Sashe 8
Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin duhun daren........... . *************** ************* *********** . INASON CIGABA NEPA SUN HANA SAIKU JIRA SU . ALAKAKAI-14 loading....... [20:57, 1/21/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-14 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Zakayi ihu ma sai agaba shege barawo. Me ka sato acikin akwatin? Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren.... . ********* *********** ******** . Adaidai lokacin dana sulalewa zan fadi acikin cabalin ruwan ne sai wani busashshen hannu mai kamar iccen makera ya cafi kwalata ya dagoni sama da karfin tsiya ya girgizani. Me ka sato aciki Barawo? Aka sake tambayata akaro na biyu sannan sai busashshen hannun ya damki makwogorona. Idan baka fadi abinda ke cikin akwatin nan ba kasheka zanyi shege azzalumi kudin wa ka sato? Wallahi ba kudi bane.. Nace dashi cikin karaji. Uwarka ce to aciki? Shege Allah ya tona asirinka kananan barayin unguwa daman jira kakeyi afara ruwa saika biyo dare ka dauki wannan ka zari wancan kamar mayen karfe ko? Haryanzu ba'a daina tsuga uban ruwan saman ba na hadiye yawu da kyar ba karamin riko yayiwa makoshina ba dakyar nake numfashi gashi ya daga hancina sama ruwa sai shiga yakeyi kamar bututu. Busashshen hannun ya dada girgiza ni zuciyata sai harbawa takeyi Tam Tam kamar tamaula tsakanin hakarkarina akwatin kankame akirjina na san idan na sake ya bude akwatin kashina ya bude. Daureka zanyi yace dani yau Allah ya toni asirinka bazan buda akwatin daka sato ba amma da zarar gari ya karasa wayewa zan mika ka ga hukuma. Mutumin ya tura ni riki riki da akwatin ahannuna muka nufi katon gidan attajirin nan mai katanga dauke da fitilun lantarki burjuk kamar hasken rana. Mutumin yaci gaba da jana kamar mushe rabi ina tafiya rabi kuma kafata na jan kasa kamar kafar gawa. Wani lokacin idan aka kwantsama aradu mai karfin gaske sai mutumin ya dan dakata da jana yace. Shege dama ta fado maka azzalumi. Nayi mamakin ko wanene azzalumin tsakanina dashi. Bayan wasu yan tsirarrun mintuna muka kawo ga kofar gidan attajirin nan. Na dubi dankareren gidan kana na dubi yan mitsi mitsin kwayoyin ruwan dake ta zubowa bila adadin daga sararin Subhanahu Kamar hazo lokaci guda kuma na juyo akaro na farko nayiwa mutumin kyakkyawan kallo. Banyi kuskuren fasaltashi cikin zuciyata ba. Domin kamar dai yadda nayi tunaninsa haka nan yake saima abinda ya dadu kato, baki, jajayen idanu, fankaceciyar kafada, kamar kofar shagon kasuwa. Abin dayafi bani mamaki ga halittarsa shine duk da girman jikin nan nasa kansa dan kankanine haka kuma fuskarsa tsukakkiya ce fatar bakin siririya kama an tsaga wanda da tsinin wuka. Koda ya dada fizgata muka dada matsawa daf da kofar gidan sai tangamemiyar kofar ta bude wasu dogayen mutane suka fara fitowa daya bayan daya har suka zama su uku. Basu damu da ruwan da ake kwararawa ba. Mutanen uku duk Buzaye ne sirara masu dan rakeken wuya kamar kasan almakashi ka dauke. Kowannensu dauke da dakon katon rawani kamar mushen tunkiya rike da takobi tsirara. Wa Allah kuma ya hada ka dashi MAMUDA? Daya daga cikin masu gadin ya tambayi katon mutumin dake tike da wuyan rigata. Irin yan kananan barayin unguwannin nan ne dake damun unguwa da yan sace sace yanzu ma dubunsa ce ta cika na zagaya cikin ciyayin can sainaji DUNA yana haushi nakai masa agaji nakamo wannan karamin marar kunyar. Yana gama fadin haka saiya hankadani gaban buzayen da karfi na fadi ricaaa agabansu. . Wannan akwatin fa dake rungume akirjinsa? Buzun maigadin ya tambaya ban budata ba babu ruwana da abinda ya sato ku barshi kawai idan gari ya waye saimu mika shi ga jami'an tsaro domin irin kananan barayin nan annoba ce ga al'umma dan irin su ne idan suka rika sai su zama yan fashi da makai. Yasa kafa ya daki Duwawuna da karfin gaske na kwalla kara. Au dan dan wannan ma? Ai somin tabi ne kawai na baka ladan kamu ne saima gobe idan kaje hannun yan sanda kayi mai dalili Ya fashe da dariyar mugunta. Ku jefa min shi cikin dakin injin bada wuta yace da buzayen. To! Suka amsa baki daya sannan kowa daga cikinsu ya kama inda yafi rainawa ajikina sukayi sama dani kamar gadon kara suka nufi cikin gidan dani. Kada ma ku damu kanku da sai kun daure shi kudai ku kulle shi kawai aciki karamin barawo ne babu abinda zai iya yi. Suka karasa dani kofar wani dan daki dake manne ajikin bangon gabas na farfajiyar gidan dan dakin kusan duk akere yake da shuke shuken furannin alfarma haka nan duk farfajiyar gidan. Nayi bakin ciki domin duk da mummunan halin danake ciki basu barni na kashe kwarkwatan idanuna ba. Muna isa kofar dakin sai suka ajiyeni akasa biyu daga cikinsu suka rikeni yayinda dayan ya bude dakin jannaretan nan da nan karar injin dake cikin dakin gamida hayaki suka gauraye gurin. Anan zaka kwana in kuma kaso ma to kana iya sace injin gaba daya duk ribar kafa ce wai giwa ta taka kwado. Suka jefani cikin dakin kaina ya bugi jikin injin. Sannan na mirgina gefe guda ina murkususu. Masu gadin suka mako kofar garam!!! Sannan naji karar kwadon sun kulle dakin. . Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda karajin inji sannan kuma idanuna kamar zasu fito waje saboda hayakin injin dake shigo min. To amma fa duk wannan bai sa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba [10:23, 1/22/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-15 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda Karar injin sannan kuma idanuna kamar su fito waje saboda hayaƙi injin dake shigo min. Toh amma fa duk da irin wannan wahala baisa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba na yunkura Dakyar sannan na nufi kofar kofar dan karamin dakin injin bada wutar lantarkin adaf da kofar dakin akwai wasu yan kananan tagogi ajere reras guda shida don haka ina Karasawa ga tagogin Saia tura hannuna ta cikin kofar daya daga cikin yan kananan tagogin hakan danayi shi ya bani damar shakar tsaftatacciyar iska sannan kuma sassanyar iskar ruwa ya bugi fuskata nan da nan naji na dan fara dawowa hayyacina akusa da kofar dakin daga hannun hagu akwai wai katon duro na mai. Na matsa kusa da durom din na ajiye akwatin akai na jingina dashi sannan kuma wani lokaci guda fuskata na cikin yar Jafar tagar ina shakar iskar tsaftatacciyar iskar ruwan Saman ahaka ko barcin gajiya ya dauke ni. Bansan iya sa'o'in dana share ina barci ba Nidai kwatsam ba zato ba tsammani sai ji na nayi nadaku da kasa. Sannan naji wani abu ya Fado min awannan sa'ar na tashi firgigit cikin tsoro sannan ne to na fuskanci ashe barci ne ya daukeni a tsaye harna ture durom jakar dana ajiye da kuma akwati. Na tashi tsaye da kyar jikina na rawa ga mamakina sai Naji gidan yayi tsit wannan shi ya tabbatar min da cewa an Dade da dauke ruwan saman acan wani bangare kuma na Unguwar nasu wani ladan mai zakin muryar gaske yana kwada kiran sallah asuba tayi nace a zuciyata kashina kuma ya bushe kenan. Na sake cewa a zuciyata Daman nasan da gari ya waye marasa imanin masu gadin nan zasu Mika ni hannun yan sanda shin anya kuwa haka zata yiwu? Yafa kamata ka motsa ko zaka samu hanyar tsira wata zuciya tace dani. Na nufi kofar dakin ahankali kafata kamar zata balle saboda ciwo nasa hannuna a jikin kofar na dan jijjigata sannan ne to naga kofar dakin......... Karshen abubuwan........ Ne. . Karfe da gilashi kuma gilashin dake daf da inda nake masakalin dan makullin yake a daya sakon. Nan da nan zuciyata tafara harbawa inama ace zan iya murde dan makullin na ce da kaina. Namika hannu naji hannun ya taba kwadon dakin kamar wasa sai kawai naji kwadon ga mamakina ya bude gumi yafara sarara agadon bayana sannan ne to wata zuciyar tace dani shashasha mai gadin bai balle kwadon ya shiga daidai ba. Nan da nan na murde kwadon na tura shi sama sai ya fadi can kasa Tim. Jikina kamar mazari na rawa na dauki akwatina sannan na tura kofar ahankali sai ta dan bude nayi shiru ina saurare ko zanji motsi shiru babu motsin komai sainaga hanya yakin bishiyoyin gidan da iska ke kadawa banyi mamakin jin shirun ba domin nasan hankalin masu gadin a kwance yake tunda dai a tunanin su ina nan a kulle abu na farko da ya fara zuwa zuciyata shine hanyar da zan bi na tsere to Saidai kuma tuni na tabbatarwa da kaina cewa bashi yiwuwa na tsere ta kofar da suka shigo dani idan nayi gangancin bi ta kofar to kamar na tura kaina ga halaka ne da gangan. . Tsakanina da inda dakin yake dakuma tangamemiyar kofar gidan yake akwai tazara don haka sai wata zuciya tace dani tunda dai kofar bata biyuwa me zai hana ka lallaba ta cikin duhun shuke shuken da suka kare dakin ka zagaya ta baya? Nan da nan sai na koma ina mai amincewa da shawarar zuciyata tunanin daya fara zuwa min shine na zagaya bayan gidan saina haura katangar indira cikin tsohon kangon dake makwabtaka da gidan wanda Daman tun farko anan nayi niyyar jefar da akwatin mai JARIRIN. Na tura kofar dakin ahankali sannan na fito waje. Sannan ahankali ina bin lungu lungu sako sako dake cikin shuke shuken har na kawo ga ginin gidan adaidai lokacin to naga yar siririyar hanyar data bi ta bayan ginin dakunan gidan har zuwa katangar arewa wacce itace ke makwabtaka da gidan. Fasalin ginin dakunan gidan irin Fasalin nan ne da zaka iya ginin dakunan su kadai ne a tsakiyar gidan batareda an jingina koda gini daya da katanga ba wannan shi ya baiwa rufanin damar yin yado ajikin katangar hakan nan kuma yan dukur dukur fitilun alfarmar suma suka kai kusurwar katangar kudu ta gidan abin gwanin ban sha'awa me yiwuwa hakan ce tasa akayi ginin tsakiyar gidan batareda an jingina shi da koda katanga daya ba. . Na lallaba ahankali kirjina na Dakan shida shida na bi yar siririyar katangar ta tsakanin