← Book details Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 15

Sashe 10

Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kake fada bai kamata na sani ba domin sirrinku ne ku kadai bai shafe ni ba. Mutumin ya dago kai yana girgiza shi. Ya shafe ka bawan Allah. Awannan karon ni na dube shi cikin mamaki. Tayaya ya shafeni? Mutumin ya sunkuyar da kai na tsawon lokaci yana girgiza kai. Can saiya dago alamar damuwa a fuskarsa a fili. Ga mamakina sainaga ya mike tsaye ya nufo inda nake ya sunkuya akaina ya dafa kafadata yace. Bantaba neman alfarma agurin kowa ba tun da nake.... Amma yau zan fara. Abinda yace sai ya daga rudani. Ban fahimce ka ba. Ya daga girarsa sama kamar biri na lura karfin ikonsa da kwarjininsa na attajiri sun fara dawowa gare shi. Abinda nake nufi shine ina neman kayi min alfarma guda biyu bawan Allah. Ni kuwa zan saka ma da abinda baka taba zato ba. Numfashina ya dauke abinda ban taba zato ba? Indai ba kuskuren fahimtarsa nayi ba nasan abinda kalmar ke nufi muddin ta fito daga bakin ATTAJIRI. Wa.... Wacce alfarma kake so? Ya dubeni na tsawon lokaci kana yace. So nake ka rufa min asiri maganar jaririn nan ta zama daga kai samu don Allah na rokeka ka rufa min asiri domin idan ta fito fili nagama yawo... Kaga shekara mai zuwa nake son tsayawa takarar GWAMNA zuciyata ta harba tsakanin hakarkarina. Bakina na rawa nace dashi. Indai don wannan ne Alhaji kada ka damu in Allah yaso babu wanda zai kara jin ta abakina. Nayi tsammanin zai saki fuska cikin jin dadi amma sainaga haryanzu dai tana nan yadda take babu yabo babu fallasa. Sai kuma alfarma ta biyu bawan Allah yace. Lokaci guda kuma naga akwai alamar razana a fuskarsa. Fadi muji ranka ya dade. Nace dashi ina dada kwantar da murya domin kalaman dayayi ne zaiyi min abinda ban taba tsammani ba yasa zuciyata lissafe-lissafe,,,, na tuna da dimbin bashin da ake bina. . Bawan Allaj me ye sunan? Sunana Hilal. Yawwa hilal. Alfarmar danake nema tanada nauyi amma kamar yanda nace dakai abaya zan saka ma. Ya danyi shiru sannan saiyace, Zaka iya hilal? Na dubeshi cikin mamaki nace to ai bansan me zanyi ba Alhaji. Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya daga kansa ya dubeni ido da ido yace. SO NAKE KA AURI 'YA TA FADILA. . ************ ************** ************* ********* . KU HUTA TUKUNNA SAI MUCI GABA . NA SADAUKAR DA WANNAN KASHI NA 17 GA DUK WAYANDA SUKA JE KADUNA TA'AZIYAR ABOKIN HULDA AWANNAN DANDALIN IBRAHIM TAREDA DUK WAYANDA SUKAYI TA BUGO WAYA SUNA MIKA TA'AZIYAR SU TA HANNUN MU DAKUMA MASU COMMENT A CIKIN POSTING DINA NA RASUWAR DA TAFIYA TA'AZIYAR ALLAH YAYI MANA RAHAMA DA RAHAMARSA BADON AIKIN MU BA [13:22, 1/27/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-18 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya. . Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya dago kansa ya dubeni ido da ido yace. SO NAKE KA AURI 'YA TA FADILA. . ********* ******** *********** . Ba karamar girgiza nayi da kalamansa ba. Kaduwar danayi ita ta sani zaune nayi mutuwar tsohuwa na kasa cewa dashi komai domin bansan me zance dashi ba. Na auri fadila? Chab babbar magana. Yaya kayi shiru Hilal ko baka sonta ne? Na girgiza kaina cikin kaduwa. Bahaka bane Alhaji... Kaga dai yan sa'o'in da suka wuce na santa kuma.... Ya daga min hannu. Hilal basai ka fada ba nasan abinda kake tunani. Auren yarinyar banza kamar fadila ko? Yarinyar data yi cikin shege ko? Ya danyi shiru sannan yaci gaba. Abinda yasa na baka duk tarihinta abaya shine so nake ka aure ta da halinta. Kuma ko da yake baka dade da saninta ba kai kasan fadila kyakkyawa ce bata da wani aibu in ya wuce na dabi'unta na banza. Hilal inason ka sani cewa in dai kana sonta zaka aureta da halinta to zan saka maka da babban alheri domin tuntuni na gaji da zamanta agidan nan. Ganin sharrin dataso ta dora ma shi yasani tunanin babu wanda yadace ya aureta sai Kai. Na gama rudewa zuciyata sai dum dum dum takeyi duk abubuwan dake faruwa ji nake kamar amafarki. Mecece sana'ar ka hilal? Mutumin ya tambayeni hakan dayace shi ya sani dada gyara zama. Harkar shirin fim nakeyi... Nace dashi cikin gaggawa mutumin ya shafi kansa da tafin hannunsa na dama yace. Saurareni da kyau hilal zan baka lokaci kayi shawara zan kuma sami Fadila nayi mata maganar. Ya danyi shiru sannan yaci gaba. In dai zaka yarda zaka aureta da halinta nayi maka alkawarin zan sayo maka duk abubuwan da kake bukata na harkar shirin fim idan nafita kasashen ketare. Ko gobe ka amince kazo ka sameni ka fada min zan aika cikin sati guda a sayo maka duk abinda kake bukata inason kuma ka nemi gida mai girman gaske a ko ina ne zansa arugujeshi agina maka kamfanin fina finanka zan kuma zuba maka jarin naira Milliyan biyar kyauta. Na shiga uku nace cikin zuciyata. Milliyan biyar? . Alhaji zanyi shawara.... Abubuwan sunyi yawa akaro na farko sai ya saki wata tattausar dariya yace. Ai kadan ma ka gani ya mike tsaye sosai zo muje in rakaka. Jikina na rawa na bishi abaya. Ruwan saman ya tsaya cak. Tuni gari har yafara haske naji sa'ar da agogo ya buga karfe shida na safe. Muka bi ta wata yar kofar sai na ga mun bulla a filin ajiye motoci. Motovi bakwai ne ejere kusan duk sababbi ne akwai jeep guda biyu Lexux daya marsandi biyu da honda shudiya da ja. Ga mamakina sai naga ya tsaya ajikin motocin. Alokacin ne fa nayi masa kyakkyawan kallo dogo ne siriri fari mai gashi irin na buzaye yalo yako me yiwuwa bafilatani ne kokuma mutumin Mali. Allah masani. Sa'ar daya dubeni yayi dariya sainaga hakorinsa na sama guda daya a bantare. . Zan baka sati guda kayi shawara hilal abinda ka yanke saika zo ka fada min ni da kaina zan sami iyayenka. A ina kake ne? Ya tambayeni hannunsa na dama akan rufin motar lexux. Anan unguwar nake can ciki nake (No 106) Af ashe ma makwabvina ne. Ya fadada murmushinsa ya laluba aljihun doguwar jallabiyar shudiya dake jikinsa ya dauko dan makullin mota sannan ya nufi shudiyar motar honda. Alha..... Alhaji bama sai.... Ka bari kawai saina karasa ma akasa. Murmushinsa ya fadada. Uhm hilal kenan kaifa nace dakai yanzu ka dan ma ka gani. Ungo rike wannan. Ya miko min dan makullin mota ya nuna shudiyar motar da baki yace. Gata nan nabaka kyauta. Wannan kyautar bata cikin wancan yarjejeniyar tamu koda baka amince ba wannan motar dai taka ce... Na bude baki cikin kaduwa da mamaki chab. Dan saurayi hilal anya kuwa ba mafarki kake ba? Bansan irin godiyar da zanyi maka ba alhaji na gode Allah... Ya katse ni ta hanyar daga min hannunsa a fuska.. Kada ka gode min Domin asirin dakayi alkawarin zaka rufa min yafi dahaka. Da'ace ciniki zamuyi. Ya dan saurara yana dan dukan saman motar da yan yatsunsa. Shikenan hilal sainaji daga gareka kana iya shiga motarka Allah yabamu alheri nakuma gode domin nine da godiya. Yana gama fadi saiya juya yayi ciki da sauri. Yakoma cikin gidan ta inda muka fito. . Na dade anan saroro a rude domin abin kamar a mafarki awani bangare kuma na zuciyata sai cewa akayi dani wannan yaudarar ce irin na aljanu. Amma sa'ar dana bude hondar na lume acikin kujerar direba sai na gaskata faruwar dukkan al'amarin. Ada na dauka dana shiga motar zan ga ta bace saina tsinci kaina kwance akan tsohon gadona. Amma tabbas ko shakka babu duk abinda nagani tun daga dare har zuwa wayewar gari gaskiyane babu zancen aikin aljanu KAMAR A FIM. . Nayiwa motar key na tashi sannan na fara tukata ahankali na nufi kofar gidan azuciyata nace Allah mai yadda yaso yan sa'o'i kadan nine ke yawo da mataccen jariri ina neman inda zan jefar dashi sannan lokaci guda kuma na tsinci kaina amatsayin barawo sai gashi akarshe cikin ikon Rabbana motovina da bashi ya cinye daya ta dawo daga cikinsu. Koda na fara tuka motar sai na juyo da nufin na yiwa ginin gidan kallon karshe gabana yayi RAS. Sa'ar dana hangi..... . AKWAI CIGABAN ANJIMA IDAN KUNA SO [13:24, 1/27/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-19 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Gabana ya fadi ras sa'ar dana hangi FADILA tsaye agindin taga tana daga min hannu ba ganin nata ne yasa zuciyata ninkaya ba sai tunanin cewa ayanzu abinda ke tsakanina da zama miloniya shine kawai na yarda zan aureta. LAURIYYA ta fado min arai. Ga koshi ga kwanan yunwa nace araina. Koda masu gadin suka hangoni tafe sai sukayi sauri suka bude min kofa atunaninsu ubangidansu ne koda suka fahimci nine sai suka bi ni da kallo bakunansu a bude cikin kaduwa. Dankareren katon daya kamoni amatsayin barawo idanunsa suka firfito cikin kaduwa kamar idanun kwado. Na daga masa hannu harda murmushi na take sabuwar motata abina na nufi gida. . ********** ********* ********* . Tun daga nesa na hangesu tsaye akofar gidana motoci biyu da mutane biyar kowannensu nata waige waige suna ta duban hanya akwai alamar damuwa a fuskokinsu. Nayi fakin da dalleliyar hondar adaf dasu ina ganin alhajiji ta cikin gilashin motar yana duban agogo baiko damu daya kalli motar data tsaya afad dasu ba domin nasan babu wanda acikinsu yake tsammanin nine na bude kofar motar ahankali. Sannunku da zuwa furodusa. Nace dasu da faffadan murmushi. Duk su biyar din suka juyo acikin mamaki ganin nine sai fuskokinsu suka washe. Dan Banza daga ina a ina ka kwana? Tun dazu karfe biyar da rabi muke nan muna jiranka duk sauran yan wasan sunyi gaba kai kawai ake jira na dubeshi bayana jingine da motar ina karkada dan makulli. Kun aika gidan kawuna ne nemana? Na tambayesu gabana na faduwa. A'a bamu aika ba daman USMAN ne ma yace mu aika nikuwa nasan da wahala in kana ciki. Nayi ajiyar zuciya da sun aika gidan kawuna nemana da sun janyo min jaf'i. Bari in shiga gida in dan wasa ruwa sai mu tafi ko? Usman dake ta kallona tun zuwana yasaka magana saboda kullewa sai kawai safa da marwa yake. Kaga
Chapter 10 · 0% Book details