← Book details Auren Lagos Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Auren Lagos Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

To A al'adar gizimawa sai and'aura aure akekai lefe, saboda haka yau gidan su fahad zasukai lefe Wanda lefen yana'bangaran hajiya asma Wanda sauda tace sai anrage kayan yayi yawa
Laura kuma tak'i yarda amma hajiya asma da sauda saidasukarage kayan afad'arsu wai ai tinda yace ya yafe kayan d'aki suma bazasukaimusu kaya mai yawaba🤔

****** ***** ******

Ankai lefe gidan su amarya akwati
Shida masu kyau da tsada kayan cikiko inmuntsaya lissafawa macinye sauran lokacinmu kowa yak'isyata aransa kawai. Ahakanma anrage kayan amma ba'abun da babu, mutane natasan barka

Lokacin dinner nayi akakai kowa
Sai ango da amarya sukarage
Wanda imran shi yad'auko ango sukabiyo sukad'auki amarya da babbar kawarta rahama domin kuwa amarya tace tare zasutafi

Suna isa akafara shagali dama su'akejira, inda akak'ira sa'idu borno, yawak'e amarya da ango
Anci ansha anyi 'barin naira tako wani 'bangare
Inda amarya da ango sunyi ankon
Shadda 'yarmali sunyikyau har sungaji, taro yawatse lafiya and'auki amarya anmaida ita gida nsu, akan sairanr tafiya LAGOS kuma
Amma anti sauda tace " k'aryane dole ad'auko amarya a kawota gidansu kafin tafiya LAGOS
Saboda ko auren imran saida akakawo ilham
'Yar gidan danmajalisa gidansu kafin suwuce damaturu
Bare matar fahad 'yar matsiyata
Hakataita kunfar baki dole akaje akad'auko kairiyya awanan daran akakawota gidan su fahad a'bangaran Fahad
Aka'ajiyeta Allah yasa da kaya a'bangaran.......✍🏼

Please read & shere

Allah yajikan iyayenmu🤲
AUREN LAGOS

Romantic love story & short story👩‍❤‍💋‍👨


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
```{{The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities}}```
https://mobile.facebook.com/Zauren-Home-Of-Qualities-Writers-Association-106248871038663/

*⚜{{H.Q.W.A📚}}*

*NA* Karimatu Abdulhamid ( mommyn minal)

[ thee end]

Wanan page sadaukarwane ga
'Yan home of Qualitei's writer's
Association
Allah yatamaki k'ungiyarmu 🤲
Inayinku over💋

Page 40

The last page

Ankai Amarya kairiyya, 'bangaran fahad
Awanan Daren Allah yasa dakaya a part d'in
Itada k'awayenta Rahama da basira da k'anwarta kausar, sai cousin d'inta mata subiyu, suka kwana tare domin kuwa Al'adar 'yan jihar yobe state ne sai anyiwa amarya kwanan d'aki Ranar da'akakaita
Washe gari sai ango yashiga d'akin amaryarsa

To" hakan takasance da kairiyya, yaukwananta d'aya gidan su Fahad, kuma yaune sukewata Al'adar in'ankai amarya yau washegari wuni sai ai liki dayamma, kowa Yakama gabansa.

Yautake lik'in kairiyya Wanda za'ayishi 4: 00 pm
Haka amarya kairiyya take zaune a'bangaran Fahad, itadak'awayenta da 'yan'uwanta, ankawomusu abin kari daga 'bangaran hajiya asma, daranama ankawomusu,

Sai yanzu misalin
3:00 pm Anti sauda tashigo tanawani d'ad'aga
hanci tatsayamusu k'erere aka tace" ita amaryar bazatabud'e fiskartabane, muganta, ai amarya mai tsada take rufe fiska bawananba mai araha....
Acikin cousin d'in kairiyya akwai Habiba dama ita batada hak'uri kokad'an kanamata zatarama. To yanzuma ita tadakatar da Anti sauda tace" dakata Anti karkiga kingirmemu kitinanin gayamana magana muk'aleki, Toni Habiba banacin bashin magana komin muninta saina rama
Ai " Anti amaryarmu itace maitsada domin kuwa tsadarta yagani shiyasa yace baison komai sai ita Dan itayakebuk'ata.
Bashirgiba kuma yasameta, d'anbak'in ciki sai yamutu. Anti sauda tace nikikegayama haka marar tarbiyar yarinya
Habiba tace" kekikanema kuma kinsamu
Kairiyya tace" dan Allah kuyi hak'uri

Anti sauda tai tsaki mmttss... dangin marasa tarbiya saiku shirya akwai lik'i
Anjima tai ficewarta, tanafita surahama sukayiwa kairiyya
Caaa akanme zatabada hak'uri aidatabari Habiba
Tagyaramata zama. Kairiyya tace" A'a bansan tashin hankali
Basira tace Allah yakyauta,

Anacikin haka Anti safna tazo takawowa kairiyya kayanta wa'yanda zatasa kafin anjima damangariba akawomata sauran
Nan suke sanarma Anti safna abindayafaru
Kuma suke sanarmata za'ailik'i anjima
Anti safna tace" kairiyya tatashi tak'ara wanka
Kairiyya tayiwanka Anti safna ita tazauna ta tsaramata kwaliyya light mecup tabata wani cot less mai matuk'ar kyau milk color akanad'amata head Golding sai hil shoe shima Golding da forse d'insa. Sai sark'arta 'yar k'arama ta gold
Wanda kakarta tawajan uwa tabata amatsayin gift sai veil akarufamata akai yarufemata fiska
Mai sharashara milk color
Tayi matuk'ar kyau, kamar kad'auketa kagudu🤪

🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯🔯

A'ban garan Ango shima shadda yasa milk color da agwada tasha aiki takalminsa,agogo
Hula, duk brown yasa sai baza k'amshi yake abokansa sukai filin lik'i dashi
domin kuwa 'yan uwa duk antaru nan akafarawa ango zuba kud'i kafin amarya tazo

*wai INA labarin wasila*

Wasilafa nacan abin duniya ya isheta itafa agaskiya tanason ya Fahad yanamatuk'ar burgeta dan action d'insa dakomainasa shine irin abin datakeso ajikin d'anamiji😳kuma
Gashi yanzu yai auransa yabarta
Danhaka takasa jurewa taje tasami mahaifiyarta tasa ta agaba tanakuka reras
Hajiya Ayiya tace"
Lafiya yauranar murna zakisani agabakinakuka.
Ni gun lik'i zantafi
Kifad'amin mekedaminki

Ni hajiya agunkune ranar murna amma Ni ranar bak'in cikine aguna🤔
Nadad'e inason ya Fahad duk nakiri samarina saboda shi shine yanzu zayi aure yabarni, zancan banza hajiya tace" shiyata'ba fadamiki yanasonki A'a wasila tace tokokinga saiki hak'ura tinda tinda bakifad'iba
Ashe baffa isa yanajinsu yace aidole tahak'ura tinda yasami k'aramar yarinya sa'ar su fadila ba'abin dazai da ita gashi matarsa
'Yargidan tarbiya
Yajuya yafice abinsa, sa'ar su fadila wasila tamaimaita.

Acancikin gida kuwa anatalik'i a ango akai sanarwar iyayen ango zasufito silik'i nan su nur sukaruga 'bangaran amarya sukace afitoda amarya filin lik'i.nan su Anti safna sukafito da kairiyya akai wajan lik'i a nazaunar da kairiyya kan kujera kusa da Fahad da yabaza babbar Riga shi ga ango hanun kairiyya yarik'o yadamk'e cikinasa yasunkuya kansa setin fiskarta yace my wafy wanan lallan yayi kyau yasumbaci hanun yanad'ago kai suka had'a ido
Da Anti sauda yakawar dakansa abinsa, nan iyaye sufito akafara lik'i nkud'i ana photuna 'yan uwa nataliki amma ba'yan uwan amarya

Anti safna tacewa Habiba wai ansanar da gidakuwa Habiba tace A'a nan Anti safna takira gida awaya tasanarmusu nan 'yan uwan baban kairiyya Dana mamanta sukazo suma sukafara 'barin naira kowane 'bangare sunyi bajinta

Anyi lik'i antashi anmai da amarya'bangaranta , 'yan biki kowa yawatse sai amarya da k'awayenta sunajira angwaye suzo ayi siyan baki

Ango yashigo da abokansa anyi siyan baki kowa yatafi abokan ango sunmai dakawayen amarya gida
Haka amarya da ango sukakwana
Ba abindayamata
Haka kairiyya take zaune a gidan batada damuwar komai
Ankawomata kayan anfaninta daga gidansu da kayan su cincin da alkaki.
Batama girki daga gun hajiya kulun shukura ke kawomusu, hajiya nfahd namatuk'ar k'aunar kairiyya
Kairiyya da Fahad kullum haka suke kwana baimata komai sai 'yan wasani hartsoyon
Sati biyu yanzuma shirin tafiya lagos sukeyi Wanda zasutafi jibi asabar, kuma Fahad yace mutum biyu zasi masu rakiya dan a jirgi za'atafi sai babbar k'awa rahama

**** ****** ******

Yau tasakasance kairiyya zasubar gari duk sunyi salama da dangi har damaturu sunje gidan imran

'Yantafiya suma sunshirya mama balki da bahba maryam dantace sai taje taga garin arna gakuma hawa jirgi aibaza'abarta abayaba.🤪bahba maryam d'in shagali kingama zagin tuzuru kuma gashi kinatijara akan zuwa gidansa😀

Sai kanwar kairiyya, shahida 'yarshekara 7 akabata. Haka imran ya 'yebesu zuwa iyaport din damaturu basudad'e dazuwa iyaport d'inba jirginsu yatashi sukatafi
Sukaba 'yan uwa dakewa.

To" saimuce su bahba maryam asauk'a lafiya😢

Plight dinsu yasauk'a garin Lagos 2:00 pm
Dasauk'arsu akaturo k'atuwar jeep daga office din su Fahad ta kwasesu tai cikin
Garin Lagos dash
Bahba maryam CE tafarawa Lagos k'irari " kaga cunkus d'akin tsuma sama ruwa k'asa ruwa, tsakiya gida makarinki sai ankoma😀
Sunatafiya k'abilu kalakala natawucewa da kayan dashi da babu duk kusan d'aya. Oh" Ni meramu gani agarin arna Allah
Yasawak'a karde aje ahaifamana jikoki arna Ni mero

Awata unguwa festac unguwar manyan mutane wane da wane nan akashiga dasu bahba maryam tace nan Americane ko Nigeria bawanda yakulata, awani bakin kofargida mai tsananin kyau of cheir anan mai motar yai hon maigadi yabud'e sukadana
Motarsu cikin gidan akai pakin sukafirfito
Suka shiga ciki gidan babban palone da d'akuna uku ak'asa sai kicin, da store kuma kowani d'aki da toilet aciki sai step dazakaho yanashinfid'e apalon ajikinsa duk tails dajikin dikka gidan d'akunan sama kuma biyune sai babban Palo da kicin da stor komai namore rayuwa akwai agidan, bahba maryam tace kud'in da babanki yabayar yace inkwai abin dabemikiba a sanjamiki ai saide akoma dasu dankomai akwai agidanankam
Mama balki tace A'a abatakud'inta
Tayiwasu abudasu

Kwanansu d'aya da zuwa abonkan aikin Fahad suka had'amusu partyn murnar aurensu
Inda kairiyya tasamu kyautuka

Kwanan su bahba maryam biyar suka koma potiskum inda sukakoma da abin arziki bahba maryam sai cewa take Lagos bak'arya tayi wallahi dan harwani haske tak'ara ga aljihunta cike yake dakud'i banda sutiru da Fahad yasiyamusu kairiyya ma tabasu, dan haka dukwanda yazomata sannu dazuwa sai tace Lagos ba k'arya
Kudin da abban kairiyya yabada akan acanjamata abin da baimataba ta bawa mama balki
Tace tabawa mamanta da Antinta suraba

Yaude anatashek'aruwa a Lagos tunsafe haryanzu dare ruwanan baitsayaba
Fahad ne yadawo dagagun aiki kairiyya takaishi sama yai wanka
Yaci abinci sukad'antaba hira
Yace takai shahida d'akinta tasameshi anashi d'akin taje tadawo yace kina
da alwala tace eh yanzu nai wanka nad'aura awalar kwanciya yace OK
To misala raka'a biyu sunyi salla
Fahad yamusu addu'a maitsayi suka shafa yad'auki abarsa sukai gado kairiyya gabanta yafara faduwa saboda wasanin dataji yanamata
Yace dakata madam yau aurenmu sati uku
Ainayi k'ok'ari
Adaranan Fahad yafanshe sadakinsa
Sai da akayi kwana biyu anaruwa batsayawa Fahad nagida nacin amarci

Satin Fahad daya nacin amarci sanan yakoma bakin aiki
Yanemi makaranta shek Abubakar Gumi yasa kairiyya dan takarasa karatunta
Shahidama nazuwa school da islamiya

Bayan shekara bakwai

Su kairiyya ne da Fahad da shahida
Sai yara biyu namiji da mace sukafito da ga jirgi imran da iyalansa sukadaukosu daga iyaport zuwa gidansu sukaci abinci suka huta sukakama hanyar
Potiskum kai tsaye gidansu Fahad sukawuce
Inda sunashiga yaran suka ruga
Palon hajiya suka k'ank'ameta suna hajiyarmu hajiyarmu
Suna haka iyayen sukashigo kairiyya tace kai kucikata maza munason harjirmu karkujimata rauni
Hajiya tace k'yalesu yarane ai
Babban d'an musa mai sunan bahban Fahad sunakiransa Abul kairi sai macan mai sunan antinmu nafisa sunakiranta intisar, kairiyya tazama babbar mace inkaganta kasan Hutu yazauna, shima haka Fahad din
Yaginamusu tafatsetsen gida Wanda insunzo nan suke sauk'a

Kausar tayi aure ta auri ya usman da 'yarsu daya kairiyya
Rahamako k'awar
Kairiyya ta auri ya Ibrahim zumunci sai abin dayai gaba wasila ma tagaji tayi aure ta auri wani babban mutum akano da matarsa daya ahto dan kairiyya takafe ta tsare bawata gun Fahad sai ita

Yanzuma shirye shiryen sauran su nur da shukura akeyi,yau kairiyya tashirya yaranta danzasu ziyara gudayawa kafin sukoma Lagos
Gidan bahba maryam sukafara zuwa sukagaisa a kakawomusu abinci tuwan shinkafa miyar taushe amma sai yaran sukayiwa mominsu magana da English waisu basaci itakuma uwar taimusu magana da larabci sukabata hak'uri sukasa hannu sukaci tuwon anakiran salla abulkairi mai shekara shida yace mommy zani masalacin kofar gida nai sallah
Intisar kuma mai shekara hudu ta dauro Alwala ta tada sallah
Bahba maryam tadubi kairiyya tace takwara yaranki nabirgeni
Gaturanci ga larabci ga ibada. Gatarbiya maikyau dakikabasu
Kairiyya tace" ai bahba karatunan dacan badayabane
Can sunfikaratu maikyau Ni wallahi dankaratun yaranan zankoma
Dan inaso inzauna cikin 'yan uwana. Bahba maryam tace kamar wanicikine
Dake kairiyya taduk'ar dakai tace eh bahba

To " Allah yaraba lafiya musha shagali💃💃💃

Anan nakawo k'arshen littafin
Auren Lagos
Wanda naidede Allah yahad'amu aladan Wanda naikuskure Allah yayafemin🤲

Please read& shere⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀

Sai munhad'u asabon book inmai dukka yaso

Allah yajikan iyayenmu🤲
Chapter 9 · 0% Book details