← Book details Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Amanar Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hilal duk da yana namiji sai da ya zubda mata hawaye, ji yake kamar ya maida ciwon jikinshi saboda tsananin tausayin matarshi, momy ma kuka take cike da tausayi, wani duka akayiwa ameelah shi saita rufe ido, saboda ihun da ameelah keyi,
Abbah ne ke qarfafa musu gwiwan basu haquri yana kwantar musu da hnkali! (Su Ameela kam anji jiki, ko wannan ya isheta darasin cin Amanar Aure??)

Tufafin dake jikin ameelah duk sun lalace,

Abbah ne yace ma hilal yaje ya dauko mata kayanta saboda daga nan idan tafarka gida zasu wuce da ita saita qara samun sauqi! Jikinshi a sanyaye ya tafi cikin tunanin halin daya bar Ameelah!

Sai da yaje gidanne ya iske a bude kamar yadda ya barshi, yananan ynda suka barshi, qafarshi yaji ya daki wani abu akasa, ya duqa wayar Ameelah ne ya dago yana dubawa kusan 9 miss calls.

Bai duba ko na waye ba yana shirin ajewa wani kiran ya qara shgowa! "HMM" yaga an rubuta, ya dauka ya kara a kunnenshi yana shirin magana.. Hmm ya rugashi!

Cikin tattausan murya yake magana "haba! Haba!! Haba!!! My Ameelah ni babu abnda zaki cemun, kinsan yanda na shaqu dake bzanso kimin nisa ba koda na qaramin lokaci ne, ya za'ay ki brni tun jiya ba chat ba waya? Yayi shru yana jiran abnda zatace.

Shikau hilal mutuwar tsaye yayi da waya a hannunshi, ko motsi yaa kasayi! HMM yaci gaba "ya zaki shru ki qyaleni masoyiyah? Kinsan irin son da nake miki ko kin daina sonah ne? Nasan hkanma bzai yiwu ba amma kimin magana ko zanji dadi a raina!

Shi kadai yake magana yana qara ma hilal quncin zuciyah! Shi da kanshi ya gaji ya kashe har lokacin hilal yaa kasa cire wayar a kunnenshi yayi tsaye kamar wanda aka dasa!

??kuyi haquri plz da rashin jinmu kwana biyu dabaku yiba, duk muna exam ne???? Masu neman na bayanma su mana uzuri plz??

Na:-?Rabiatu sk mashi, da Mr, Smiles??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [9:49AM, 4/19/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??49 and 50??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

A sandare hilal yakai xaune saman kujira, "innalillahi wa inna ilaihin raju un" itace kalmar dayaketa maimaitawa a bakinsa, Ya tafe qirjinshi da hannu

yana mayar da nunfashi, gumi ya karwo masa, wani irin zafi yakeji a zuciyarsa, saboda tsananin kishi, idanuwansa sukayi jajir,
A hankali ya dora kansa a jikin kujera, ya rufe edo, kalaman dayaji a wayar sukadai ke masa yawa a kwakwalwa,

Cen bayan wasu yan mintuna ya bude idonsa, a lokacin hawaye suka sauka kan kumatunsa, yasa ya share,

Wayar ya dauko yafara duba number, number airtel ce, ya fiddo da wayarsa yayi copy na number, sannan yasaka wayoyin duka biyu aljihunsa, yatashi yanufi dakin ameelah,

wani dinkin atamfa yadauko mata tare da wani katon hijab, sannan yafito,
Saidai ya tsaya ya rufe gidan kam sannan yashiga motarsa, airtel office ya wuce direct yabasu number suduba masa, suka ce masa saiya jira nadan wani lokaci, gudun karsu abba suga yajima baidawowa yasa yabar musu number tare da cemusu zai dawo anjima,

Har a lokacin hilal yakasa dawowa hayyacinsa, jiyakeyi kamar zuciyarsa zasa fashe. Da zaiga wannan mutum da ya kira matarsa daya yayi mummunan saba masa,

Hakadai yakarasa gidan malam mai ruqiyya a bakin kofar gidan kafin yashiga yatsaya ya daidaita kansa domin ba yason su abba sugane yana cikin damuwa, sannan yashiga cikin gidan, ya mikawa momy tunfafin,
Abba da hilal suka fita momy ta chanzawa ameelah kaya, sannan suka dawo suna jiran farkawarta,

Kusan rabin wuni sukayi a gidan, tun cikin dare har safiya ta waye, sai misalin 12:00pm na rana ameelah ta farka, a hankali ta bude ido tana kallon su momy da suke gefe da ita, bakinta na rawa tace "momy ina ne nan meya kawoni nan"

murmushi momy tayi kafin takarsa gurinta tadafa kanta tace "ki kwantar da hankalinki, muna gurin nema miki lafiya ne "

Atsorace ameelah tace "lafiya kuma umma meya faru dani" momy tace " aike yakamata muyiwa wannan tambayar, meya faru dake a daren jiya ?"

Gaban ameelah yafadi domin ita harta mata da abinda yafaru da ita sai yanzu da momy tayi mata wannan maganar,
Bakinta yadau bari, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, abba da hilal suna gefe suna kallonta, ameelah tace "nima bansaniba "

Na:-? Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles??
[9:49AM, 4/19/2016]
????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??51 and 52??

ViOHW????

Cike da mamaki momy tace "kamarya baki saniba?" Abba yayi gyaran murya momy tajuyo gurinsa, abba yace "kedaina tambayarta kijira ta samu natsuwa daga baya maji sauran zancen a gurin mijinta"

momy taso tayi magana sai kuma tafara domin tasan tana musa masa zai hau masifa, saita kame bakinta,
Suna zaune malam yashigo, yatarar da ameelah ta farka, godiya yayiwa Allah sannan yayiwa abba bayanin zasu iya tafiya da ita, taje cen gida takara samun natsuwa, abba yaciro bandur na kudi yabawa malam sannnan yayi godiya suka dauki ameelah,
Gidan hilal suka wuce da ita, hilal yabude gidan suka shiga momy ta rikata suka karasa har cikin dakinta, saman gado ta ajiyeta sannan sukayi sallama dasu suka tafi,

A mota momy tafara masifa anhata taji matsalar yarta wlh ba ai mata adalciba, abba shiru yayi ko kulata baiba yaci gaba da tukinsa, harsuka kasa gida masifa take, suna shiga harabar gidan abba yakashe motar ya rigata fitowa zuciyarsa cike da takaici ya nufi cikin gidan,
*** **** ***
Hilal kuwa kamar jira yake su momy sufita, suna fita ya shigo dakin ameelah, tsaye yayi akanta yana kallonta, cike da bacin rai, fuskarsa a murtuke,

Yana yinsa kadai ameelah ta kalla tagane cewa akwai matsala, taja jiki takarasa bakin gado, "mijina meya matsalar"
Hilal ya tsuke fuska daman jiran yake tafar magana wayarta ya dauko yanuna mata, nan yafara fada cike da hargowa "daman abubuwan da kike aikatawa kenan a cikin wayarki, daman cin amanata kike.. Ehhh ameelah kifada mana?" yakarasa maganar cike da hargowa, da kuma zafin zuciya,

Ameelah tayi rau rau da edo, tsoro yakamata matuka, kaku yasoma kubuce mata, muryarta na rawa tace "daman .... Ehmm..ehmm... "

" daman me Kifada mana, kifada.... Ya nuna kansa da dan yatsa "me kika rasa a gurina, kulawa, soyayyah, addini , ko kuma me, menai miki kike cin amanar aure na" yayi shiru yana jiran ameelah tayi magana amma takasa kuka kawai take,
Hilal yadaga wayar cike da zafin rai "babu matakin dazan iya dauka akanki domin bazan iya sakin kiba amma nasan wannan ce koh, wannan ce matsalarmu koh, to daga yau babu ke babu kara rike waya"

Da karfi ya narka wayar a kasa, saida ta tarwatse gabaki daya,
Ko uffan bai kara cewa ba ya juya yabar dakin yana huci,

Yana fita ameelah ta share hawayenta daman na munafincine, dukawa tayi tadauko fasanshiyar wayarta, taduba sim dinta taga yana nan, ajiyar zuciya tayi, tace "alhamdulillah, daman ni saki kawai nake tsoro, amma tunda baka sake niba, da sauki" tayi murmushi takara kallon wayar kafin tace " hilal kenan kaida kanka zaka kara siyomin wata nasan yadda zanyi dakai"

Nan ta kwashe sauran fila2 wayarta ta ajiye gefe, sannan ta koma kan gado ta kwanta,
*** ***
A gefen afham kuwa, tun lokacin dayayi yiwa amal wulakanci momy tai masa magana, tun daga ranar yake gaba da momy, ya daina mata magana, koya ganta saidai ya sunkuyar dakai ya wuce, duk abinda yakeso saidai yasa aneesah ta kawo masa, (hmm kunji yayan zamani masu gaba da iyayensu, yanzu hakan wasun suke, da zaran iyayen sun sun musu fada to shikenan gaba ta shiga tsakaninsu, su ala dole ba a musu fada, hmm Allah dai ya kyauta)

Momy ce zaune a bakin gadon dakin abba tana kallonsa yana shiri, hulla yake sakawa yana duban mirror,
Damuwa ce tattare a fuskar momy tace "maganafa nake maka amma kayi banza dani, abubuwan yaron nanfa sunfara yimun yawa" tana karasa maganar tayi shiru,
Saida abba ya kammala saka hularsa sannan yajuyo gurin momy fuskarsa a daure yace " afham yana ina" momy tace "yana dakinsa mana " abba yafara taku "zomuje " yanufi hanyar fita, momy uffan baka kara cewaba tabi bayan sa,

Direct dakin afham suka shiga, abba ya turo kofar da karfi yana kiran sunansa, yanajin shigowarsu ya mike tsaye, abba yatsaya yana kallonsa, afham ya sunkuyar da kai, abba yafara masifa "ka kyauta, kuma kayi daidai, wato kai dan zamani koh, kana gaba da mahaifiyarka saboda tayi maka magana akan Amal, to shikenan nima saika shirya yin gabar dani domin wlh bazan janye maganar aurenka da amal ba, idan zaka shirya kashirya domin munsaka ranar aurenku nan da sati daya, marar mutunci kawai " abba yakarasa maganar cike da bacin rai, yajuya yabar dakin,
Kafin momy tafita saida ta dallawa afham harara, sannna tafita,

Afham ya duke kai yana kuka, sai bayan sunfita sannnan yazauna yafara masifa "Allah dai yasani nidai banason amal, auren dole saikace wata macce, wlh bazai yuyuba saidai nabar musu gidan su zauna sukadai, kuma suje su samo wani dan su aura masa amal, wlh gidan zan bari...

Na:- ? Rabi'atu sk mash da Mr, Similes??
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles??: [1:12PM, 4/24/2016] ????Amanar Aure????
???????? www.gidannovels.blogspot.com
??53and54??

Kaya afham yashiga hadawa, saida yacika akwatinsa kaf, sannan ya tsaya yana tunanin idan yafita ina zai dosa, ina zaije,
Kofar dakinsa yaji anturo, yakurawa kofar ido yana jiran yaga wazai shigo,
Aneesah ce tayi tsaye tana kallon yana yinsa, akwatin data gani a gefensa ta kurawa ido cike mamaki tace "yaya afham mekake shirin aikatawa ne, naga kahada kaya"

Afham yakauda kai daga kallon datake masa yaci gaba da rufe zip din akwatinsa, saida ya kammala rufewa yadaga kai yasake kallon aneesah "gidan nan zan bari, kuma idan natafi kigayawa su abba karsu nemeni, domin nabar gidan nan har abada, domin nayi shawara da zuciyata barin gidan nan shine kadai katangata agareni akan auren amal "
Chapter 8 · 0% Book details