← Book details Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 52

PART 1

Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,
ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
I want comments not stickers
Comments dinku
shine kwarin gwiwata
_My first novel_
Haka ta tsaya daga inda take ta dinga caccaka masa maganganu son ranta maganganu masu ciwo ciki harda Kalmar dayafi tsana Mara tarbiyya sabida tasan baze iya cinmata ba
"Inda zuciya kadena shaye shaye kazama mutumin kirki kacigaba da abota da yayana in ba zuciya kuma kacigaba da zuwa kana like masa cingam ko kuma ince
Salansa sarkin hayaki ""
Ta juya takoma cikin Gida abinta kaman batayi komai ba
Maama ta tarar a palour tana tsifa
"Maama kawo in tayaki naga tsifar dayawa "
"To karbi kibiyar"
Hmm yarinyar nan akwai shiga rai ba ruwanta dukda tasan abinda ke tsakanina da mahaifiyarta amma ko a fuskarta ban taba ganiba,
inma dai salon wani makircinne duk zan iya daku d'a na ne dai ba a isa a hada min zuri a da wadda take da raunin nasaba ba, tayi wannan zancen a zuciyarta.
Shikam tsayawa yai cak kaman an dasa shi, yama rasa wani mataki ze dauka, fasa zuwa gurin Jawwad yayi ya koma gida ya shige dakinsa, ya dinga tuttulawa cikinsa giya seda yayi mankas sannan ya zube a gurin yana bacci.
"Nana gaskiya abinda Yar uwarki tamin ya mugun bata min rai, ya dace tafadamin haka agabana taci zarafin Dan uwana, wallahi taci albarkacinki dasena shukamata rashin mutunci wallahi"
Itakuma tsayawa zatayi tana kallonki ba bakisan wannan uwarkice a fitsara ba kina ganinta haka shi kansa uban gayyar ina tsoron randa ze danketa (Jalal)Nana tayi maganar a zuciyarta a fili kuma Se cewa tayi
"Nasani Ilham bata kyauta ba amma zanmata magana haka halinta yake bata boye abu a ranta komene ne zata fada a gabanka amma kiyi hakuri insha Allah hakan baze kuma faruwa ba"
"Kinga ni tafiya zanyi bansamu biyan bukatana sema karamin takaici da kukayi"
"Naface kiyi hakuri Dan Allah ki gaida mommy"
Banza tayi mata tai tafiyarta
a palour taga Jalila nayiwa Maama tsifa harara ta wurgawa Jalila
amma me ita seta maida mata da murmushi
"Kigaida Gida sister Ilham agaida mummy da yayanmu" tafada dauke da murmushi a fuskarta
Maama CE
"Ilham kicewa mummynku in ankawo lesunan tamin magana zan turosu su zaba"
"To zangaya mata"
shine abinda ta iya fada saboda Jalila takawota iya wuya.
Tana zuwa Gida dakinta ta wuce ta nemi guri ta kwanta maganganu Jalila suka shiga dawo mata
{"Sedai in akwai wani sirri da kike
boyewa Wanda bakowa yasani ba"!!}
To ya akayi tasani, taga a iya tunaninta babu Wanda ta taba wannan zancen dashi balle ya gayawa Jalila
To ya akayi tagane akwai wani abu a ranta haka taita tunane
Har bacci yayi awon gaba da ita
Se banyan
isha'i sannan giyar
da yasaha tasake shi ya farka daga nannauyan baccin da yayi, ji.yayi kansa yayi mugun nauyi kaman ba a jikinsa yake ba haka ya tashi yana rarraba hanya ya shiga toilet yayo wanka tare da alwala
Ya fito palour ya shimfida sallaya yayi azhar yayi la'asar ya dauke sallayar
(Nikam nace magariba da ishan fa?)
Cikin gida ya shiga ya tarar mummy na waya, ya kai minti biyar yana jira amma wayar taki karewa har ya kosa yagaji da zama yafara tsaki
"To Dan sarkin Mara kunya tsakin me kake" mummy tafada bayan ta kammala wayar
"Tun dazu na shigo kina kallo amma kin tsaya kina surutu a waya kin barni ina zaman jiranki kuma kinsam gurinki Nazo"
"Wayar da nake ne surutun JALAL?"
Tafada tana kallonsa
"Munyi waya da megidan nan dazu yace in gaya miki
yana dawowa jibi"
yafada a takaice batare daya bata amsan tambayrta ba, inba hakaba yanzu zata fara masa fada Takara masa wani takaicin, kuma shi a rayuwarsa ya tasani fada.
Ilham datake kitchen taga shigowarsa Dan haka ta aje abinda takeyi ta dakko juice da cup ta dorosu a tray ta fito palour tana yauki ta nufi India Jalal yake
Cikin iyayi tafara magana
"Yayana ga juice na kawo maka"
Bece komai ba sema Kafeta da yayi da ido ko kiftawa ba yayi
Nan ta sha jinin jikinta saboda kallon da yakemata
"Mtsewwwww" yaja wani dogon tsaki ya mike ze bar palourn
"Haba Jalal meyasa kake hakane? Ilham fa kanwarkace koba komai ai yakamata ka karba kasha" mummy tayi maganar adan hasale
Ko takansu be biba seda yaje bakin kofa ya tsaya batare da ya waiwayo ba
"Yace in gayamiki jirgin karfe hudu ze biyo" (yana nufin mahaifinsa)
Yayi gaba abinsa
"Na shiga uku mummy meyasa Yaya Jalal yakemin haka kwata
bana gabansa mommy kiyi wani abu Dan Allah wallahi ina son Yayana amma ni meyasa baya sona"
Ilham takarasa maganar cikin sheshsheka kuka
Rungumota mommy tayi tana rarrashi
"kiyi hakuri Ilham ina iya kokarina ni kaina fama nake Jalal kinagani ina mahaifiyarshi amma ban isheshi komai ba
Amma in dai ina raye Jalal bashi da wata matar inba keba insha Allah"
Aikuwa daga ranar da burina yacika kingama yawo mummy dan sekinyi kuka da hawayenki Dan ba lefi bane in anmaka abinda kayi tafada a ranta amma a zahiri kuma secewa tayi
"Allah yasa mummy kitemaka min burina yacika in mallakeshi Dan Allah wallahi in ba shiba bazan iya auren kowaba"
"Karki damu Ilham keda Jalal duk abu dayane a gurina insha Allah zanyi duk meyiwuwa inga kin auri Jalal"
"Nagode sosai mommyna inkikamin haka kingamamin komai"
Wai ni Jalal
yarinyar nan take cewa innayi zuciya indena kula yayanta saboda muna da banbancin tarbiyya
Zanyi maganinta ai rana dubu ta barawo daya tak itace tame kaya zan kamata a hannu
Haka yayi ta wannan zancen zucin
Bayan kwana daya
Gidansu Jalal suka tashi da aikace
saboda shirin dawowar magidan,
sedai aikin yayiwa mummyn da Ilham yawa saboda me aikinta ta tafi kauyensu za ai bikin yayarta ga Ilham da shegen son jiki.
Dan haka mummy ta Yanke shawarar kiran maama a waya tace Dan Allah tabata Aron su Jalila su tayata aikin dan yayi musu yawa,
kimanin wata hudu kenan rabon mahaifin Jalal da Nigeria Dan haka dole ayi shiri na mussaman domin tarbarsa.
A waya ta kira maama ta sanarda ita Dan Allah inba abinda su Jalila suke ta turo su tayata aiki ayyukan dayawa
Itakuma tace zata turomatasu
Dakinsu mama taje ta sanar dasu sakon mummyn Jalal
Nanace tace
"To maama zamuje insha Allah"
Itakuwa Jalila cikinta ne yayi wata kara me sauti kuuuuuuuu!!!
"Na shiga uku ni Jalila !!?
" me yafaru ne Jalila?" Nana ta fada tana kallon Jalila
"Au tambayata ma kikeyi yanzu in Jalal ya ganni fa? Yanzu ni yazanyi"
"Tab yanzu meye abunyi ainamanta da kinmasa rashin M,
shiyasa nace miki ba ruwanki dashi Jalila yanzu ga irinta nan"
(Nikuwa nace hmm danma bakomai kikasani ba jiyama tamasa rashin kunya" Jalila sarkin rawar kai da shishshigi)
"Kinga ni ba wannan ba ko ince kawai bani da lafiya? Se in zamana base naje ba"
"Kai Jalila wannan ba shawara bace yanzu fa Maama ta shigo ta ganki ras dake sannan kice baki da lafiya wannan ba shawara bace Sam"
"To ya zanyi? Inkuma muka hadu fa ?"
"Bazaku haduba insha Allah kitsaya a waje in leka in baya nan seki shigo"
"To amma nikam ina jin tsoro Nana"
"Ba abinda ze faru insha Allah, kwantar da hankalinki taso mu tafi"
A kofar Gida Jalila ta tsaya tana
waige
itakuma Nana ta shiga domin dubawa in Jalal yana nan minti uku Sega Nana ta fito ta kalli JALILA ta girgizamata kai
"Shigo baya nan"
"Kin tabbata"?
"eh na tabbata banganshi a ciki ba,
Hmm waike dama kinsan kina jin tsoro amma kika tsokano shi"
"Ke ni matsa in wuce tun kafin ya dawo ya ganni anan" Jalila tafada a gaggauce
Tare suka shiga cikin gidan Jalila tana ta faman
rarraba ido
A palour suka ci karo da Ilham rike kwanuka zata shiga kitchen, bata kula suba tai shigewarta batace musu komaiba ta shige kitchen ta ajiye kwanukan sannan ta fito sewani shan kanshi take tana hura hanci
"Waike Ilham har yanzu abinda yafaru be wuceba a gurinki kike ta wani kallonmu kina hade rai
Indai Jalila CE ita tamanta ma kunyi kiyi hakuri Dan Allah"
Jalila kuwa a ranta cewa tayi
Tab lallai aiki yaganki indai nice bana gani inyi shiru
"Hmm bakomai ya wuce kuzo mukarasa mummyn tana ciki"
Suka bita gaba daya wani part suka nufa Wanda tunda Jalila tazo a rufe take ganinsa tana kyautata zaton shine part din mahaifin Jalal
Shigarsu yayi dai
da fitowar mummyn dauke da labulaye a hannunta, Nana daga inda suke ta Dan rusuna ta gaisheta ita Kuwa Jalila seda ta durkusa har kaasa, sannan ta gaisheta, fuskarta a sake ta amsamusu
Har cikin ranta taji inama Jalal din tane haka yake girmamata
Karasawa Jalila tayi gurin mummy ta karbi kayan hannunta
"mummy kawo ina za akaisu?"
"Dama wasu za a canza wannan zan badasu wanki biyoni seki karbo wasu a canza tace to"
Juyowar nan dazatayi taganshi zaune akan kujera, alamu ya dade a gurin itace bata lura dashi ba
Nana kuwa tun shigowarsu taganshi a zaune amma ta lura JALILA ba ta Ganshi ba,
Be dago ya kalleta ba seda mummy tayi gaba tabiyo bayanta, sannan yayi mata kallon zamu gauraya dake
Itakuwa kallon up and down tayi masa hada murguda baki tayi sauri tabi bayan mummy
Akajima Jalila ta dawo da labulaye a hannunta suka fara gyaran part din yana zaune beje ko ina ba
" mummy tace Nana da Ilham suzo su siyo abinda babu saboda girki tunda taga Jalila tafisu rashin son jiki"
"Mummy indai Jalilace intaga dama batajin aiki "
"Ainima naga alama Nana"
ILHAM da Nana suka tafi cefane yai saura Jalal, Mummy, se Jalila
Mummy ce take kokarin Jan wata durowa na litattafai amma takasa,
Jalila tazo ta tayata amma suka kasa,
Takaici ya ishi Jalila ganin ga JALAL a zaune amma yakasa temakawa tsaki taja
"Mtsewww mummy wannan Dan naki bashi da amfani Sam wallahi yana kallo muna fama amma ko a jikinsa"
"India JALAL ne kadan kika gani bari in dakko bagco a rage litattafan mugani ko zamu iya janye durowan"
Ita Jalila a hankali tayi maganar batai zaton yajiba,
Sedai kawai gani tai yana kallonta
Mummy na Barin dakin,
ya tashi ya tako har gabanta yana muzurai yana mata wani irin kallo, yana zuwa gabanta yatsaya yadan kura mata ido
Nan da nan jikinta ya dau rawa
"Mara tarbiyya, Mara amfani, mutumin banza, mekama da yan daba, Dan shaye
Niko?" Yanuna kansa da yatsansa
"To bari ingaya miki wani abu ba tsoronki nakeji ba Dana kkyaleki ban
kakkaryaki ba,
bana son in batawa Dan uwana rai sedai kawai zan maidake Irina ne, shize tabbatar miki bani da tarbiyya kinga in mukazama mu biyu semunfi dadin kwatance
Jahila kawai dakikiya na tsani ganin ko fuskarki"
Ya juya da nufin yafita yabar dakin
" duk jahilcina nasan girman iyayenaa kuma inazuwa makarantar islamiyya,
a islamiyyarmu ma nasan akwai ukuba game sabawa iyaye tundaga duniya, dukda Jahilcina bana zuwa mashaya ina girmama manyana, kaga sekanemi waye jahili"
Yana jinta kalamanta suna dukan zuciyarsa amma ya fice ya kyaleta da sannu ze maganinta.
Haka sukayita aiki har yamma tayi suka shirya girke
suka gyara ko ina Wanda yakasance Jalila ce karfin aikin
"Karfe hudu da rabi dai
Jawwad da Jalal sukaje airport suka dakko Alhaji Habib Kamal,
mahaifin Jalal ya karaso gidansa cike da farincikin ganin tilon dansa cikin koshin lafiya, dukda yawan korafin da mahaifiyar D`an nasa kanyi masa game da miyagun halayen yaron nasu.
Gaba daya sukashiga cikin gidan kowa se fara a yakeyi ana mass sannu dazuwa
Daka ganinshi kasan mahaifin Jalal ne saboda
tsabar kamar dasukeyi,
kaman yadda yake dabi'ar
Jalila, har kasa ta durkusa ta gaisheshi,
Da sakin fuska ya amsa mata tareda cewa
" wannan fa?"
"Ai Yar wajen marigayi ce kanin babansu Jawwad" mummy tabashi amsa
"Allah sarki, Ashe takwarar Jalalce ta girma haka, tubarkallah
gata nutsatsiya
Allah yaraya ma naku gaba daya"
Suka amsa da "Ameen" gaba daya
Banda Jalal dayake ta cin magani a ransa yace "wai wannance nutsatsiya munafuka Mara kunya yarinya"
Watsewa suka farayi a hankali domin Barin daddy ya huta
Ilham ta tafi dakinta tashiga wanka saboda tagaji,
Jawwad yakoma Gida
Shikuma Jalal yatafi part dinsa
Jalila da Nana Suma suka nufi hanyar Gida har sun fito Jalila ta tuna
wayarta tana gidansu Jalal inda ta kwaso labulaye daga Shanta
"Au Nana wayata rakani in dakko please"
"Gaskiya nagaji bazan koma b"
"Dan Allah ki rakani, inkuma Jalal yakamani fa?"
"A gabanki fa Yakoma part dinsa baya cikin gidan inajiranki anan jeki dakko"
"To bari inje"
Tashiga ba kowa a palourn Dan haka da sauri tashiga ta dakko wayar,
tana zuwa corridor din daze sadata da waje taganshi a tsaye yabawa inda take baya yana waya na Shiga uku inya kamani na shiga uku, wata dabara ta fado mata
Ta tako da gudu zata wuce tabayansa caraf ya riketa
"Haba karamar Mara kunya kinzaci bansan da shigarki bane yau babu me kwatarki zanga karyar rashin kunya",
" meye haka dalla malam cikani"
Tafada tana kiciniyar kwace kanta
"Ooh har kin manta da maganar mune
Zan maidake Irina ne kawai in samu abokiyar shaye
"Dalla ka cikani ni ba Yar iska bace "
"Nima ba Dan iska bane kawai Mara tarbiyane, kema kuma hka nakeso kizama,
yanzu sigari kawai zaki sha kema kizama salansa kaman ni kullum bakinki cikin hayaki"
Wani mugun kallo tayi masa
"Allah ya kiyaye in zama irinka kai halinka har wani abun sone
mara...........
Bata karasaba yasaka sigarinsa a baki ya zuka hayakin a bakinsa
Ya rikota yasa hannunsa daya ya toshe mata hanci, yasa bakinsa a nata ya dure mata hayakin nan tas a bakinta,
aikuwa take numfashinta ya sarke,
Yakuma zuka ya dura mata sau uku
Sannan yasaketa ta zube tana wani irin tari tana Jan numfashi da kyar, idanun ta sukayi jawur, numfashinta yana sama yana kasa kaman me asthma
Share please
More comments more typing............
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
_ABDUL
JALAL_
_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)
PAGE-
Chapter 6 · 0% Book details