← Book details Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nishadi take replyn har tazo kan numbrr Afham, tsayawa tayi saboda number tayi matuqar burgeta so speacil, shiga tayi ta duba text din kamar haka "Assalamu Alaiki, Sunana Afham! Ina fatan zan iya kasancewa Abokin firanki"

Murmushi tayi a ranta tace "sunan nashi ma mai dadi, ko ya kamanninshi zasu kasance?? Tunanin Amsar da xata bashi ta tsayayi, data rasa me zata ce mishi ta wuce kawai,

Taci gaba da duba text dinta, har a lokacin "Hmm" yana online, text dinsa nakarshe ta karanta kamar haka "beauty idan ina chart dake jinake gabaki daya natsuwata tadawo gareki"
Kalaman sun matukar mata dadi murmushi tayi wadda yakara bayya kyaunta sannan tafara typing

Ameela "??hmm nima hakan nakeji aduk lokacin da muke chart, hakan yasa a duk lokacin da zamuyi chart sainaje nayi wanka na chaba ado kafin mufara"

Hmm "??beauty kenan najidadi sosai, gaskiya inason naga irin kalliyar da kikayiwa wannan chart namu"

Ameela " To shikenan,
Daidaita zamanta tayi sanan ta kunna camera, ta dauki wani kyankyawan selfie tatura masa,
Photon yanuna alamar yashiga

Hmm "?? wow kinyi kyau sosai, Allah ya mallakamin ke a matsayin matana,
Gaban ameela yafadi ta tsaya tana karewa text din kallo, tana tunanin wace amsa zata bashi,
Nan taji dinn, karar text yakara shigowa, text dinshine kamar haka

Hmm "Naji kinyi shiru bakice ameen ba kobakya sonane"
Ameela tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tana tunani mezata rubuta masa...

Na:-?Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles??: [9:28AM, 3/27/2016]
???? Amanar Aure ????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??13 and 14??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Sai 12pm na rana amrah tabar gidan, haka baki suka dinga zuwan gidan zuwa ganin amarya,

Ameela tarika tarbar bakin hannu bibbiyu,

Misalin karfe biyu narana bayan ameela tagama sallar azahar sannan tadaura indomi guda biyu, bada jimawaba tadafe indomi kan danni table ta daura indomi ta cinyeta tas sanna tatashi tashiga bandaki tayi wanka, tafito tasake sabon shiri, cikin atamfa dunkin yasha aiki, kuma yakama jikinta sosai tayi kyau abinta,

Kangado ta kwanta ta janyo wayarta ta kunna DATA tana jiran shigowar messages,

Cikin seconds messages suka fara shigowa,
Bayan sun gama shigowa ameela tadanna hannunta akan Facebook,
Text tafara gani na wani frd dinta wadda yace mata shi dan fim ne kuma yana online, da sauri tashiga wurinsa bayan tagama karanta text dinda yayi mata, wadda yayi mata jiya dadare bata gansaba wayarta tadauke,

Ameela "barka da warka"

Dan fim "barka dai mai kyau meyasa jiya muna cikin chart kika fita, kina fita sainaji duk chart din badadi, gaskiya nayi miss dinki beauty"

Ameela taja nunfashi tana kallon text dinsa kafin tace "hmm sory wlh wayatace tadauke, yau baku aikine, naganka online, da rana"

Dan fim "hmm muna aiki mana yanzu haka ina gurin shooting wani fim ALLURA DA ZARE, muna tare da rahama sadau da Adam zango"

Ameela ta dafe baki cike da jindadi tana masifar son rahama sadau saboda yadda take rawa, tana burgeta,

Ameeela "woow my rahama tana tare daku yanzu, wayyo jinake kamar nabiyo iska nazo naganta, dan Allah kace mata fan dinta tana gaidata"

Dan fim "hmm zataji, karki damu mai kyau aike tamusamman ce agurina, dama ace zakiyi fim, dasai kinfi rahama fans"

Ameela "hmm inada sha'awar yin fim"

Dan fim "ayya to kizo ai zaki samu shiga indai kinaxa kyau, da ilimi, kuma ina tare dake zanmiki hanya,
Baijira tayi reapply ba yasake turamata
"Sorry director yakirani, yanzu zamu koma aiki, muhadu 12:00am zamuyi magana sai anjima beauty"

Ameela "to shikenan saimun hadu" tafito daga cikin username dinsa sannan tashiga duba notification dinta da kuma frd reqst da aka turo mata kuma duk tayi accept duka mazane babu macce ko daya, a kalla kullum zata samu frd reqst kusan mutum ashirin kuma duk maza,
Hakadai takare da Facebook, sannan tafito tashiga Whtsapp,
Badama tafara duba texts dinta bakuwar numbers tagani har guda ukku, sai sauran messages na grp dakuma kawayenta da samarinta,
Bakuwar number tafarko tafara budewa sakone kamar haka "aslm, sunana ANISA daga gombe gaskiya pic dinnan dakika saka yamun kyau shine naji ina son kizamo kawata daga Sun shine grp"

Ameela tayi murmushi kafin tafara typing na reapply, "wslm, sannunki da zuwa kuma nagode, nikuma sunana Ameela"
Bayan tagama typing din tatura mata sannan tafito tashiga bakuwar number tabiyu, sallamace kawai akayi mata tayi reapply sannan tafito ta duba ta ukkun, sakone kamar haka "wow kyankyawan surar jiki kamar na bata, ga manyan boobs, gaskiya ta ko ina kin hadu"
Tsaki taja tafara typing "kai malam dakata nifa matar aurece"
Ta sender masa daidai dayana online,
Alamu tagani na tabbas yagani kuma yakaranta, a saman number aka rubuta is typing,
Ta mannawa number ido tana jiran zuwan sakon, bada nimawaba sakon yashigo ta danna cikin number tafara karantawa "?? wai matar aure, to ainima namijin aure ne, to koma daike mecece, nidai nagani inaso kuma, ina fatan zan more dake, sunana kamal"

Ameela jitayi kamar tayi block dinsa saikuma tafasa

Ameela "kafita harkata nagaya maka nifa matar aurece, kuma ni bayar iska bace"

Kamal "hmm kwantar da hankalinki yan mata nifa ba tabaki zanyiba kawai dai zamuna rikayin sex chart dakuma send pic din .... Kidai gane, gaskiya kinada kyau sosai domin ni harna sace pic dinki a dp dinki yanzu haka shinake kallo inasamun natsuwa"

Ameela cike dajin haushinsa tarubuta masa "dan banza, marar aikinyi tare tsaki sanann tayi block dinsa,
Sannan tafito taci gaba da sauran text dinta,
(Nace yayi kyau Yau Ameela ta hadu da gamonta, irin mazan nan masu lalata sakankun mata a chart, Allah ya shirya mu" ameen

Na:- ?Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[9:43AM, 3/27/2016]
???? Amanar Aure ????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??15 and 16??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Number data rubutawa HMM taduba baya online amma yabar mata sakon cewa yau su hadu karfe shabiyun dare, akwai magana, kuma yaga pic yagode"

Tagyara kwanciya tayi, tai ajiyar zuciya sannan taci gaba da chart dinta,
Tajima tanayi da samarinta, dakuma kawayenta,
Sannan taji ankira sallar la'asar, amma taki ajiye wayar haka taci gaba da chart har aka tayar da salla, aka gama kamar ba a kunnen akayiba, ko motsawa batayiba, balle tasa niyar tashi tayi sallah,

Saida tagaji sannan tatashi ta ajiye wayar akan gado tanufi bandaki tayi alwala, tun acikin bandaki takejin karar wayarta, amma taki fitowa saida tagama alwala sannan tafito,
Tataras anmata, 3miss call,

Zare ido tayi alokacin data duba number babu shakka number guy din nan ce wadda yayi mata maganar banza a Whtsapp chart tayi block dinsa, dafe baki tayi tana mamaki tace "nashiga ukku"

Dasauri tashiga blacklist tasaka number shi sanann tajiye wayar tajanyo sallaya tafara sallah,
Bayan tagama sallah, tadanyi adu oi sannan takara janyo wayarta tana kallon pic dinda sukayi dazu ita da kawarta amrah,

A hakali taji anturo kofar dakin anshigo,
Hilal ne rike da jakar aiki a hannunsa alamar gajiya ta bayya a fuskarsa karara, tashi tayi, tai masa sannu dazuwa, sannan takarbi jakarsa, cike dajindadi,
Hilal yakarasa bakin gado yazauna, bayan takai jakar a mazauninta,
Ameela tazo tazauna kusa dashi tana murmushi "Dee mezakayi wanka, ko bacci ka huta domin naga alamar kagaji."

Hilal yajuyo ya kalleta cike da kasala yaja tsaki, kamar mai rowar muryarsa yace " wanka zanyi, kuma idan nafito zanzo muyi fira kafin sallar magrib",

Ameela tace "to shikenan, bari na hada maka ruwan zafi" tana karasa maganar tatashi tanufi bandaki, bada jimawaba tafito tace "Dee evry thng is rdy"

Hilal yatashi yacire kayansa ya daura tawul yanufi bandaki,
Bayan yafito suka zauna sukayi fira irin ta mata da miji, har zuwa magriba, sannan hilal yafita yaje masallaci yayi sallah,
Bai dawo gida saida aka kira isha akayi sallar isha, bayan angama sannan yadawo gida, yatsaya yarufe kofofin gidan sannan yakaraso cikin gidan,
A kan kujera yasameta tana dannar wayarta, tanajin shigowarsa tayi sauri ta ajiye, tana murmushi,
Shima ya mayar mata da amsar murmushinta kafin yakaraso gurinta yasamu kujera yazauna, suka kara taba fira, sannan hilal yatashi yace "tashi muje mukwanta" bata musa masaba tatashi suka nufi daki,
(A lokacin harna shiga dakin nafara rubuto muku abinda zai wakana sai abdul yayi saurin janyoni baya, yace karnaje lekon asirin ma aurata bakyau, banshiga dakinba, nafito amma ina gani aka kashe wutar dakin), ... Toooh??

Na:- ?Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles??
[10:20AM, 3/27/2016]
???? Amanar Aure ????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??17 and 18??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

tunda sassafe natashi, naci gaba da rubutuna,
babu abinda yachanza game da chart dinda Ameela takeyi, amma dai jiya bata samu damar chart din dareba,

Ko yau hilal bai tsaya karyawa cikin gidan ba, wanka kawai yayi yadauki jakarsa yawuce gurin aikinsa,

Bayan fitar hilal ta dauki wayarta tayita chart domin bata aikin komai, sabuwar kawarta data samu wato anisa sunyi chart yau mai dadi kuma hartayi save din number ta domin taga anisa tana da kirki sosai, duk wadan da tacewa zasu hadu shabiyun dare jiya, tabashi hakuri tace musu baccine ya dauketa, bata farkaba sai safe... Kujimun karya irin ta Ameela,
*****
A WANI GIDA

Wata wainar ake toyawa,

A Falo suke zaune sunyi jugum jugum, suna jiran amsar daga bakin AFHAM,
Afham yayi shiru ya sunkuyar da kansa kasa, yakasa magana

kawu bello yace "magana muke maka Amma kayi mana shiru, shin kanason AMAL ko kanada wadda kakesone"

Afham ya girgiza kai "aa kawu babu wadda nakeso amma kuma kawu maganar amal dince.."

Abban afham dayake zaune a gefe haushin afham yakamashi yayi saurin cewa "maganar amal dince.. To fada mana, abban afham yajuya ya kalli kawu bello yace "nifa kaine kake masa ta laluma, mumuka haifesa koshine ya haifemu, kagafa saboda gudun irin wannan matsalar yasa naki barinsa yayi karatu anan naija, nakaisa cen waje saboda karya taso ya bijirewa umarninmu, nifa nafada wannan auren shida Amal saifa anyisa domin wannan burin mune tun muna yara"
Chapter 3 · 0% Book details