← Book details Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 15

Sashe 5

Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fahimci abinda nake nufi. Toh hilal sai gobe din kenan ma hadu. Kada ka manta fa da asussuba alhajiji yace zaku fita.... Na dubeta cikin murmushi ban taba sonta har cikin zuciyata ba kamar wannan ranar. Dan haka sa'ar dana fara zirga zirga acikin dakin inata lissafin dimbin basussukan da suke kaina sainayi mamakin irin tsabar son da lauriyya takeyimin. Kafin naci gaba da labarin nan danake baka bari in baka hoton lauriyya. Dakuma ranar da muka fara haduwa da ita domin lauriyya tana da matukar muhimmanci acikin labarin. . LAURIYYA doguwa ce launin kofi mararta ashafe siraran yan yatsun kafarta da na hannu gami da dan madaidaicin bakinta ma'abocin tattausan murmushi tare da taimakon dara daran fararen idanunta gamida dogon hancinta mai kamar kan biro su suka fallasa kyawun da ta gado daga kakanninta fulani mazauna Gongola. Haduwar mu da ita tsautsayi ce domin adaren wata juma'a ne nafito daga ofishina mukayi kicibis da ita dauke da jaka kallo daya nayi mata ta burgeni. Sannan naga zatayi daidai da budurwar da muke bukata acikin fim dina na DAREN MUTUWA. Kaine Hilal? Kwarai kuwa nine Wallahi daga gongola nake masauki nake nema. Hakanan a saukake don tsabar taren aradu da ka dakuma neman tsautsayi da rashin tunani sai kyawunta ya rufe min idanu na samar mata masauki batare da na binciki abinda ya rabo ta daga gida ba. Yan kwanaki kadan na fahimci ashe tanada ilmin boko mai dan tsayi domin har diploma ce da ita abangaren tsimi da tanadi. Haka nan tanada wayo da hikima hakan ce tasa na maida ita amatsayin sakatariya lokaci lokaci kuma nakan jefata a fina finai naso ace duk fim din da zan fito tare zamu fito to amma saboda acewarta. Bana son fuskata tayi yawa acikin fina finai sai kawai na kyaleta ban kuma tambayarta dalili ba. Har yanzun nan da nake safa da marwa cikin dakin bayan shekaru biyu cif cif da faruwar al'amarin ina tambayar kaina shin me ya raba lauriyya daga gaban iyayenta? Hakika lauriyya ta fara shiga raina sosai. Adacan sa'ar dana fara ganinta kyawunta ne kawai ke burgeni babu dadi ba ragi. To amma ayanzu abin ya wuce haka lauriyya ta zama jinin jikina abin tunaninaba dan komai ba kuwa sai don na fahimci ita kadai ke damuwa da fushina ita kadai ke farin ciki da karuwata ita kadaice komai ke sani dariya ta dauke min kewa aduk lokacin dana shiga damuwa. Gobe in Allah yaso saina tambayeta labarinta baki daya. Nayiwa kaina alkawarin hakan. . Haryanzu ruwan saman ake tafkawa kamar da bakin kwarya na sake nazarin sabon dakin dana dawo cikin takaici domin baikai ko rabin bandakin da nake wanka ba atsohon gidana dana sayar na biya bashi. Dakin danake ciki dan kankani ne kamar dai sauran dakunan da ake yiwa boyi boyi agidajen gwamnati kujeru uku ne kacal dakin ya iya dauka. Koda yake dai in ma zaici fiye da hakan ba samu zaiyi ba domin duk na sayar da kujeruna sama da talatin na biya bashi ayanzu kam in kadauke tsohon gadon katakon dake dakin katifar daya dana tsira da ita gamida talabijin daya mai kala da bidiyo da rediyon jin labarai mai gidan kaset daya dakin babu komai sai shegen zafi gamida manya manyan saurayen dake fizgar rigata ta baya ina kwacewa dakyar. Dakin danake zaune ayanzu an tanadae shi ne dan yaron gida dayake kawuna ma'aikacin gwamnati ne ya kuma san irin yadda mutane ke ta kawo min ziyara sai ya shawarce ni dana dawo nan na tare tunda da dai karayar arziki tazo min. . Nakoma bakin gadon na zauna sannan na cire rigar dake jikina na kwanta akan tsohon gadon inajin zazzafar iskar fankar dake busowa akan fuskata. Sannan kuma lokaci guda ina mai addu'ar allah sa adauke ruwan kona sami damar bude kofar nasha tsabtatacciyar iska. Ina nan kwance idanuna rufe zuciyata cike da zullumin basussukan da ake bina gamida tunanin Lauriyya ga kuma shegen zafi wannan shi ya hana barci ya daukeni. Nashiga cikin damuwa domin nasan gobe da asusussuba zan tashi domin tafiya sabon fim din da aka daukeni na Sinad production. Gashi kuma yanzu ba da ba. Domin banida ko jaki ballantana mota. Bansan sa'ar da barci ya daukeni ba adaren. Acikin barcin ne harna fara mafarki wai anata bubbuga min kofar dakin danake ciki kuma wai muryar lauriyyace ke kirana. Nayi firgigit na farka ina mitsitstsika idanuna sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa a gaske kofar dakin nawa ake ta bugawa....... [20:28, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-09 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa da gaske kofar dakin nawa ake bubbugawa. Nayi fakare kamar zakara zuciyata na harbawa cikin mamakin ganin mafarkin nawa yazama Gaskiya. To saidai kuma buga kofar yasani cikin damuwa domin na lura haryanzu sheka uban ruwan ake kamar da bakin kwarya tabbas nasan ba lauriyya bace. Toh wanene ? Na tambayi kaina nadubi agogon dake jikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da mukayi shirin flm din Daren mutuwa dasu. Karfe biyu da rabi na dare. Domin kuwa banga wanda zai buga min kofa ba cikin wannan uban daren sai ko barawo. Aka sake bugun kofar dakin Das Das Das kamar ana kugun kwarya da sullen kara. Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin ko wanene ke bugun kofar to yana tausaya mata. Aka sake bugawa Raf Raf Raf har sau uku gumi yafara sartu a goshina hakika amafi yawan fina finan danake fitowa ni jarumi ne mai zafi marar tsoro to amma azahiri tsorone dani amar farar kura domin dan karamin yaro ma na iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona. Me yiwuwa lauriyya ce.... Kai ba ita bace babu mamaki dai kawuna ne nace dakaina. To amma jikina baiyi amanna da kalaman zuciyata ba domin tun ranar dana tare agidan kawuna bai taba lekowa bangaren danake ba in son ganina yake saidai ya turo ayi kirana indai shine to tabbas ba lafiya ba. Can kuma sai wata zuciyar tace dani to ai kuwa idan shine kiran sunana zaiyi kai tsaye basai ya tsaya yanata kwankwashe kwankwashen kofar ba. Wannan shiyasa cikina ya dada durar ruwa jikina ya dauki bari nan da nan naji hakorana sun fada haduwa da juna kaf kaf kaf saboda tsoro. Najuya ahankali akan tsohon gadon na dubi yan tarkacen da suke dakin nace da kaina. In dan wannan ne sai na basu su tafi sun dauka jiya yau ce. Kawai wayannan barayi da rashin basira suke su basuda labarin na tsiyace ne ? Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na doddoke su acikin sauki ina hura hanci wasu ma darakta yasa na kakkama su na daure. To amma duk wannan daban domin wasa ne yanzu kam shine azahiri domin gasu akofar dakina. Na lalubi aljihuna na dauko rubabbiyar naira goman da mai mashin yabani canji daman naira hamsin ce kadai ta rage a aljihuna sa'ar da zamu rabu da lauriyya na bata ashirin ta tafi gida nikuma na hawo acaba naira ashirin nakaraso gida da goma. Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi a bude koda yake kusan ko yaushe ma ahaka take saboda abokai da maziyartan dake yawan zuwa gurina cikin dare wasu lokutan ma sai na dawo daga daukar fim cikin dare zan sami baki suna jirana. Amman ban taba samun bakin kusan karfe biyu na dare ba. Raf Raf akaci gaba da buga kofar na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin inata salati da sallallami. Wai wan....ne ? Nace muryata ashakre ban iya shaida ta ba amatsayin tawa, maimakon abani amsa sainaji an sake kwankwasawa. Wai wanene? Nasake kuga tambayar shiru ba amsa ba. Haushi yakamani saina tuna da fim din DAREN MUTUWA. Mun taba yin wani guri mai kamar wannan inda wasu barayi sukazo suna kokarin balla kofata nikuma nabari saida suka jingina da kofar suka gama bada karfinsu akanta sai na bude kofar da karfi suka zubo dakin kamar an handakosu nikuma na doddoke su. Yau ma zan maimaita nace cikin zuciyata saidai kuma sabanin wancan karon yanzu idan Allah yabani sa'a suka fado cikin dakin tsallake su zanyi na Gudu. Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi jin hakan shiyasani tunanin me yiwuwa mai bugun kofar jikinsa ya jingina akofar don haka cikin sauri saina zare sakata na janyo kofar da karfi sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abinda ya biyo baya. Ashe dai ko a gaske Jarumi ne. Wata zazzakar murya tace dani. Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki. Mace ce tsaye akofar dakin sanye da doguwar riga baka da jan lullubi akanta jikinta na digar ruwan saman daya daketa hakika ajin farko ce ajerin kyawawa. . ******** ********** ********** . Mun shafe kusan rabin minti muna tsaye muna duban juna haushi da fargaba da mamaki sun hanani magana. Shin ko na iya shigowa sanyi nakeji gaskiya kuma duk kayana ajike suke. Idanuna suka kai ga katuwar akwatin mai taya dake hannunta sai hakan ya tuno min da farkon haduwarmu da LAURIYYA. Malama ina fatan dai lafiya?.... Ma'ana daga ina kike cikin wannan uban daren? Kuma da wacce kika zo? Yar budurwar ta dubeni sa'annan t jefeni da lallausan murmushin Allah kasheni don dadi. Lafiya kalau Hilal tun daga wata nisan duniya nataho gareka domin kawai na ganka na dade ina ganin fina finanka ina kaunar araina da begen ganinka shne naga bazan iya jurewa ba sainazo na ganka da idanuna. Ta danyi shiru tana kokarin share ruwan dake sartu daga cikin gashinta zuwa fuskarta. Gashi dai cikin duhu muke tsaye dakin babu wuta amma duk dahaka fuskarta har sheki takeyi idan akayi Walkiya. Ko makaho ya lalubeta yasan Allah yayi halitta agurin. Tsarki ya tabbata ga mahaliccin kyawawa. Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba... . KUCI GABA DA HAKURI DAI SAURA KIRIS HARHARDEWAR DA LABARIN YAYI WAJEN TYPING DINA YA WARWARE [20:29, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-10 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar
Chapter 5 · 0% Book details