← Book details Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki yacika aneesah sosai, tarike kugu tana kallon afham "hmm yaya afham zuciyarka bata baka shawarar kwaraiba, domin tanema maka saukankiyar hanya wadda zata saka mahalincinka (Allah) Fushi dakai, domin yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye, yaya afham kayi gaggawar chanza wannan gurguwar shawarar taka, mezaka cewa Allah yanzu idan katafi kaddara takiraka kasamu matsala atafiyarka, zakacene kayi fushi da iyayenka shine kabar musu gida, mafi aka sarin irin wannan tafiyar bata zama alkhairi, yaya afham karkaje, kazauna cikin ahalinka shine mafi alkhairi agareka "

edon afham yayi jajir cike da masifa yace "yakikeson nayi kenan natsaya a auramun wacca bana so, nifa kwata2 bana son amal, wlh matukar ba'a rabani da amal ba to wallahi zanbar gidan nan"

Aneesah tayi ajiyar zuciyar, tana mamakin irin zuciyar afham shi baya daukar nasiha, a duk lokacin da kake masa nasiha shi a lokacin yake kara zafi,

Aneesah tasaukar da murya tace " Bana son katafi, kazauna ni zanyi abba da momy magana, zan fahimtar dasu cewa bakason amal, kuma insha Allah zasu saurareni, kabani nan da kwana biyar"

Afham yaja numfashi sannan ya ajiye akwatin akan gado yace "kwanar biyar kikace, nabaki, amma kisani cewa matukar ya wuce kwana biyar to tabbas zanbar gidan nan" yana karasa maganar yanufi hanyar bandaki,

Aneesah tana murmushi, takarasa kusa ga akwatin, tadauketa takaita cikin drowar tasaka, koda tajuyo yashige bandaki,

Kida kai tayi tana murmushi tabar dakin...
*** ***
Bayan hilal yabar daki ameelah cike da zafin zuciya, airtel office yakoma, koda yaje sunkarasa komai, an rubuta duk wani detail akan number, yakarba yafara karantawa, mai number bama gari daya sukeba, nisa yake dasu sosai,

Hilal yaja tsaki jiyakeyi kamar ya yaga pepar, miyakai ameelah waya da maza, meya rageta dashi meye baya mata, duk zuciyarsa yake yiwa wannan tambayoyin, saidai kuma ba amsa,

Cen kuma wata zuciya tafara kawo masa wasu wasi,
Ayya kuwa ameelah zata iya masa haka, tunawa yayi da irin soyayyar da sukayi abaya kafin aure,...

Na:- ?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[1:17PM, 4/24/2016] ????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??55and56??

Auren soyayya sukayi, baya tunanin ameelah zata iya cin amanarsa, (hmm baisan kuwa tagama ba )... cikin motarsa yakoma, yadafe kansa, yana tunin irin fadan da yayiwa ameelah, sai yaji duk tausayinta yakamashi,

Yafi kusan minti goma cikin motar yana tunani duk jikinsa yayi sanyi,

Sannan yakunna motar yadawo gida domin jiyakeyi kansa namasa ciwo, dakinsa ya wuce baiko gayawa ameelah yadawoba,

Gado yasamu yayi kwanciyarsa,
*** ***

Sai bayan la'asar lis ameelah tafarka, jikinta duk yayi tsami saboda dukan datasha,

A kasale tatashi tanufi bandaki, tahada ruwan zafi tayi wanka,
Jikinta yadan saki, tarage jin zafin bulalar, bata fito daga toilet dinba saida tayi alwala,

Tana fitowa tayi sallah azahar da la'asar, domin bacci tayi bata samu damar yin sallar azahar ba,
(Wa'iya zu billah, yan uwa mudaina wasa da sallah, sallah itace hisabinmu nafarko a ranar gobe kiyama, Dan Allah yan uwa mukiyaye)

Bayan ameelah tagama sallah, tatashi ta nade sallaya, ta ajiyeta saman gado sannan tanufi gurin mek up dinta,
Motsi taji a falo, murmushi tayi domin tasan bakowa bane sai hilal, fushi yake da ita shine bai shigo dakintaba,

Kwalliya ta chaba, wacca bata taba yiwa hilal irintaba,

Bayan tagama ta kalli kanta ta mirror taga tayi kyau tai murmushi sannan tatashi, tanufi gurin shirinta,

Wasu kananu kaya naga tadauko, tana kokarin sakawa, ( nan mukabar dakin muka fito waje, bayan minti biyar na leka dakin, ido na kafawa ameelah, wani irin kyau datayi)

A hankali ameelah tafara zagaya dakin, kamar mai kowon tafiya,
Tabbas tasan kwalliyar datayi danta janyo ra'ayin hilal ne zuwa gareta,

Cike da kinsa da karairaya tafito waje,

A falo tasami hilal yana kallon wani indian fim, RAJKUMAR...

Tundaga nesa hilal yaji kamshin turarenta, ya juyo suka hada ido, yagagara dauke idonsa,

??NOTE??
Muna bawa Masoyan littafinnan namu AMANAR AURE, haquri zaku d'an jimu shru na kwana biyu! Da kuma masoyan HAFSATUL KIRAM, kuyimin uzuri insha Allah dana dawo zan qarasa muku! Muna godia da 'Kaunar littafanmu da kuke!??????

Na:- ?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [5/2, 8:57 AM]????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??63and64??

Momy tana zaune harya karasa sallarsa, sai da yagama adu a sannan tatashi tafita,
*** *** ***

Hilal kuwa sai bayan magriba yadawo, yayi parking na motarsa sannan yakaraso ciki falon, sallama yayita rabkawa shiru, babu amsa,

A zuciyarsa yace kodai wannan bacci take,

Dakin ameelah yanufa ya tura kofar yashiga, a kwance yasameta kasa tana kakin yawo masu kumfa,

Tadafe cikinta, tana kugi, a firgice yakarasa gurinta ya daga kanta cike da firgita yadaga murya sosai "ameelah meya faru dake, meya sameki"
Ameelah takasa magana, edanu take fitarwa bul2,

Hilal ya tsorata sosai, a gigice yadauketa yaje yasaka ta a mota ya nufi asibiti cikin gudun bala i,

Yana karasa asibin aka karbeta aka bata taimakon gaggawa,

Kusan awa Daya ameelah bata farkaba,
Hilal duk ya tsorata, yaso yakira iyayenta amma yafasa,... Yana xaune Likita yafito a firgice bai tsaya gurin sa ba yawuce office dinsa,

Hilal yatashi yabi bayanshi,

Dashigar likitan cikin office din ya dukufa gurin neman wani abu,

hilal yashigo office din, a tsorace yace "likita meya faru da matata"

likitan yadaga kai ya kallesa sai kuma ya basar yaci gaba da dubin takar dunsa, hilal yakara tambaya, sannan likitan yace " ba matarka bace a gabana yanzu, domin matarka farkawarta kawai muke jira, guba taci abinci kuma mun magance matsalar domin gubar bamai yawa bace, kuma bamai saurin illatawa bace, amma dai kukiyeye gaba,"

hilal yayi ajiyar zuciya yace "to shikenan Allah ya farkar da ita"

likitan yace amen, bai kara cewa komaiba yafita yabar office din, likitan yaci gaba da neman takardunsa,

Wata takarda yagani acikin wani file, daukota yayi, sannan yaduba yayi ajiyar zuciya, yafita,

Sai bayan isha ameelah tafarka, likita yayiwa hilal izini akan yashigo yaga matarsa,
Hilal yashiga yazauna gefen gadon da ameelah take kwance ya kalleta ta sunkuyar dakai yace "waya baki guba abinci"
Kanta a sunkuye tace "nima bansaniba"
Hilal yayi ajiyar zuciya yace "meyasa baki kiraniba lokacin da kika fara jin abin acikin ki, yanzu da Allah baisa nazo bafa yazakiyi kinga sai kawai nazo natarar da gawarki"
Ameelah tadaga kai ta kallesa cike da mamaki tace "dame zankiraka ai kasan banada waya"

Hilal yaja nunfashi "sorry kinga harnama manta, yayi shiru kamar yana nazarin wani abu, sai cen yace "to shikenan zansan mezanyi akai, yatashi yana kallonta "yanzu kijirani nakarbo takardar sallama saimu koma gida"
Ameelah ta girgiza masa kai yafita...

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[5/2, 9:00 AM]????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??65and66??

Takardar sallama yakarbo yadawo suka wuce gida,

Har suka dawo gida iyayen ameelah basu san da zancen ba,

Da isarsu gidan yawuce dakinsa, ameelah ma haka dakinta ta wuce taje tasame gado tayi kwanciyarta
*** *** ***
Acikin daren afham yahada kayansa saida ya kintaci su momy sunyi bacci sannan yafito,
Tafiya yakeyi cikin sanda, harya karsa bakin kofa fita, ya bude yafita,
Motarshi yashiga, ya kunna, a lokacin mai gadi yatashi, yabude masa kofar get babba yafita,

Yakama hanyar gombe zuwa ganin ameelah ( kujimun wauta, Allah yakaremu da shairin zuciya)

Tafiya yaketa tsala sai kusashen asuba yakarasa gombe,

Wata babbar Hotel yakama yaje ya ajiye kayansa, wayarsa yadauko yayi off dinta yacire sim dinsa yadauko wani sabon sim yasaka, sannan ya kunna wayar, a cikin sabon sim din number ameelah ce kadai a ciki, kiran number yayi yajita akashe kamar yadda yasaba ji a yan kwanakinnan,

Zauna yayi a bakin gado cike da damuwa, sannan yayi ajiyar zuciya, ya wullar da wayar saman gado yatashi yanufi ban daki yayi wanka, bayan yafito yadawo ya kwanta,

Washe gari

Sai misalin 9 nasafe yatashi, a lokacin yayi sallah,
Sannan ma ai katan hotel din suka kawo masa kayan karin safe,
*** *** ***

Acen kuwa gidan su afham, momy tagama hada kayan kari, aneesah tafito tace "momy ina yaya afham duk yau bangan saba"

Momy tace "kinsan inda yake kije kisamesa "

Aneesah ta zunbure baki, ta nufi dakin afham,
Tunda ta tura kofar dakin takejin gabanta nafaduwa, a hankali takada kafarta cikin dakin, tayi sallama shiru,

Wata yar gajeruwar takarda tagani a gefen gadon sa, takarasa bakin gadon tadauko tana dubawa, karantawa takeyi a hankali, tun kafin takarasa karanta takarda hawaye suka fara zubo mata,
Juyo tayi da gudu tafita tana kiran momy,

Tana isah falo taci karo da momy da abba zaune akan danni, takarasa tana kuka tace "momy yaya afham yagudu" a gigice momy tace "innalillahi wa inna ilaihin raju un"

Abba dayake zaune agefe yakarbi takardar datake hannun aneesah, yafara karantawa, a karshen takardar aka rubuta " niban bazan iya auren amal ba natafi gurin wadda nakeso" edon abba sunyi jajir, ya dago kansa yakalli aneesah yace " wacece yakeso"

Aneesah tana kuka tace "wata yar gombe ce a chart suka hadu"

Abba ya girgiza kansan cike da takaici yace " lallai yaron nan zai hadu da fushina, wlh duniya kadai zai bari nafasa auren dazan masa shida amal, dole sai anyi wannan auren ko baya garin nan"

momy tace "aa alhaj..."

Abba yadaga mata hannu " karkice komai hajiya, wannan shine hukuncina" yana gama maganar yatashi yabar gurin , aneesah kuka take sosai momy tana lallashinta,
*** *** ****
A gidan ameelah kuwa, tunda safe hilal yafita bayan yakarya,
Ameelah takasa samun sukuni domin tunda tatashi daga bacci takejin gabanta nafaduwa, tarasa meye dalili...

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[7:10PM, 5/23/2016] Mr, Smiles??: [11:16PM, 5/4/2016] Mr, Smiles??: [11:06PM, 5/4/2016]
????Amanar aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??67 and 68??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Ana gama azahar hilal yadawo gida, rike da jakar aikinsa a hannunsa,

Dakin ameelah yakarasa yasameta tana bacci, yaja tsaki a zuci yace "yanzu haka batayi sallar azahar ba"

Afili kuwa sunanta yafara kira yana dukan kafarta,

A hankali tafarka sukayi ido hudu ciki muryar bacci tace "harka dawo "

Hilal ya tsuke fuska yace " eh nadawo, kinyi sallar azahar"

Ameelah tadafe kai "au har lokaci yayi ne"

hilal yace "aa ki kwanta lokaci yajiraki"

Tagane bakar maganar yamata hakan yasa tayi murmushi tatashi tanufi bandaki tayi alwala,

Hilal yana tsaye tafito, saiya tashi yace "idan kingama sallar kisameni a daki"

Ameelah tace "toh"
Chapter 9 · 0% Book details