← Book details Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 52

PART 1

Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,
ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
I want comments not stickers
Comments dinku
shine kwarin gwiwata
_My first novel_
"Gobe ma in kikaga Jalal kikuma zaginsa useless creature kawai"
Yayi tafiyarsa ya barta a gurin tana ta mimmikewa tana fama da numfashi ta galabaita har a tafara fita hayyacinta.
Mummy ce tafito daga sashen daddy zata shiga kitchen ta dinga jin kakari da nishi, dawowa tayi da baya a Dan tsorace, tana duba meke wannan nishin,
Jalila tagani a zube a gurin tafita hayyacinta numfashinta nata fita da sauri
(Lallai JALILA ta sha hayaki)
" subhanallah ke Jalila meyafaru meke damunki??"
Tazo tana taba ta
"Ohh ni khadija meke damun ta kodama tanada athma ne
" Ilham!,
Ilham!!,
Ilham!!!,"
Tashiga kwala mata kira
"Ke Ilham kifito da sauri"
Itakam Nana gajiya tayi da jiran Jalila Dan haka kawai tayi tafiyarta ta shige Gida,kai tsaye taje dakin mummy
"Mummy mun dawo "
"To sannunku ina Jalilan?"
"Wayarta ta manta ta koma dakkowa shine na taho"
Kai inkuma Yaya Jalal ne yamata wani abunfa tai wannan tunanin a ranta
da sauri tafito ta nufi gidansu Jalal
Shikuwa Jalal gurin Jawwad yatafi abunsa, kaman be aikata komai ba hankalinsa kwance
Amma lokaci2 in ya tuna maganganun Jalila se ransa yabaci .
Da gudu Ilham tafito
"Mummy lafiya kuwa?
" zo kiga Ilham dama tanada asthma ne ko wani cutan?"
Ilham ta Dan zaro ido
"Mummy ya za ayi in Sani"?
" maza jeki gidansu kifada suzo akaita Asibiti kar ta mace min a Gida"
"To bari in je"
Mayafi Ilaham ta dauka ta fito da sauri a bakin gate taci karo da Nana
" yawwa Nana Jalila dama tanada asthma ne kowani cutan?"
A firgice Nana ta kalleta
"Asthma kuma? Bata da wani asthma, me yasameta?"
"Zo muje kyagani"
Ilham tafada tana janyo hannunta zuwa cikin gidan
"Subhanallah Jalila meya sameki?"
Nana tafada tana jijjiga Jalila amma Jalila bata San me akeba tafita hayyacinta
Da gudu Nana ta tafi gida domin sanar dasu abinda yake faruwa,
tana shiga gida a harabar gidan ta ci karo da su Jawwad
"Ke Nana lafiyarki kike gudu haka? sekace wata karamar yarinya mene haka"
Jawwad ne yayi maganar a Dan fusace
"Yaya Jalila CE"
"Me yafaru da ita?"
Yafada hankalinsa a tashe
Nima bansaniba
yaya tana gidansu Yaya Jalal yanzu muke tare da ita takoma dakko wayarta yanzu kuma
ta suma bata iya numfashi sosai
"Suma kuma"
Ai bejira tagama bayanin ba yayi hanyar waje da sauri
Wani Dan guntun murmushi Jalal yayi sannan yabi bayan Jawwad
Itama Ilham ta karasa cikin Gida dan ta sanar da maama abinda yake faruwa
Suna zuwa suka tarar da Jalila kwance akan cinyar mummy bata numfashi, se kadan
"Subhanallah Jalal bani key din motarka mu kaita Asibiti" Jawwad yafada da sauri
Key din ya danka masa
memakon ya raka Jawwad sema ta shi da yayi yai ficewarsa
Jawwad beyi wata
ba ya dauki Jalila yayi waje da ita yasaka ta a mota ya tada motar kenan
Nana ta shigo
gidan ya tsaya ta Shiga motar
"Yaya maama tace muyi gaba zata taho in Abba ya dawo"
Be amsa mata ba yaja motar
"Ilham ki bisu mana kirakasu ko Asibitinne kinga ni badamar in fita yau babanku ya dawo" maama tayi maganar tana duban Ilham
"Ba inda zani wallahi Allah ya bata lafiya in nabisu ai bani zan bata lafiya ba"
"Haba Ilham amma ai a gidanmu abun yasameta"
"Ni wallahi mummy a gajiye nake ba inda zan iya zuwa yadda nagajin nan
hutawa nake sonyi"
Ta wuce daki abunta
"Ohh ni hadiza yaran nan se a hankali kowanne da halinsa
Suna zuwa Asibitin aka karbesu aka shiga da Jalila emergency don ceto rayuwarta
Wajen karfe Tara na dare Maama sukazo asibitin ita da Abba
Wanda yai dai
Da fito da Jalila daga emergency aka basu daki
Alhamdilillah numfashinta ya dawo dai
se dai tanata bacci ga drip da aka saka mata
" Allah sarki diyata Allah yabaki lafiya, Amma nayi mamaki iya sanina bata da wani ciwo makamancin haka"
Abba yafada cike da damuwa yana kallon maama
Dan tabe baki maama tayi
"A'a to ai ba dolene kasaniba watakila tana dashi mune bamu saniba kasan uwatta bakomai zata gaya mana ba tunda...."
"Ya isa haka Zainab.." Abba ya katse maama
"Yanzu lafiyarta muke fata ba wani surutu ba"
Likitan ne ya shigo domin kara dubata
Jawwad ne yayi gyaran murya
"doctor meyake damunta ne?"
"Eh blockage ne akasamu a airways dinta maybe ta kwarene ko kuma ta shide da wani abun,
Zatasamu lafiya insha Allah munyi mata allurai zatayi bacci karku damu Allah yabata lafiya" suka amsa da Ameen
Guraren sha daya na dare
Abba da Jawwad suka tafi Gida akabar Nana da da maama suka kwana a gurin Jalila
Washe gari da sassafe Jawwad ya tashi ya shirya da nufin ya koma Asibiti, dayake motar Jalal a hannunsa ta kwana kafin ya wuce ya maida motar gidansu Jalal,
Jawwad ya tsaya
suka gaisa dame Gadi yayai masa yame jiki dayake yasan meyafaru,
ya" amsa da sauki,"
Jawwad ya juya zefita se yadawo da baya ya kalli me gadin
"Jalal yana nan ne"
"Eh yana nan yana bangarensa"
"Nagode"
Jawwad ya juya ya nufi part din Jalal Lamar kullum ya na kwance yayi dai
yana bacci babu alamar yayi salla
Jawwad ya daddaki pillown da Jalal yake kwance
A hankali Jalal ya bude ido
"Tashi kayi sallah Dan nasan bakayi ba"
Seda yadan ja seconds sannan ya tashi zaune yana hamma bece masa komai ba ya mike yaje
Yai alwala yagabatar da sallar asuba karfe 7:30am
"Jalal fushi nake da kai"
Jawwad yafada tare da Dan hade rai
Jalal ya kalleshi
"Why"
"Kanwata ba lafiya rai a hannun Allah amma ko ka tambayeni ya jikinta talk less of kace zaka min kara ka dubota to ni na roki arziki ka rakani Asibiti"
Dabeyi niyyar zuwa ba amma yaga in yai haka be kyautawa amininsa ba wato Jawwad Dan haka yace
"Sorry bross karkayi fushi dani bari in shirya muje"
"Seda na roka?" Jawwad yafada yana Dan hada rai
Murmushi Jalal yayi "to koma mene ai nace zani in kuma bakasone in koma baccina"
"Kai ka isa ni yi Sauri karmu makara ni sonake tana farkawa tafara tozali da fuskata"
Girgiza kai kawai Jalal yai a ransa yace ka dorawa kanka wahala saboda wannan banzar yarinyar Mara kunya
Kafin Jalal yagama shiryawa Jawwad yakira maama
A waya bugu seda ta kusa tsinkewa sannan ta daga
" salami alaikum maama barka da safiya "
"Yawwa barka ya daddynaka"?
"Muna lafiya dama tahowa zanyi nace ko kuna bukatar wani abun?
" a'a bama bukatar komai ka hanzarta dai inaso indawo Gida in huta nibana son zaman Asibiti "
"To maama yanzu zan iso insha Allah, nace ya kuwa Jalilan ta farka ne"
"Ban saniba in kazo kaganewa idonka kaita wani rawar kai akan yarinyar nan ka kiyayeni wallahi"
Ta kashe wayarta
Shidai a iya tunaninsa beyi wani abu dabe daceba amma meyasa maama ta dau zafi haka yayi ta zancen zuci har Jalal yagama shiryawa suka tafi
Sun isa asibitin dukda Jalal ya Dan bata musu lokaci
room din da aka kai Jalila suka nufa
Jawwad ne ya bude kofan tare da sallama
Maama ce ta amsa dayi musu sannu da zuwa,
yawwa tunda kunzo bari mu je Gida dama ruwa zasu karasa mata da allurai kawai su sallameta,
Ninazata tun dazu zakazo Abbanku yazo ya dubata yanzu ya tafi.
shikam gogan kujera ya janyo ya zauna abinsai be kula kowa ba
Alhamdilillah jikin Jalila yayi kyau sun sameta tana rama sallolin dabatayiba
"In ta idar Jawwad ka kira nurse din suzo su karasa mata abinda zasuyi mata seku taho Gida" Maama tafada tana shirin tafiya
Sukagama abinda zasuyi maama da Nana suka tafi Gida.
"Yaya ina kwana"
Jalila ta gaisheshi
"Lafiya qalau ya jikinnaki?"
Jawwad yafada cike da kulawa
da sauki Yaya
"Waime yafaru dakene? Ya akai haka tafaru"?
seda ta kalli inda Jalal yake suka hada ido, tai sauri ta dauke kanta
Ta maida kallonta ga Jawwad
"Kwarewa nayi" tafada a takaice
"Kwarewa kawai numfashi ya dauke ko kinada asthma ne?"
"A'a Yaya banida asthma"
Duk abun nan Jalal danne
wayarsa kawai yake, ba Wanda ya kula a cikinsu
"To tunda kin idar bari inje inkira nurse suzo su miki alluran dafatan kinci abincin?"
"Eh naci abinci, amma ban idar da sallah ba zanyi walhane"
"Kai sisyna bakida lafiya fa ai Allah yaga zuciyarki"
Jawwad ya danyi maganar a shagwabe
Jalal ji yayi kaman ya shake Jawwad yaga yanata wani lallabata hada yiwa mace shagwaba saboda shirme
(Niko nace a ganinka ba)
Itama a shagwaben tafada maganar
"Nifa zan iya Yayana kasan sallah haske ce me girrma kuma tana hana mutum aikata wasu laifukan,
Yayana abune mawuyaci kaga Wanda ya tsaida sallah yana aikata wasu miyagun laifuka da baya kunyar yinsu agaban mutane,
Koda ze aikata yana kunyar mutane suganshi
Kaga inka tsaida salloli biyar seka kara da nafila bakasan abinda Allah ze duba a ayyukanka ba yai maka rahama"
"Nice one sisyna proud of you
Allah yasa iliminki ya amfaneki ya amfani al Umma"
Jawwad tafada yana murmushi
"Proud of u too bros"
Jalal yasan da biyu tayi wannan maganar amma yai kaman besan me sukeba
Seda ta idar da sallah takoma kan gadon sannan
Jawwad ya kalli Jalal
"yace brother zomuje induba nurse din suzo susa mata ayi ai sallamemu"
"Jeka dawo ina nan" abinda Jalal yace kenan
"OK to bari inje"
Gaban Jalila ne yafadi ta kalli Jalal idonsa yana kan wayarsa ba ita yake kallo ba
To in yayi min wani abun fa
Jawwad nafita Jalal ya kalleta
Kina tsoron in kumayi miki wani abun ne?"ya mike daga inda yake yadawo kujerar gaban gadonta
"Meyasa baki gaya musu gaskiya cewa taba kika shaba,
rashin sabone kawai, in bahakaba daga shan sigari seki suma kikusa shekawa lahira?"
yafada yana murmushin mugunta
Banza taymasa taki kallon sa
"Yanzu sauranki giya da kwayoyi tunda ina sha kema sekin sha,
Kwanan nan kema zaki fara zuwa mashaya"
Yafada yana hade rai
"Allah ya kiyaye ya tsareni, dazama irinka bazan taba zama irinka ba Mara tarbiyya...
" ohoh wait ashefa Ke kin tsaida sallolinki biyar a rana hada nafila nikuma banayi shiyasa Ke ba irirna bace,"
Nima bani na saiwa kaina ba amma zanyi meyuwuwa inga kinzama Irina tunda jiya kinfara ki rubuta ki aje sauraanki giya da kwayoyi zaki zamaa abar kwatance kaman ABDULJALAL sha
jahila, I hate u"
"God forbid, over my death body kwatance in dai bana Alkhairiba indai irinnaka ne Allah ya kiyaye kuma niba Jahila bace wallahi"
Hannu yasaka a aljihunsa ya dakko taba da lighter
"naga kaman ta jiya bata isheki ba sokike in kara miki wata"
girgiza kai tashigayi tana zare ido
"Mara kunyar karya kawai"
Yafada tare da maidasu aljihunsa
Ya mike ze koma kujerar da ya taso kawai yaji muryarta tana fading
"Kuma wallahi Allah ya isa abinda kamin jiya kodayake bakasan ma'anarta ba kona maka bazaka damu ba amma ban yafe wallahi azzalumi kawai me kama da yan daba"
Ohh God yarinyar nan ba zata canza ba,
Dawowa yayi inda take har gaban gadonta yasa yatsunsa biyu a side din kumatunta ya matsa da karfi
Wani uban ihu tasaka saboda zafi jitayi kaman ze Huda mata kumatu da yatsunsa nan da nan hawaye ya shigo zubowa daga idonta wani nabin wani sedayaga fuskarta tayi jawur hawaye na ambaliya a fuskarta
Sannan ya cikata Yakoma inda yake zaune da farko yana danna waya
Jawwad ne yayi sallama tare da nurse
Kallonta
Jawwad yayi
"lafiya kuwa sisy kukan me kikeyi?"
Seda ta kalli inda Jalal yake amma ba ita yake kallo ba
"Ni Kaduna zankoma gurin Ummi'"
Tai maganar tanakuma fashewa da kuka
Se da Jalal yayi murmushi mugunta
"Haba Jalila dama hayanzu kina wannan rikicin naki kiyi hakuri in muka koma Gida mayi wannan maganar"
Kai kawai ta gyada masa
Nurse din takarasa mata abinda yakamata aka sallemesu.
Har suka Shiga mota suka kama hanyar Gida kuka takeyi shikuma
Jawwad se aikin rarrashi yake
Shikam Jalal Jawwad yafi bashi haushi se wani lallabata yake
Itakuwa ita kadai tasan zugin da fuskarta takeyi ga kirjinta hayanzu ba dadi saboda wahalar yin numfashi da tayi
(Nikam nace in rashin kunya abinyine gobe maki kara)
Maama da Nana suka iso Gida Nana wanka tayi ta kwanta saboda batasamu tayi bacci sosai ba Daren jiya
Maama kam datayi wanka seta shiga kitchen da niyyar Dora sanwar rana
Sallama taji a parlour Dan haka ta aje abinda take ta domin ganin me sallamar
Wata matace mekama da maama sekuma wata budurwa da batafi sa'ar su Nana ba
"Yaya mairo sannu da zuwa yanzu kuke Tafe da ranar nan"
Wadda takira da Yaya mairo tace
"eh mune ai munzo tunsafe bakowa a gidan narasa INA kuka tafi da safe haka gashi ni ba waya a hannuna tasamu matsala,
Kukuma makota kowa gate a rufe sekace marasa gaskiya"
"Wallahi kinga Jalila ce tazo mana hutu se kuma ta yanke jiki tafadi jiya,
A Asibiti muka kwana sedazu muka dawo, mun baro za a sallamata Jawwad ze taho da ita"
Wani mugun kallo Yaya mairo tayi mata
Sun iso gida lafiya sukayi parking
Jalila fuska duk hawaye amma se cewa tayi "Yaya JAWWAD an kira azahar ka tsaya a masallaci kai salla
Kasan sallar jam'i tafi lada akan sallar mutum daya kodayake garama Wanda yakeyi shika dai wanima bayayi"
Jawwad ne ya kalleta da mamaki
da nufin yayi magana
Ta bude kofa tafice da Sauri
Shiko Jalal yasan dashi take sarai haka halinta yake bazata canza ba amma seyayi kaman beji me tace ba shi dariya ma taso bashi ganin fuskarta duk hawaye amma Neman magana take
Ta nufi cikin gida abinta har yanzu jikinta babu kwari sosai, tana shiga ta nufi dakin maama domin ta Sanar da ita ta dawo an sallameta
takama handle din kofar da nufin ta shiga
amma maganganun datajine
Suka Sa ta daskare a tsaye zuciyarta ta fara bugawa da karfi
"Gaskiya zainabu baki da hankali yanzu har asibiti kikaje jiyyarta kika barota da danki, dangin arna ababen kyama kika bari tana mu'amala da yayanki hartazo miki Gida Hutu koda take musulma ai daga tsatson arna tafito!!!"""
Tirkashi wasa farin girki
Please share
More comments more typing......
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
_ABDUL
JALAL_
_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)
PAGE-
Chapter 5 · 0% Book details