← Book details Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu bello yace "a a yaya karka yiwa yaron nan abinda bayaso, yanzu dai abarshi yaje yayi shawara, kawu bello yajuya gurin afham yace " tashi kaje kayi shawara zamu nemeka" Afham yatashi ransa abace, shiba macceba amma ace za'ai masa auren dole, shifa baya son Amal dinnan,
Haka dai yashiga dakinsa zuciyarsa cike da wasi2 kala2,
Ya zauna gefen gado yayi jim yana tunanin wani abu saikuma yatashi yafito, yanufi dakin kanwarsa ANISA wadda akoda yaushe itace abokiyar shawararsa,

Akwance yasameta saman gado, Tana dannar waya, yayi sallama sannan yashigo dakin,

Dago kanta tayi tana murmushi ta amsa masa sannan yanemi gure a gefen gado yazauna yadan saka murmushi " chart kike koh, bakida aiki sai chart,.sai ciwon chart yakamaki"

Anisa tayi dariya sosai "la yaya harda wani ciwon chart akwai ne"

Afham yace "sosai ma idan mutum ya nace akan chart to chart zaibi jikinsa mutukar baiyi saba to bazaiji dadi ba"

Anisa tace "toh wannan likitancin kane yaya, anisa tatashi zaune tace "ai nama gama chart din daman wata sabuwar kawace nasamu wallahi yaya karka ganta ta hadu kamar ita tayi kanta,

Anisa tashiga gallery cikin Whtsapp prfil pc takai ga photon ameela tatsaya "kaganta yaya, sunanta ameela, kamar baindiya" tamikawa afham wayar, yakarba, dam yaji gabansa yafadi a lokacin dayayi tozali da kyankywar fuska ameela, sak irin yadda yake neman macce dakyau da diri da kuma kyakkawar surar jiki,
Anisa tana gefe tana dariya ganin yadda afham yakurawa photon ido,
Kamar daga sama taji muryar ummanta tana kiranta, dasauri anisa ta karasa bakin gado tasaka takalminta, tayiwa afham alama da hannu "ina zuwa yaya,.bari nazo musa labule idan yarinyar taimaka," takarasa maganar cike da zolaya dakuma dariya,

Afham gabaki daya pic din yatafi da imaninsa, lumshe ido yayi sannan yasake budewa, tabbas yasamu irin maccen daya jima yana nema, wadda tajima tana zomasa a mafarki,

baimasan da fitar anisa ba yajuyo yayi yana waige waige ganin bata cikin dakin yasa yayi saurin fitowa da wayarsa yashiga xender yatura pic din, sannan yashiga Whtsapp yaga number da aka rubutawa ameela, da sauri yadauki number yayi save a wayarsa ya ruba mata ZABINA,
Sannan yajiyewa anisa wayarta a kan gado yafita yakoma dakinsa,
Akan kado yakwanta yakamo pic din ameela yana kallo yana maimaita sunan a bakinsa, yaa lumshe ido sunan da surar jikinta duk sun masa, tabbas ya yayi gamu da katar kuma yanzunne zai samu damar tunkarar su kawu bello da abbansa yafada musu cewa yasamu wadda yakeso, matukar wadda yake gani a pic dinnan ta aminta dashi, duk azuci yake fadan wadan nan maganganun, a fili kuwa tambayar kansa yake, to ta ina zaifara....

Hmm akwai chakwakiya kenan.. muje zuwa

Na:- ?Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles??: [9:14AM, 4/2/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??23 and 24??

A hankali take typing, ba 'ason rantaba harta karasa rubuta masa" ina son sosae, har cikin zuciyata"

Hmm Yace "Amma naji dadi sosae Ameelanah??"

Suna cikin fira Afham yahau, yaga taga text dinshi harta karanta amma babu amsa,
gabanshi ya fadi a ranshi Yace "Ya Allah ka taimakeni akan soyayyatah! Ganinta online yasa ya shiga rubuta mata wani text din..

Afham "Sunana Afham, ina zaune a garin gombe, na ansa numbrki ne a wurin qanwatah Aneesha, Ameelah kinyi matuqar burgeni ne, saboda irin kyaun da Allah yamiki, lokaci daya naji zuciyatah ta kamu da sonki, ina fatan babu wanda ya rigani!"

Ameelah ta jima tana tunani akan text din kafin ta bashi amsa, kalamansa masu dadi sun ratsa zuciyarta,

Ameelah "gsky ngde sosae??"

Afham Yace "hka kawai zakice, kinko san yadda zuciyata ta kamu da sonki, dan Allah kibani cikankiyar amsa wadda zata gamsar da zuciyata"

Ameelah taja nunfashi tana nazarin kalamansa masu sanya zuciya shaukin so da kauna, sannan tayi murmushi,

Ameelah "??hmm tohm mezance??

Afham yace "inaso ne ki bani amsa, wlhy Ameelah daga jiya zuwa yanzu zuciyatah qara cika take da zazzafar qaunarki, idanuwana basa muradin kallon komai bayan kyankyawar fuskarki, ki aminta dani namiki Alkawarin bazan barkiba"

Murmushi take tana kara maimaita kalaman a kwakwalwarta, kanta yadau zafi, tana zaune ta kurawa text din ido,
TaRasa abinyi gashi bangare guda HMM text dinshi sai shigowa suke shima da irin nashi rigimar, ga messages na Facebook sai shigowa suke,
rufe datar kawai tayi ta zauna ta dafe kai tana tunanin Afham,
( Ameelah tabani tausayi, irin zaman danaga tayi saikace shege agurin rabon gado, saikuma wata zuciyar tace meye abin tausayi a tattare da wannan bayan nema take taci AMANAR AURE, ai Allah bazai taba barinta tasamu kwanciyar hankali ba)
*** ***
Batasan iyakar mintocin data bata tana tunani ba sai dai qarar wayarta ne daya katseta, number Aneesah ne da tayi saving da 'qawah' sai data kusan katsewa kafin ta dauka ta sanya a kunne cikin rashin kuzari.

Tun kafin tayi magana Aneesah cikin barkwanci ta fara cewa "haba qawah, gsky banji dadiba yanda kika saka yayanah cikin damuwah, Allah yana sonki da yawah ba yabon kai ba yen mata da yawa na sonshi amma ban taba ganin wadda yakeso kamanki ba! Don Allah ki amince mishi, kinji qawata"

Ajiyar zuciyah Ameelah tayi kafin tace "bazaki gane bane qawah matsalan kawai itace inada...."
katseta Aneesah tayi dacewa "kina dame nidai karkicemun kinada saurayi, kuma basaina gane ba kawai ki fitar da yayana dga cikin damuwah, kinga yadda yashigo dakina kuwa, a gigice wai ameelah taki aminta dashi"

Murmushi ameelah tayi sannan tace "shikanan zamuyi magana dashi anjima"

Dariyar jin dadi Aneesah tayi kafin tace "ngde sosae qawah bari na mishi Albishir"

Ameelah tayi saurin cewa "kenifa bacewa nayi na amint.... kafin Ameelah tayi magana aneesah ta kashe wayan, Shirun da ameela taji yasa tarinka fadan Hello, hello, a lokacin tafahimci cewa takashe wayar, tayi ajiyar zuciya, zuciyarta cike da tunani kala kala..

Na:-? Rabiatu sk msh da Mr, Smiles??
[9:14AM, 4/2/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??25 and 26??

Ameelah ta dafe kanta kafin ta yarfar da hannu tace "tohm miye ma A cikin Soyayyar? Soyayyah ne pa kawai shi da yake gombe ma ina xai ganni?" A zuci tayi maganar sannan ta buda datar ta taci gaba da charting dinta, amma a lokacin afham baya online, batama shiga Whtsapp ba Facebook tashiga tayi chart da dan fim..

Akayi sallar laasar duk tana zaune, charting yahau kanta,
(Wa'iyazubillah, wannan jarabar chart da masifa take, yanzu Ameelah ko tunanin mutuwa batayi, hmm Allah yakara karemu da kariyarsa, wai kaga mutum ana sallah shiyana zaune yana charting, wai bayason sauka, to idan baisauka anan duniyaba ai ya sauka kiyoma, Allah ya kyauta)
*** ***
Har lokacin dawowar hilal yayi babu Abinda tayi tana kwance falo saman kujera ya shigo da sallamarshi da sauri ta ajiye wayar tana kallonshi kamar marar gaskiya sannan ta mishi sannu da zuwa..

Ya amsa a gajiye, ganin yanayinta yasa baikara maganaba ya shige dakinsa, dasauri ta janyo wayarta ta rufe data, tayi ajiyar zuciya, tana zaune ya fito ya zauna saman kujera ya kishingida, Yace "wlhy yau na gaji da yawa, ga yunwa da nakeji"

Ameela ta dubesa tayi murmushi Tace "ayyah sannu"

Hilal yace "sannu bazata gamsar da yunwar danakejiba ki daukomin Abncinah inci"

cike da mamaki ameelah Tace "Yau kuma?

Hilal Yace "ban gane yau kuma ba?

Ameela takara yin murmushi Tace "naga ko breakfast baka tambayana ne, Yau kuma harda tambyar Abncin rana ko ka manta satin daya daka bani, baifa cikaba saura kwana biyu??

Girgiza kanshi yayi cikin takaici yaja tsaki, sannan ya daure ya danne damuwarshi ya tashi tsaye ya koma daki, ciki minti biyar ya fito ya canja shiga da mukullin motah a hannunshi, Yanufi kofar fita, tana zaune tana kallonsa,

Har yakai bakin kofa bai ce matah komi ba,
sai itace tace "ina kuma zakaje?

Hilal Yace "zan fita ne inciyo abincin waje, tunda nayi aurenma bazan huta ba"

Muryarta a shagwabe kamar zatayi kukah tace "ayni daman baka damu da cin abincinah ba"

murmushi hilal yayi yace "hmm ki fadi Abnda kike bukatah zan zo miki dashi, domin nasan kema yunwar kikeji"

Mikewah tayi tsaye sannan tace "ni sai dai ka tafi dani"

cikin mamaki yake kallonta kafin yace "ina zakije ko sati bakiyi da aure ba? Ina zanbarki ki fita wani ya kallemunke, Kiyi zamanki ki huta, kinji"

sororo tayi a tsaye don tasan maganace ya gaya matah, tana tsaye har yayi ficewarshi.

Ta tabe baki ta zauna taci gaba da chating dinta, kusan minti biyar tana jiran Afham har a lokacin bai hau ba, ta kagara suyi chart, ta rufe datar domin duk taji chart din ba dadi, ta ajiye wayar akan kujera, "Allah tadani naje nayi sallah" tafada sannan tatshi tanufi dakinta tashiga bandaki, tayi alwala sannan tafito tafara sallah, tayi raka'a biyu, tana cikin tahiya, taji karar wayarta a falo, a dai dai lokacin Hilal yashigo falo, da ledojin abinci a hannunsa, Ya dallawa Ameelah kira, saida ta zabura duk da sallah take, gabanta yayi mummunan faduwa,
Yau kam asirina ya tonu" tafada a zuci...

Na:-? Rabiatu sk msh da Mr, Smiles??
[7:06PM, 5/23/2016] Mr, Smiles??: [8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [6:16PM, 4/2/2016]
???? Amanar Aure ????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??27 and 28??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Jitayi anturo kofar dakin da karfi, duk inda ilahirin jikinta yake yadau rawa, tayi matukar tsorata,
Hilal yashigo yatsaya yana kallonta tana sallah, ya girgiza kai ransa a bace yaja tsaki yafita ya koma falo,

Jitakeyi kamar takarawa sallar gudu, shaf2 ta gama sallar ko adu'a bata tsaya yiba tafito falo a gigice,
Wayarta tagani a hannun hilal, ta zare ido ta zabura kamar anmata sock, tayi matukar razana, taku takeyi cikin sanda ta sunkuyar da kanta kasa,
Jin tafiyarta yasa hilal yajuyo sukayi ido hudu taga yanayinsa ya chanza, ta tsaya cak guri daya tana jiran taji mezaice
A zuci take fadan nashiga ukku yau ruwa yakarewa dan kada"
Ameela ! Hilal ya kirata,
Cike da fargaba murya na rawa ta amsa,

hilal yace "karaso nan" ya nuna mata kujera da hannunsa,
Kafafuwanta har wani rawa suke dakyar takarasa bakin kujera tazauna, ta sunkuyar da kai tana wasa da dan yatsan, gabanta naduka shida shida,
Chapter 4 · 0% Book details