Sashe 9
Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shuke shuken na nufi katangar. A daidai lokacin ne to sainaga tagar daki ta bude nayi sauri na sunkuya acikin shuke shuken dake daf da tagar kadan ya rage tagar dakin ta buge min kai domin jikin ginin dakin nake bi bantaba zaton za'a bude tagar din ba haka nan shiyasa ni tunanin ko na koma da baya na sake hanya domin a baya na akwai jerin wasu tangagogin har guda biyar kafin nakai ga katangar danake hari. Bangama shawara ba sai na sake jin abin da yasa zuciyata harbawa da karfin gaske. Wata shakakkiyar muryar magidancin mutum tace..... Ke FADILA tashi munafuka INA KIKA JE DA DADDARE naji shiru na dan lokaci sai Naji an sake cewa Ke ba ke Nake yiwa magana ba? Shiru ba'a amsa ba can sai Naji an amsa BABA NI WALLAHI BABU INDA NAJE........ Jin muryar shi yasani mikewa zumbur kamar wanda aka sokawa kibiya na sake saurarawa dakyau To don iyayen ki ni zakiyiwa karya ina kallon ki fa jiya ana wannan ruwan kika fice dauke da akwati a hannun ki Ina Kika kai akwatin ina kuma kika ajiye motar da kika dauka? Wani abu mai Kamar gizo gizo ya biyo tun daga babban dan yatsana har zuwa bayana. Bab...... Don Allah tafara kuka na Mike tsaye ahankali na leka tagar dakin sannan ne to naji numfashina ya dauke ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI NE [13:00, 1/24/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-16 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI ne. . Tana zaune abakin gado ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta gashin kanta awarware wani katon mutum ne dattijo tsaye akanta sanye da babbar riga bana raba daya biyu mahifinta ne. Naci gaba da saurarensu jikina na rawa. Ina kika kai jaririn munafuka? Mutumin yace sannan ya matsa kusa da ita ya gaura mata mari tas ina kuka kai jaririn iye? Wato jefar dashi kukayi ko? To zakici gidanku.... Yau daga ke har shegiyar uwarki data bataki sai kun fice min daga gidana ke kuwa ahannun yanda zan mika ki. Kai Allah wadaran haihuwar irinku haihuwar bakin ciki. Adaidai lokacin ne to naji budewar kofar acan cikin dakin. Kada ka zageni. Wata sassanyar muryar mace tace duk abinda yafaru akan FADILA kai ka janyo ai sai da nace dakai kada ka riga sakarwa fadila kudi tun tana karama nayi nayi dakai ka ki kasai mata mota har guda uku don shagwaba har kasashen turai kake tafiya da ita tokuma shin ayanzu don.....idonta ya bude da iskanci har ta sami nasarar ba wa... DAN GWARZO shine kuma zaka zargeni ? Matar tayi shiru tana maida numfashi ai saida nace dakai a zubar da cikin ka ki yo kuma yanzu don ta haifi dan ta jefar shine zaka zo kahauta da duka ka dagata don Allah Alhaji kada ka kashe min 'ya ba fa taka bace kai kadai. Mutumin ya dubi matar a fusace yace. Allah wadaranki Wallahi nima kaddara ce tasa na aure ki rabon dai in sami wannan tsinanniyar yarinyar da zata janyo min abin kunya agari kema kafin na aure ki ciki nawa kikayi aka zubar? To kace ma fadilar ba 'yar ka bace mana. Matar tace a fusace nan da nan sai maigidan ya sake shake yarinyar yahauta da duka. Wayyo Allah baba na shiga uku fadila ta fada cikin kuka. Baki shiga uku ba ma tukunna sai ma na dora wuka a mokogoronki don ubanki. Ina kika jefar da jaririn. . Batare da na sake jiran komai ba sai kawai na dauki akwatin na koma... Da gudu ban damu da ko masu gadin zasu ganni su sake kamani ba. Ina zuwa saina nemi kofar shiga babban falon na tura kofa na shiga bayan nayi yan dube dube saina jiyo hayaniya awani daki. Hakan shi ya bani damar gane cewa shine dakin da nake nema. A ina kika jefar da jaririn? Ya sake tambayarta banyi wata-wata ba saina tura kofar na fada cikin dakin babu sallama. Gaba daya mutanen uku miji da mata dakuma 'ya suka juyo a firgice suka dubeni kamar wani Aljani. Kayi hakuri alhaji da shigowata babu sallama. Nace dashi. Zuwa nayi na ceci ran 'yarka domin ba sai ka dora wukar a makogoronta ba. Ga Jaririn nan bai yi nisa ba dazun nan tayi min kyauta dashi amatsayin kyakkyawan jaruminta na shekara. Nayi musu murmushin yake su kuma suka dubeni saroro kamar wadanda suke tunanin na tabu. Na ajiye akwatin agabansu sannan nace. Jaririnta yana cikin nan yana barci ni zan koma Alhaji saidai kuma don Allah kayiwa masu gadin nan magana domin su Barawo suka kamani jiya da daddare adakin injin dake baku wuta na kwana. Allah ne ma yasa zan raba wannan rikici shiyasa na fito. . Karya yake Wallahi baba shine ya sace jaririn wallahi shi ya sace min fadila tace. Yi min shiru munafuka mutumin ya buga mata tsawa na dubeta nayi murmushi sannan na lalubi aljihuna na dauko wasikar datayi min na mikawa mutumin nace. Duba min nan Alhaji shin wannan rubutuna ne ko nata? Ni sauri nakeyi domin muna da fim din da zamu fara idan an jima. Idan kuma kana bukatar karin bayani to saurareni da kyau. Mutumin ya amshi wasikar daga hannuna nikuma saina dubi Fadila itama ta dubeni nayi mata murmushi nace. Kadan ya rage ki kai labari yan mata to saidai kuma kyautar da kikayi min tayi girma dayawa. In banda abinci ina ke ina yi min kyautar Jariri? Ai tayi min yawa ina laifin ma ki bani Kyautar KWALBAR TURARE KO FULAWA Adaidai nan naji sautin sawun masu gadin suna ta guje guje atsakar gidan. Lafiya meye haka? Mutumin yace yana dubana nayi masa murmushi nace dashi kada ka damu masu gadinka ne suke nemana. Fadila ta daga kai idanunta cike da kwalla tace. HILAL nace Na'am FADILA Tace don Allah ka yafe ni. Na dubeta na tsawon dakiku sainaji tausayinta ya kamani saina dubeta da tattausan murmushi nace. Na yafe miki Fadila saiki nemi kuma gafara agurin Ubangijinki dakuma mahaifinki. Fadila ta fashe da kuka. Adaidai lokacin ne masu gadin suka kwankwasa kofa. Ku shigo nace dasu. Waya saka? Mutumin yace dani na dubeshi nayi masa murmushin ko in kula. . HUDU 4 . Kusan minti guda muka share tsaye muna duban kofar kodayake fadila bata kallon kowa sai ni. Kofar dakin ta fara budewa ahankali kamar iskace ke turota sannan sai kakkausar muryar kartin nan tace. Salamu Alaikum....Alhaji mu shigo ne? Mahaifiyar fadila wacce ke tsaye rike da tsantsa tana huci kamar kububuwa. Mamuda ne? Shigo kai kadai. Maigadin yace bakinsa na rawa Garsakeken katon ya shigo dakin cikin sanda yana zuwa saiya dubeni ya rusuna agaban maigidansa yace. Kayi hakuri don Allah Alhaji Wallahi adakin injin bada wuta muka sashi ya gudo. Bari inyi waje dashi na hada shi da yan sanda. Yana gama fadi saiya yunkuro DAMKE NI............ . 17 Yana Tafe Anjima Insha Allahu Zan Biya Bashin jiya I banyi ba saboda balaguron da mukayi [13:00, 1/24/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-17 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Yana gama fada ya yunkro zai Damkeni... . Uhm Uhm mamuda kada ka taba shi. Maigidan yace cikin karaji. Mamuda yayi cak kamar ruwa ya cinye shi. Alhaji barawo ne... Kada ka damu mamuda jeka waje kaci gaba da aikinka kawai. Toh yallabai katon yace cikin girmamawa lokaci guda kuma ya nufi kofa. Af mamuda... Maigidan ya kira sunansa katon ya juyo cikin sauri na lura duk a rude yake me yiwuwa tunda yake gadi agidan bai taba shiga wannan dakin ba. Wannan maganar daga kai sai mu ka. Kafadawa abokan aikina ma bana so ta wuce tsakaninku. Kakuma kawo min akwatin daya bari adakin injin wutar. Katon ya gyada kai cikin fahimta sannan saiya dubeni. Kallon dayayi min na iya nufin komai. Nayi masa murmushi cikin sanda ya juya kamar yadda ya shigo ya sulale daga dakin. . Muka sake yin shiru na tsahon mintuna akaro na biyu mahaifin fadila na kallon tattausan kilishin dake dakin yayinda fadila ke kallon. Nikuwa idanuna na kallon mahaifiyar fadila wacce ta kurawa fadila idanu bata ko kiftawa. Azuciya na yarda da maganar mahaifin fadila dayace da mahaifiyarta tun farko itace ta bata fadila domin na lura da alamun damuwa karara a fuskarta dakuma kauna ga fadila yarta. Ku shiga daga ciki RASHIDA. Maigidan ya kira sunan matarsa akaro na farko. Nayi zaton zata hau masifa amma maimakon hakan saita dubi Fadila tace. Taho mu tafi. Fadila tayi min kallon gefe idanu tabi mahaifiyarta suka bi ta wata yar tsukakkiyar kofa suka shige ciki. Maigidan ya dubeni gamida sassauta yanayin dake fuskarsa yace. Zauna bawan Allah ya nuna min kujera araina sainaji na kaunace. Hakan shi yasa nayi biyayya na zauna batareda nayi jayayya ba. Ya danyi shiru gamida sakin wani tattausan tari kana sai ya dago kansa.. . Tun tana karama muke fama da ita kadarar yarinya ce ka ganta nan gashi da babu abinda ta rasa agidan nan na daga kayan alatu amma bata iya zama sai shegen yawo. Mahaifiyarta ce ta bata tun tana karama.... Yayi shiru akwai alamar takaici karara a fuskarsa. Na tausaya masa. Babu daman nayiwa yar cikina fada sai mahaifiyarta ta hauni da masifa. Haka kullum nake fama kwatsam ran nan sai muka fahimci yar banzar yarinyar tayi ciki mahaifiyarta tayita uzura min sai a zubar da cikin. Nikuma ina tuna mata yin hakan barna ce domin kisan kaine saimu bata goma biyar bata gyaru ba. Haka mukayi ta fama har zuwa ranar data haifu shine yanzu don tsabar rashin imani suka hada baki ita da mahaifiyarta suka kashe dan jaririn wata daya kawai da haihuwa....hawaye ya fara kwarara akan fuskarsa. Na yunkura akan kujerar cikin damuwa ni duk maganganun sun fara gundurata duk da dai basu shafeni ba ni abinda kawai nake so shine yabar ni na tafi dan na lura tuni har gari yafara haske. Duk da yake banga agogo ba ina kyautata tsammanin biyar na safe ta wuce. Fita fim dinsu Alhajiji ne araina. Alhaji.... Allah ya sawwake.. Nace dashi ina ganin in babu wani sauran abu to ni zan tafi alhaji domin kaga duk wannan abubuwan da