← Book details Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cewa takeyi dani kai shashashan banza saikace ba wayayye ba ka manta kawai da lauriyya ka auri fadila ko ka rabu da talauci da wulakancin Abokan harkar ka na shirin fim yanzu in banda shirmen ka har akwai wani abun kunya da aibu da miliyan biyar bazata iya lullubewa ba? Hilal..... Naji muryar lauriyya ta daki dodon kunnena na dago kaina firgigit ina shafar fuskata da hannu. Tunanin me kake yi? Ta tambaya lokaci guda kuma ta matsa kusa dani ta zauna akan teburin dake gaban kujerar danake zaune kadan ya rage gwiwarta ta gogi tawa. Akwai alamun damuwa karara a fuskar ta. Uhm.. Bawani tunani nake ba gajiya kawai nayi lauriyya ta zuba min idanu na tsawon lokaci na lura karyar dana shirya bata samu matsugunni ba. Mintunan ka ashirin fa kenan kana zaune cikin ofishin nan kai kadai kuma kace ba tunani kake ba? Sai fa dana kira sunan ka har sau hudu kafin kaji ni... Ban amsa mata ba dan banida abin cewa Gaskiyar ta tabbas tunani nake. Lauriyya ta ci gaba da wasa da Biron dake hannun ta tana kida dashi a tausashe akan teburin. Da wata shawara nazo da ita Hilal... Kokuma ince neman alfarma. Nan da nan na juya na kalle ta cikin mamaki sai a lokacin ne na lura ashe akwai jaka rataye a kafadarta. Ina zaki tafi ne naga kin dauko jaka? Lauriyya ta girgiza kai. Babu inda zani muka sake yin shiru. Ni Nafara magana. Wacce shawara ce.... Kokuma ince wacce alfarma kike nema? Na tambaye ta zuciyata na harbawa abin na da rudarwa. Yan sa'o'i kadan fa kenan da attajirin ya nemi alfarmar na Auri 'yarsa to ko itama alfarmar na aure ta zata nema? . Hilal nasan ana binka basusuka dayawa wadanda na tabbata bazaka iya biya ba a kwana kusa. Lauriyya ta dago kanta ta dube ni sainaga kwalla ta taru cikin idanun ta. SHI Yasa nazo neman alfarma. Alfarmar itace zanyi Maka kyauta ta musamman da wani abu wanda zai taimaka maka ka rage mafi yawan bashi da ake binka. Idan na baka so nake ka karɓa kada ka juya hannun kyauta baya shine kawai alfarmar..... Wani abu mai kamar gare gare yafara zaryar cikin kwakwalwata. Me kike son ki bani? Na tambaye ta a iya tunanina lauriyya bata da wani abu da zai iya biyan koda rabin bashin da ake Bina. Jikinta na rawa ta sauke yar madaidaiciyar jakar dake makale a kafadarta ta dorata akan bencin dake gabana sannan saita daga jakar sama ta zazzage abubuwan dake ciki akan teburin. Alokacin sa al'amarin ke faruwa duhu ya gauraye dakin domin tuni har an fara kiran Sallar magariba kuma bamu kunna kwan lantarkin dake cikin ofishin ba. Amma duk da hakanan sai kyalkyalin abubuwan ya haskake dakin sarkokine yan kunnaye da sauran tarkacen kayan karau na kwalliyar mata duk dayake bansan darajar su ba amma nasan sunada tsadar gaske bakina na rawa na girgiza kai. Lauriyya.... Baza ta yiwu ba bazan iya raba ki da kayanki ba... Kuma ina kika same su ban taba ganinsu ajikin ki ba dan abin da kike samu kuwa a kamfanin nan bai isa ko iya tarawa kike balle har ya sayi wannan ba. Lauriyya ta matso gareni ta dafa kafadata tace. Kayiwa Allah Hilal kayiwa Annabi ka karɓa tunda nake ban taba neman alfarma agurinka ba sai wannan idan kaki karɓa ka gama bata min rai ka konan zuciya. Toh amma dai lauriyya bai kyautu ba ace in har ni ban yi miki ba ke ki..... Ta katse ni ta hanyar daga hannayen ta. Kada ma kafara wannan zancen Hilal tunda nazo garin nan wake wahala dani in ba kai ba Kaine uwata Kaine ubana Kaine abin kaunata ka kadai ne ka iya sani dariya har cikin zuciyata. Ta danyi shiru tana kokarin share hawaye. Farin cikin ka shine farin ciki na tunda nazo garin nan baka taba sanin tarihina ba baka kuma takura min saina fada maka sirrina ba amma kake taimaka min iya karfin ka yau juyi nane na taimake ka don Allah kwashe su Hilal ko a kasuwar barayi ka sayar dasu akalla zasu kai dubu dari shida. Ta dafa hannuna ta kankame. Kaji Hilal don Allah kwashe su Narasa abin da zance da ita. Wata zuciyar nacewa dani kada ka yarda ta rudeka dubu dari shida basu kai miliyan biyar ba. Karkari dai su biya ma bashin amma zata kare babu komai a hannun ka Nayi fatali da kururuwar zuciyar. Hakika abunda lauriyya tayi min bazan taba mantawa da ita ba har iya rayuwata nasan cewa a yadda take da Matsalar ta sa komai tabani kadarar ta cancak ta makudan kudi zata iya bani naira miliyan dari inda ita tana da shi. Hilal... Hilal kayi magana mana ka zura min idanu in kuma banida matsayin da zan nemi alfarma kayi min saika fada na kwashe kayana na tafi. Kada kice haka lauriyya ki kuma daina cewa alfarma kike nema ai nine kika yiwa alfarmar bakisan wani abu ba lauriyya nace da ita ina duban ta ido da ido. DUK duniya a yanzu banida wadda tafiki in babu ke lauriyya bansan inda zan sa kaina ba kece garkuwa ta mai tallafa min na yarda zan karɓa amma ki ajiye min su agurin ki daga nan zuwa sati guda kawai. Lauriyya ta dada kankame hannuna saita fashe da wani tattausan KUKA. Ban taba farin ciki irin na yau ba Hilal kuma..... Kwankwasa kofar da aka yi shine ya katseta nan da nan ta Mike tsaye cikin sauri ta share hawayen dake idanun ta muka dubi kofar lokaci guda aka dada Kwankwasawa. Bari in je in gano tace dani a tausashe. Na gyada mata kai sannan nayi sauri na boye sauran kudin dubu ashirin da suka rage me yiwuwa wani mai karbar bashin ne nace cikin Raina. Bata dade da fita ba sai ga lauriyya ta dawo ta tsaya gabana ta rike tsantsa akwai alamun damuwa a fuskarta. Wata ce wai take son ganin Ka nayi ajiyar zuciya nasan aduk masu Bina bashi babu mace ko daya. Kice da ita ta shigo nace da ita... Ina Nan zaune sai Naji motsi ina daga kaina sainagan ta tsaye agabana. Nan da nan dakin ya hade da kamshi doguwa ce sanye da doguwar riga ruwan Hoda kanta lullube dan kyalle irin launin rigar. Baba iya ganin fuskar ta Sosai domin haryanzu ban kunna kwan lantarkin dad ofishin ba. Sannun ki da zuwa malama ga mamakina sainaga ta matso ta zauna a bakin teburina daidai da inda Lauriyya ta zauna. A'a MALAMA ga kujera nan koma can ki zauna mana ta fashe da dariya cikin wata zazzakar murya. Hilal Wallahi kabani mamaki daka kasa gane ni. Ko na kara kyau ne? Naji gabana ya fadi rasss nan da nan sai ta girgiza kanta lullubin dake kanta yafado kan kafadarta siraran gashin ta suka bayyana suna sheki. Me yiwuwa kafi gane ni ahaka ko haryanzu baka Gane ni ba JARUMIN JARUMAI. Ta sake fashewa da dariya. NICE FA FADILA...... . SHIDA 6 Loading......... . ALAKAKAI-22 Loading....... . KAI ANYA KUWA NIMA BA JAM'IYAR LAURIYYA ZAN KOMA BA [13:30, 1/27/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-22 . (m)Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Me yiwuwa kafi ganeni ahaka ko haryanzu baka ganeni ba JARUNIN JARUMAI. Ta sake fashewa da dariya. NICE FA FADILA.... . SHIDA 6 . Fadila nakira sunan ta a sanyaye ko shakka babu ta sani bala'in kaduwa domin ban taba tsammanin zan sake ganin ta kwana kusa ba Hilal kenan manyan gari ta tashi daga kan teburin ta nufi kujerar dake fuskantar teburina ta zauna. Babu wuta a ofishin ne ko kafi son zama acikin duhu ne? Na muskuta akan kujerar na fara farfadowa daga cikin kaduwar danayi. Akwai..... Wuta ban kunna bane ga makunnar nan a bayan ki Fadila ta Mike tsaye ta lalubi makunnar lantarkin ta kunna dakin ya gauraye da haske numfashina ya dauke yawun bakina ya kafe. Nashiga uku nace cikin Zuciyata ashe kyakkyawace ta gaske kamar ta karanta abin da ke zuciyata saita kashe min idanu tace. BAKA dauka na kai haka ba ko? Kallon tsoro kayi min jiya ta matso kusa da bakin teburin tana tafiya tana girgiza jikinta da gangan kusan ko ina a jikinta rawa yake ta dafa kan teburin da hamnayen ta na dubi yan yatsunta sirara ne farare sol babu wani alamar tabo ko kwarzane atare dasu kamar jikin maciji. Tsawon lokaci tana tsaye akaina ta lullube ni da kamshin turare da man dake jikinta bansan sa'ar data dauke hannaye ta daga kan teburin ta Mike tsaye ba. Hilal yaya naga kayi shiru ko bakaji dadin zuwana bane? Nayi kokarin na tattare hankalina guri guda nace. Da wacce yau kika zo kuma? Wata sabuwar kyautar kika kawo Min? Fadila ta bata rai KA cika rikon magana wannan zancen ya fita daga bakin ka Hilal. Abinda ya wuce ya riga ya wuce jariri dai tuni an gama binne shi an riga an binne shi tun da safe. Tayi shiru tana tsuke baki muka sake yin shiru. Amma.... Dai kinsan ai abunda kikayi baki kyauta ba ko? Ko kina ganin daidai ne Abinda kikayi? Fadila ta dauke kai gefe guda. Da zamu bar zancen nan dai da zaifi. Don me yasa kika ce haka? Saboda tone tone bashida dadi. Na Mike tsaye daga kan kujerar na jingina da bang. Fadila Gaskiya al'amarin ki sun dame ni kin.... Ta katse ni. Hilal Inason ka sani cewa duk abin da nayi adaren jiya nayi ne saboda mahaifina in baka sani ba kasani duk da cewa kuwa mahaifiyata tafi kaunata da shagwaba ni duk duniya babu wanda nake kauna kamar sa. A zuciyata nace duk yadda akayi yarinyar nan tanada tabin hankali babu mamaki Hakan ne yasa ake kokarin bani auren ta. Nasan Abinda kake tunani banida hankali ko? Ta dubeni. Na girgiza kai. Kada ka boye min jarumi Hilal naga alamu a idanunka amma yana da kyau ka yi tambaya kafin ka yanke hukunci. Toh..... Amma saiki kashe jariri kice wai saboda kaunar mahaifin ki kikayi? Ta kada min idanu tace. ....... Nan da wata bakwai mahaifina zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna babu abin da nake buri irin ace yau mahaifina ne
Chapter 12 · 0% Book details