
“A'a Mummy yanzu na zo ina kwana”
“Lafiya kalau ya gidan?”
Kujera Minal ta jama Mummy
“Mummy zauna a nan kici lokacin zuwa aikin ki yayi”
Nan ta juyo gurin Kairat
“Ke kuma ki wuce ɗakinki ko ki koma gida”
Mummy ta zauna tana faɗin,
“Babu inda zataje kin taɓa ganin mutun ya bar gidan su yaje wani gurin?”
Fuskar shagwaɓa Minal tayi
“Toh Mummy taje ta haɗa ma kanta breakfast ɗin dan ni ba zata ci min abunci b katuwa da ita”
Mummy zatayi magana tsohuwa dake kokarin shigowa ta rigata,
“Yau ku ji min Minal ke da nake dafa miki kina ci fa”
Juyowa Minal tayi “Ke tsohuwa mi ya kawo ki nan, kuma ni ai ba wani girma ne dani sosai ba balle kice ita fa tayi uku ɗina haka kawai zan dafa mata abinci”
Tsohuwa tace "Ai ba ita kika dafa ma Hajiya kika dafa ma Hajiya kuma uwarta ce dan haka dole ta ci”
Dariya Kairat tayi “Yauwa tsohuwa faɗa mata dai cin abinci kan har na gama dai dai kiyi hak'uri”
Mummy dake cin abinci ta kalli Kairat “Zauna kici tun bai huce ba yar mamarta”
Kujera Kairat taja ta zauna tana yima Minal gwalo, ɓata fuska Minal tayi kamar ta fasa kuka
“Har da ke ko Mummy”
Mummy ta kalleta “Yau toh ya zanyi Minal ya tace fa”
Rumgume hannayenta tayi “Toh duk ku tashi ma na fasa baku abincin”
Tsohuwa ta rik'e baki “Har da Hajiya?”
“Eh har da ita kuma kema ba zaki ki ci shi ba”
“Yau ni tsohuwa dani mi zanyi da kwai da plantain ni tun da safe na karya da koko da kosai kuma kuma na ci ɗumame dan haka ki rike abinki indan ni”
Fuskar shanu Minal tayi ta koma saman kujerar parlor ta zauna, dariya tsohuwa tasa mata ta nufi kicin tana gyara tsintsiyar da ta shigo da ita, Mummy da Kairat ma dariya suka rik'a yi mata Kairat har da wani rawar kai


Sai da Mummy ta gama cin abinci ta sannan ta tashi yana hamdala tace “Minal Allah yayi miki albarka abincin nan yayi daɗi kin iya girki”
Kawar da fuska tayi “Nidai Mummy kyale ni bazan sake dafa miki ba”
Murmushi Mummy tayi nufi upstairs tana faďin “Na kyale ki kinga ma tafiya ta amman dai ayi hakuri a sake dafa min yayi daďi kin iya girki”
Wink Kairat tayi mata da ido tace “Mummy so fa take ta nuna miki ta iya girki ayi mata Aure”
Filon kujera Minal ta ďauka ta jefe ta dashi “Tashi ki bar gidan nan busa kawai kibar biredi”
Fashewa Kairat tayi da dariya “Ai ni bana da Wata muguwar kiba dan kina kamar ki kare ne kike ganin kiba ta amman ni daidai nake yanzu ma maza son fi son masu ďan jiki ba irinki ba masu kamar su kare”
Minal tace “Wallahi karya ne anfi son irin mu na gaban mota”
Kai Kairat ta girgiza,
“Ki yarda kawai Allah anfi son irin mu yanzu idan muka auri miji ďaya sai yafi sona dake”
Sai a lokacin minal tayi dariya
“Lallai Yarinya waya faďa miki miji ďaya zamu aura har ya fi sonki dani? Ai ni bazan aure mijin wata ba wata kuma ba zata auri miji na ba”
“Toh wanene mijinki wanene kuma mijin wata?” Kairat ta tambaya,
“Idan na auri mai mata toh mijin wata ne ni na aurar mata miji dan zaki ji ance mijin wance ta aura, idan kuma wata ta auri mijina ita ce ta aurar min miji dan haka bazan auri mijin wata ba saurayi zan aura ba kuma zan bari wata ta aurar min miji ba”
Tasowa Kairat tayi ta dawo kusa da ita tana zolayar ta,
“Koma minene kara ki chanja da gaskiya miji ďaya zamu aura”
“Lol Ke kama kanki ba zaki iya kishi dani ba dan ni bana son kishiya”
“Yau ai nima ba kanwar lasa bace kinga tun nan mun saba da munje can cigaba kawai za muyi”
Da dariya tsohuwa ta fito kicin tana zolayar Minal, daďi Kairat taji ta samu mai kama mata suka rika caccakar Minal tun tana ramawa har ta gaji ta samu su ido,
Suna haka Mummy ta fito da shirinta na zuwa office, tana sauko downstairs Kairat ta tare ta “Mummy dan Allah a aura mana miji ďaya da Minal”
Watseta Mummy tayi “Ke dan Allah rufe min baki tun ďazu ina jinku kun tarar mata har da tsohuwa kuna takura mata yar baiwar Allah”
Daďi Minal taji, “Ai dama kin aura mana miji ďaya ďin da ita wallahi da kin sha wahala”
Minal ta karasa maganar tana hararar Kairat, kallonta mummy tayi “A haka Minal da wannan jiki”
B'ata fuska Minal tayi “Oh Mummy har da ke ko?”
Da fata Mummy tayi “A a ina nufin kina da kiba”
Ture hannun Mummy tayi ta nufi upstairs, Kairat da tsohuwa suka sa mta dariya har Mummy sai da tayi mata dariya sannan ta fice Kairat nayi mata Allah ya kiyaye,


Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin farinciki da kwanciyar hankali da kuma jindaďI,
Mummy tafi kowa farin ciki da daman haka take son ganin farincikin Minal shine kwanciyar hankalinta, yadda suke rayuwa yanzu har yafi na da kamar ba uwa da ya ba sai ka dauka kawaye ne ko kuma abokanin wasa tsakanint da Mummy har ma Kairat.


*I'm still on wattpad @khadeeja_candy*
_Don't forget to vote and comment_
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


NA


KHADEEJA CANDY
Chapter 10 · 0% Book details