← Book details Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 15

Sashe 11

Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

malam tun dazu da muke jiranka fa anan sai zamuyi ta jira har rana tayi mana dubi fa karfe shida da rabi. Na fashe da dariya. Dubi rigata fa usman ka gani gaba dayansu suka zubo min idanu sabodar tsabar kaguwa da sukayi basu ko kula da yanayin da rigar ruwan dake jikina take ba. Me ya sami rigarka haka naga duk a yayyage... A'a kaima ai duk a jike kake da chabi. Duk jikinka tun kafin suyi tambayar nagama tsara amsar da zan basu cikin zuciyata. Ai jiya muna rabuwa dakai lokacin daka bar mu da Lauriyya sai wasu suka daukeni muka tafi daukar wani fim. Da Allah da Annabi suka janyeni domin wai jarumin da sukayi niyyar fim din dashi baya gari kuma daukar da zasuyi suna bukatar ruwan sama. Shiyasa suka takura sai mun tafi acan na kwana. Kai jiya munyi fim da wuya. Don nasha dukan ruwa.... To indararo.... Don Allah alhajiji barshi yaje ya shirya yafito mu tafi inka biye tashi sai yayita zuba kenan daga nan har azahar. Kasan ba gajiya yake da magana ba.... Usman yace cikin fada. Na dube shi nayi masa gwalo... Sannan da gudu gudu na shige cikin gidan. . Bayan mintuna ashirin nafito nayi wanka na sanya kayana tsaf dani inka dauke zunzurutun tunanin dake raina. In banda na amsa musu tun jiya da ba zanje fim din ba milliyan biyar. . Mu tafi nace dashi cikin sauri na nufi sabuwar motata. Hilal mota ka sake ne? Alhajiji ya tambaya na san gatse yake son yi min ya dauka arota nayi domin duk fadin duniyar fim babu inda labari bai watsu ba cewa taurarona ya daina haske. Daman ai chanji zanyi shine yasa na saida wadancan nan da sati guda ma za'a kawo min marsandi daga kwatona. Alhajiji ya dubeni cikin kaduwa akwai alamun hassada karara a fuskarsa. Hakanan kuma na lura da cewa kamar dai na barshi cikin wasi wasin gaskiyar abinda nafada. Ganin ya kasa magana saina ce dash. Ina lauriyya? Fuskarsa ta washe nan da nan. Ai ka fini kusa da ita. . BIYAR 5 . Ina ganinta tsaye sa'ar dana nufo ofishin ta raba hannuwanta ajikin kofar tana ta hange hange ko shakka banayi ni lauriyya take hange taga ta inda zan bullo to amma har sa'ar danayi fakin da sabuwar honda akofar foshin Allah bai nuna mata ni ba domin atsammaninta akasa zata ganni na bullo. Nayiwa kaina murmushi sa'ar dana fara rufe gilashin tagogin motar duk yadda akayi masu karbar bashine cike suke jirana. Don na lura da yanayin fuskar lauriyya hankalinta atashe yake. Babu mamaki ma duk hange hange da take kokari take taga ta inda zan bullo tayi min inkiya na gudu batareda masu karbat bashin dake ciki sun sani ba. Na dubi bakar jakar dake ajiye akan kujerar motar. Kudin da kamfanin Sinad produtions ne suka biyani na fim din danayi musu aranar. Naira dubu talatin da biye ne cif cif. Fim din da muka dauka aranar ya burge duk ma'aikatan amfanin musamman ma alhajiji. Domin ya yaba da kwazona. Da wannan ne ma tasa sa'ar da aka kammala saiya kirani yace. Hilal akwai sauran kusan gurare hudu da zakayi mana sati mai zuwa amma zan biyaka kudinka yanzun nan baki daya. Godiya nake furodusa. Nace dashi. A'a ai ni nake da godiya domin Wallahi Hilal na dauka ka gama mutuwa domin tuni ake yawo da labarin wai tauraronka ya daina haske sai yanzu ne na lura da cewa ashe duk hassada ce. Ya danyi shiru... . TAKUN FARKO NA RIKICIN KENAN KU BIYO NAZIR [13:27, 1/27/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-20 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Tuni ake yawo da labarin wai tauraron ka ya daina haske sai yanzu ne na lura cewa ashe duk hassada ce. Ya danyi shiru na yan dakiku sannan ya ci gaba. Dubu ashirin da takwas mukayi da kai ko? Na gyara kai sai yace Toh ga dubu talatin da biyar nan saura kyauta ce ta musamman daga kamfanin sinad production domin baka taba yi mana fim ba sai yau ina kuma dada tabbatar maka in Allah ya yarda wannan fim din sai ya dada haskaka ka domin mu muna da labarai masu kyau sauran kuwa duk shirme ne dahaka ai suke so su kashe ka. Har na baro gurin alhajiji bai daina Yabona ba da zan baro gurin ma har kyautar shadda mai tsada yadi goma yayi min Don haka sa'ar dana gama rufe gilasan motar sai na dauki kudin da jakar yadin shaddar na nufi kofar ofishina. Lauriyya bata tashi ganina ba sai dana zo daf da ita sai tace cikin rada. Lahh ta Ina ka biyo? Na kalli motar ina murmushi acikin wannan motar nazo lauriyya ta waiga bayanta a tsorace bayan ta tabbata babu mai ganina daga cikin ofishin saita kifta min idanu akan na gudu Wanene aciki? Na tambaye ta a tausashe. Emeka ne tun safe yake nan har yafara fada yana cewa yau ko zai kwana nan sai ya same ka in kuwa bai ganka ba toh gobe da yan sanda zai zo lauriyya ta dada waigawa tana dubana. Mu shiga daga ciki kada ki damu ai yau a shirye nake da zuwansa hakan dana ce shiyasa lauriyya ta kalli jakar ledar dake hannuna nan da nan sainaga fuskarta ta washe cikin mutanen murmushi ta matso inda jakar take ta karbi jakankunan guda biyu daya ta kudi daya kuma ta shadda. Har naji dan dadi Wallahi Hilal. Tun dazu gabana ke ta faduwa Wallahi bana son naga kana ta guje guje akan bashi. Allah sarki lauriyya nace cikin zuciyata irin wannan kulawa tata ita take dada rura wutar begen ta cikin zuciyata. A da can ban dauketa a komai ba amma a Yan kwanakin nan dana shiga masifa lauriyya ba karamin tallafi bace agare ni. Tana gaba ina binta Abaya har muka shiga cikin ofishin. Hello Emeka barka da zuwa ya juyo firgigit kamar an tsikare shi da kibiya. Kada ka karya min kujera a banza da wacce kazo naji ance kusan kullum sai kazo nemana ko? Emeka ya Harareni. Ai kafi kowa sanin abunda yakawo ni tun yaushe ne alkawarin cikon kudin kaset din mu ya cika? Kasa sai kashe kudin mota Nakeyi a banza duk ribar ta tafi ga masu mashin da mota. Huta da nunfashin ka kada hauhawar jini ta hau ka a banza. Nace dashi ina murmushi Lauriyya ta ajiye kullin jakankunan daga can bayan teburina sannan ta fice cikin sauri ta koma can dakin karbar baki. Nawa ne cikon kudin naka? Emeka yabata rai dubu ashirin da biyar. Na bude baki cikin mamaki kai kace da man can bansan yawan kudin ba. Dubu ashirin da biyar? Ashe dai kudin naka Emeka da yawa. Ya Harare ni. Kaga Hilal ni kada ka bata min lokaci in banda lalacewar ka nawa ne dubu ashirin da biyar agurin ka. Na dube shi gamida girgiza kai. Sanin da kayi min yanzu abubuwa ne sai a hankali. Ina gama fadin haka saina sunkuya kasan teburina na zaro naira dubu goma sha biyar na Riga nasan teburin yakare Emeka bazai ga daga inda nake zaro kudin ba Nawa ne nan? Emeka ya Kalleni fuska a yatsine sa'ar daya ga kudin basu cika ba. Nawa ka gani? Dubu goma sha biyar. To ka godewa Allah daka sami wannan kayi min hakurin dubu goma sai bayan sati guda. Tsawon lokaci Emeka na nan zaune yayi jim kamar ruwa ya cinye shi can saiya nisa yace ba jiran sati guda ne aiki ba cika alkawarin ka Kada ka damu zama sami cikon kudin ka. A haka na lallaba shi muka rabu a zuciyata nace shashasha baisan ba a yanzu tsakanina da miloniya kalma daya ce tak kawai. . Bayan na raka Emeka saina dawo kan kujerata na zauna sannan sannu ahankali kamar a hoton majigi sai abubuwan da suka faru adaren jiya har zuwa asuba suka fara dawowa garai garai a faifan zuciyata. Fadila ta zame min ALAKAKAI. hakika ga dama ta sameni nace cikin zuciyata na farko dai idan na amince zan auri Fadila saina rabu da duk bashi da ake Bina saina zama gagara gasa acikin duk kamfanonin shirya Fina finan hausa. Na dubi hannun rigata sainaga har yafara kodewa sainayi tsaki fitaccen jarumi kamata yana bukatar kayan sawa akalla kala dari biyu a talauce. . Zan saya maka duk abin da kake bukata na harkar fim. Kalamansa suka Fado min a zuciya. To amma duk wannan da zarar na tuna da halayarta sai inji duk al'amarin Yafita daga raina hakika ina matukar son kudi a halin danake ciki a yanzu domin basussukan da ake Bina sun kusan miliyan guda to amma acan cikin zuciyata ni nasan auren fadila ba daidai bane na farko dai ba dole bane tace tana sona in kuma ma ta amince Dani ba itace irin uwar daya kyautatu na samarwa 'ya' yana ba domin ayanda ubanta ya bani labarin halin ta ko na aure ta zaiyi wuya in zata daina bin maza. A dacan kuma wani bangare na zuciyata nasan duk kwane kwanen da nake na abu daya ne hakika na kamu da son lauriyya tabbas in har zan auri wata mace a duniya toh lauriyya ya kamata na aura nace da kaina....... . NIMA YARIMA NACE KA HAKURA DA FADILA KA AURO LAURIYYA TALAUCI YACI GABA DA SUBURBUDAR KA. . NI KAM INA JAM'IYYAR FADILA DA BABANTA [13:28, 1/27/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-21 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Idan har zan auri mace a duniyar nan toh lauriyya ce nace da kaina. . To sai dai fa ga fadila ga miliyan biyar. Wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina acan wani bangare na ofishin agogon bango ya fara buga kararrawa karfe biyar da rabi na yamma. Zuciyata tagama shiga rudani abubuwa uku agabana. Lauriyya Miliyan biyar da fadila Biyu nafi son na mallaka daga ciki to Saidai kuma daya daga cikinsu yashiga tsakanina da guda daya tabbas in har Inason lauriyya to sai dai in hakura da miliyan biyar. In kuwa kudin nake so dole ne saina hada da Fadila. Allah kiyaye nace cikin zuciyata. A can wani bangare kuma wata zuciya sai
Chapter 11 · 0% Book details