Sashe 13
Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwamnan garin nan. Tayi shiru tana rangaji agabana kamar bishiya. Ina Fatan yanzu ka fara fahimtar hoton da nake kokarin zana ma? Kaga Hilal ciki dai nariga nayi Munso mu zubar da cikin nida mahaifiyata tun yana ƙarami mahaifina ya hana lokacin Dana haihu sainaga in har na bari dan ya girma nagama kunyata mahaifina kuma idan zancen yafito Abokan hamayyar siyasar sa na iya yin amfani da damar su bata mahaifina. Amma kuma bakya ganin yanzun ma bata sauya sani ba tunda dai ai jama'a da dama sun sani kinada cikin shege? Jama'a kamar su wa? Ta tambaye ni gamida daga girar idanunta sama. In banda kai dakuma likitan mu da ya auna ni ya tabbatar ina da cikin duk duniya babu wanda yasan inada cikin kai ko wanda yayi min cikin baisan inada shi ba domin tin yana dan wata daya aka hanani fita ko ina aka sa masu gadina har sai dana haife dan. Kawaye na da Abokan Arziki idan sun zo ne mana sai ace dasu bana Kasar. . Nayi shiru ina sauraron shashashan zancen ga mamakina sianaji duk da kyawunta nafara tsanarta ko kadan bata da kunya. Ina ganin idan babu sauran wani abu da zaki fada ni zan fita nayi sallah kinga har an idar sa sallah a masallaci nafara yar tafiya a cikin ofishin. Au harma korata kake yi? Ta bata fuska. Babu zancen kora kora in kina iyawa jirani nayi sallah sai muci gaba da hirar daga nan zuwa asuba. Muga abunda Allah zaiyi nasaki Murmushi nafara Jin dadin badakalar. Wai dan Allah da gaske kike yi baki kawo min kyautar komai ba? Ta kawo min duka cikin wasa na kauce. Ya ishe ka haka kaga bana so. Ta juya ta fara tafiya akwai alamun farin ciki a fuskar ta. Muje to ka rakani. Muka ratsa ta cikin dakin karbar baki. Ban iya yarda na kalli inda lauriyya ke zaune ba. Toh amma na lura zaune take ta kifa kanta akan teburin dake gabanta. Nayi tsammanin zata biyo bayan mu da man Ga al'ada duk bakon da ya zo tare da ita muke raka shi amma Sam Sam bata biyo mu ba tun kafin mu Gama fita na hangi katuwar marsandin tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya haskaka kofar ofishin...... . KAI NIFA NA RIKICE NA RASA WACCE ZAN GOYA WA BAYA LAURIYYA KO FADILA ???? [21:03, 1/30/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-23 . (m) Nazir Adam Salih Baban Ahmad Da Adam . (c) Yarima Gangariya . Tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya haskake kofar ofishina. . Muka karasa gindin motar babu magana muna tafe kafada da kafada da muka isa gindin motar ta fuskanceni yaushe zaka zo? Tambayar tayi matukar girgizani. Ina kike nufi? Fadila ta dafe kirji cikin razana ta harareni a fusace. Au baka san zancen ba? Wane zance? Fadila ta girgiza kai tace shikenan tunda baka sani ba daman babane yace nazo na sameka amma tunda kace baka san komai ba shikenan. Tana gama fadi saita juya cikin fushi ta shige motar. Shashashan banza sakarai. Wata zuciya tafara yi min kururuwa idan ka bari ta tafi baka lallasheta ba kamar kayi sallama ne da miliyan biyar. Mafarkinka duk ya zama shirme. Fadila Fadila na kira sunanta cikin gaggawa ta sauke gilashin tagar motar na sunkuya nace. Kiyi hakuri dan Allah Fadila... Idan kin kula duk ba'a ahankalina nake ba a rude nake... Fadila ta dubeni ta tabe baki sannan tayi tsaki tace. Yi sauri ka koma gurinta tana can tana kukan kishi kada ta mutu... Gabana yayi das das. Wa kenane kike nufi? Na tambaya baki bude. Kafini saninta... Wancan baiwar taka dake jiranka a ofis. Tasawa motarta giya ta firzgeta aguje tabarni anan tsaye ina hangen kurarta. SAI WATA RANA MILIYAN BIYAR. Nace da kaina kamar na fashe da kuka koda na nufi ofishina sainaji wani zazzafan zazzabi yana neman rufeni. . *********** ****** ********** . Har sa'ar dana dawo dakin karbar bakin lauriyya tana nan kamar yadda nabarta kanta kife akan teburina na tsaya akanta. Lauriyya na kira sunanta akwai alamar rawa a muryata. Ta dago kai ta kalleni da wani fatalwan murmushi. Ba sai an fada ba duk wanda ya kalli idanunta yasan taci uban kuka duk kuwa da matukar kokarin datayi wajen share hawaye. Har ta tafi? Ta tambayeni hannunta rungume a kirjinta. Ta.... Tafi na fadi muryata na sarkewa. Mukayi shiru babu wanda ya sake cewa kala har aka kira sallar isha. Sai lauriyya ta mike ta sakala jakarta akafada. Hilal zan tafi gida... Na danyi shiru na farko saikuma nace Gida? Haka da wurwuri... Ta danyi tsaki sai gabana yafadi tunda nake da ita bata tabayin tsaki a gabana ba. Banajin dadi ne... Shiyasa nake son tafiya yau da wuri muka dan sake shiru na tsawon lokaci. Dan dakata to ina da sauran magana dake.. Ta hade fuska. Maganar me kuma zakayi min na dauka mun gama komai tun dazu? Ga kayan ai acikin jakata. Ta nuna jakar da hannunta. Duk lokacin daka shirya saika karba in kuma kana so ma yanzu sainaba ajiye ce agurina. Akwai sauran magana lauriyya... A ina kika samosu? Naji ta rike numfashi cikin kaduwa. Hilal me kake nufi da a ina na samo su kana nufin kace ni barauniya ce? Dan girman Allah kada ki bata zancen nan lauriyya ni bahaka nake nufi ba. Ki tuna fa kyauta zakiyimin da kararki ta makudan kudi a iya sanina kuma ban taba ganinki dasu ba kinga kuwa ashe banida laifi danna tambaya. Ta sunkuyar dakai cikin takaici. Tambayar ta kona mata rai ta daga kai. Tunda ka dage saika san inda na samesu bari yo na fada ma MIJINA NE ya saya min su. Mijinki? Ta gyada kai. Kwarai kuwa baka san na taba aure ba kafin nazo nan garin ba? Nayi ajiyar zuciya. Ina fatan yanzu ka gamsu. Lauriyya tace sannan ta matso daf dani kusa dani har takai ina iya jinhucinta akan fuskata. ITACE TA BATA MAKA RAI ? Na kalleta a rude. Wa..wa kenan kike nufi? Lauriyya ta dafa kafadata tace. Nasan daman kafi karfina Hilal na dade ina kwana ina tashi da fargabar cewa watarana sai anzo har ofishin nan an kwace min kai! Gabana yafadi nayi sauri na dauke hannunta daga kan kafadata. Lauriyya nataba fada miki kuwa wata kalma kwaya daya? Wacce kalma ce wannan? Ga mamakina sai naji ina mai kunyar hada idanu da ita. Adacan Lauriyya ban dauki amatsayin komai ba fiyeda kawai sakatariya na. Nayi sa'a danaga ta kura min idanu kamar zata hadiyeni. Yau lauriyya na wayi gari duk fadin duniya babu wata 'ya mace datafiki agurina. Lauriyya ta dada matsowa daf dani. Na Gode Allah Hilal tun ranar dana dora idanuna akanka nake kaunarka. Zan baki wani labari lauriyya ki saurareni da kunnen basira lauriyya ta dubeni dakyau. Labarin me kuma? Nakama hannunta muka wuce cikin ofishina. Wannan shine karo na farko dana taaba yi mata haka. Na zaunar da lauriyya akusa dani. Lauriyya jiya da daddare wasu al'amura masu kama da shirin fim sun faru akaina. Abubuwan na da matukar rikirtarwa to ahaka dai ni gama yanke shawara azcuiayata cewa ni dai KE NA ZABA LAURIYYA. Dan Amina Muhammadu. Lauriyya tace tana tafa hannu. Ban fahimce ka ba hilal..... Me kake fadi ne kace ni ka zaba ban gane ba. Me yiwuwa idan nabaki labarin ki fahimce ni ke dai saurara da kyau. . Nafara zubo mata labarin al'amarun kyautar jaririn da akayi min tun daga farko har zuwa kan zuwan fadila ofis. Karfe tara saura kwata nagama bata labarin. Lauriyya tayi shiru bata ko motsi kamar ruwa ya cinyeta ga mamakina akaro na farko sainaji da gama fada mata labarin damuwa zuciyata ta ragu. Lauriyya ta mike tsaye tabar kusa dani sannan tafara safa da marwa.... [06:34, 1/31/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-24 . (m)Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Lauriyya ta Mike tsaye tabar kusa dani sannan saita fara safa da marwa acikin ofishin akwai wani yanayi dake fuskanta daya hanani na katse mata hanzari don haka sainayi zamana ina jiran naji ta inda zata bullo inada kwarin gwiwar cewa indai har akwai mafita to lauriyya ce zata kawota na yarda da kwakwalwarta akan hakan. . Hilal! Nayi firgigit sa'ar danaji ta kira sunana. Mecece shawarar Ki akai. Lauriyya ta dawo kusa dani ta zauna sannan tace Zancen gaskiya Hilal indai kabar miliyan biyar ta wuce ka kayi shashanci. Na zabura cikin kaduwa. Me kike nufi? Lauriyya tayi dariya miliyan biyar tafi karfin wasa Hilal Amatsayina na mai kaunarka bazan so ka rasa naira miliyan biyar saboda ni ba. Tunanina ya kure na rasa abin da zance da ita. Ni shawara ta ta Hilal kaje ka aure ta. Lauriyya meke damunki ne ta girgiza kai. Lafiya ta Kalau babu abin da ke damuna ni har kullum babu abin da ke faranta min rai irin cigaban ka Da miliyan biyar kana iya wa duk Abokan hamayyar nisa. Lauriyya kibar zancen nan tuni nagama fada miki in har akwai wacce zan aura yanzu a duniya to kece. Idan kuwa na Auri fadila bansan da idon zan Kalle ki ba ta daga kai muka hada idanu tace. Ko? Kwarai kuwa na Mike tsaye. Ko sallah banyi ba yakamata naje nayi sallah lauriyya ta biyo ni Abaya. Kayi tunani Hilal tunda dai sati daya suka baka amma ni ina ganin gara ka aure ta Hilal. Ban juyo na kalleta ba sa'ar da take maganar domin na lura ita kanta akwai wani sirri datake kokarin boyewa daga gareni. Wata zuciyar ta ci gaba da yi min kururuwa. Duk kabi ka zama wawa Hilal haka kawai kabari matan zamani suna neman su zauta ka. Daya kasan yadda take dayar kuwa baka ma san koda tarihin taba. Zan tafi gida Hilal sai goben lauriyya tace. Mamakin abin da yasa ta firgicewa haka take sauri sauri ta tafi gida. Toh shikenan sai goben kenan. Ahaka muka rabu da lauriyya ta tsallake bakin titi tana sauri sauri na bita da kallo cikin mamaki meke faruwa ne? Yanzun nan fa take nuna tsananin kishin ta a gareni take nuna cewa duk duniya ni take kauna lokaci guda kuma tana cewa naje na Auri fadila... Tabbas akwai wani abu