PART 1
Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,
ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi
Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.
Domin Samun karanta
wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar
07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din
https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
I want comments not stickers or just thanks
Your comments give me courage
-My First Novel-
"Da kasake ka tafi da yanzu ka gane illar hawayen iyaye"
"Kinmanta kashedin danayi miki game dani ko? Har yanzu baki fasa min shishigi ba ki ji da rayuwarki, ba ruwanki da rayuwata"
Ya katse wayar ya aje tare da fadin
"Jarababbiya kawai, ko ina ruwanta dani oho, zan sauke mata wannan taurin kan"
Jawwad ne ya dawo ya tarar dashi
"Yunwa fa nakeji, find something for me to eat"
"Kamar me kake so"
"Komeye ma amma banda tuwo
Yarinyar nan ta kaimin abinci nazata wani abun kirkin ne ashe wannan abinne dabana ci saboda tsabar ta rainani aikuwa zan koyamata hankali"
"Ai kai abunda baka ci dayawa wanne daga ciki"
"Kaga ni abar wannan maganar me kukayi yau"
"Nima banci abincin ba alala sukayi yau"
"What alala kuma,"
Ya Dan girgiza kai
"Kasan itama bana ci"
"Anyway bari in canza kaya muje restaurant se muci"
"Kar ka kaini inda za abani abunda za bata min ciki kasan bana son jagwal gwalo"
Murmushi Jawwad yayi
"Jalal kaima yakamata ka canza kayan nan kasaka manyan kaya"
"Nifa bana son wannan kayan nauyin isa ta suke da zafi"
"Please dan Allah kasa manyan kaya"
Jawwad ya fada yana Ciro masa wata hadaddiyar Shadda coffee colour yaita lallaba shi har ya yadda ya karba ya canza kayan yasaka shaddar nan,
Ba karamin kyau Jalal yayi a cikin kayan nan ba manyan kaya ba karamin fito da kamalar namiji yake ba Jawwad yaita koda shi, yana masa hotuna yana yaba masa yayi kyau,
Haka suka shirya suka tafi restaurant cin abinci
Jalila ce a office din malamai ta inda suka shiga ba ta nan suke fita ba suna mata fada akan rashin ji
Saboda ankawo kararta akan jiya ta tsokanowa yan uwanta dalibai yan daba, masu zaginta sunayi irinsu malam Naziru, masuyi mata nasiha sunayi ita dai Jalila shiru tayi batace komai ba
suka gama ta tashi ta koma aji tanata cika tana batsewa
Ba a jima ba malam Naziru ya shigo ajinsu da hanzari yana kiranta
"Jalila zancen musabakar nan ne ya taso wadda za ayi a Abuja
sati me zuwa insha Allah"
Wani irin mugun kallo Jalila tayi masa tai masa banza
"Jalila da ke nake fa kije ki jadadda hadda abun yazo mana a bazata dukda nasan bani da damuwa akanki"
"Ba inda zani kunemi me zuwa karkuje inja muku magana, yaza ayi kamata taje musabaka "
Tafada tana hade rai
Sekuma ya Dan sha jinin jikinsa
"Wai meye hakane Jalila ana magana kina wani zance daban ina miki magana"
Mikewa tsaye tayi tare da kara hade rai
"Nace fa bazani ba anemi wasu suyi ni bazani ba,"
Ta dau Jakarta ta bar ajin
Office malam Naziru yakoma yana mita
"Kajimin ja'irar yarinya nizata cewa bazata je musbaka ba wai anemi me zuwa"
Malam Yusuf ne yace
"Banga laifinta ba nan kuka sata a gaba da fada bama kai se yanzu kuma bukatarku ta taso kuce tazo tayi muku,
irin wannan yaran nasiha ake musu ba zagi ba duk abu suna da irin baiwarsu"
"Hmm ni ba wannan ba tunanin mafita nake kasan ta da taurin kai abune me wahala taja ga malam baya nan"
Jawwad ne ya tashi ya tafi amsa waya yayinda Jalal ya dukufa yana cin abinci saboda yunwar dayake Ji
"Masha Allah"
Wata budurwa ta fada, mikewa tayi daga inda take tazo kujerar gaban Jalal ta janyo ta zauna
"Sannu dai barka da wannan lokacin"
Dan dagowa yayi ya kalleta, ya maida kai ya cigaba da cin abincinsa
"Ehmm nace ba Dan Allah magana nakeso muyi da kai"
Still shiru yayi mata yaki magana haka tacigaba da surutun ta ko kallonta yakiyi
Jawwad ne ya dawo yasamu guri ya zauna
"Sannunku da fatan ban takura muku ba"
Jawwad yafada yana murmushi
"Mtseww kaga ci abunda zakaci mutashi mu tafi ni nagama kasan bana son kallo"
Jalal yayi maganar a fusace
"Dama yana magana?"
Budurwar ta tambaya
Dariya Jawwad yayi
"yanayi mana, gashi kuwa kinji"
"Amma nayi masa magana ya shareni"
Se Jawwad yai niyyar tsokanar Jalal
"Au be kulaki ba, aikuwa yana magana, haba bros ya zata na maka magana ka shareta"
Wani takaici ne ya tokare wa Jalal shi Sam baya San sabga da mata dan haka banza yai musu
"Au bazakayi maganar ba kuwa"
"Inaga nidin ce baze kulaba, ba komai nagode"
Ta mike zata tafi
"Kiyi hakuri fa Dan uwan nawane se a hankali"
Murmushi tayiwa Jawwad sannan ta mike ta bar gurin
Wani uban tsaki Jalal yayi yana hararar Jawwad
Sunkuyar da kai Jawwad yayi yana dariya Jalal ji yayi kamar ya naushi Jawwad
Haka Jawwad yagama cin abincin suka nufi Gida
Tunda Jalila ta koma gida sedata shafe kwana uku bata zuwa makaranta
Ummi tayi
tagaya mata meyasa bata zuwa makaranta amma taki, kullum seta ce mata bata da lafiya,
Seda malam Naziru da wasu malamai suka biyo Jalila har Gida akan takoma makaranta saboda batun musabaka
Ummi tace musu ba komai indai Jalila ce zataje musabakar insha Allah sukayi mata godiya suka tafi
Ta dawo Gida taitama Jalila fada meyasa zatace bazatayi musabaka ba har malamanta su biyota Gida suna lallabaki
Dan tsuke fuska Jalila tayi
"Ummi bakiga abunda sukayimin ba suka dinga min masifa kuma se yanzu yawani zo wai inje musabaka wallahi Dan kinsa bakine kuma Dan malam babba zani wallahi da bazanje ba"
"To yanzun ma kice bazakiba mana in dai za a biyewa halinki ai kullum se an zanekima ba fada ba"
Kayan da Jawwad yabashi yasaka ne duk suka isheshi da zafi Dan haka suna dawowa gidan su ya wuce domin ya canza wasu kayan zuwa kananan kayan daya saba sawa
Yana bedroom dinsa yana kokarin canza kaya yaji motsin Ilham a palour zata kwashe Warmer's din data kawo masa abinci, bubbudewa tayi taga baici ba
Fitowa parlour yayi ya tsaya a bakin kofa Dan dago kai tayi ta kalleshi masha Allah wani irin kyau taga yayi me daukar hankali kayan sun masa kyau sosai ta Dan kura masa ido
"Ke me ye haka uban me kike kallo, saboda tsabar kin rainamin hankali kika kawomin wannan abincin, kuma kinsan banacin wannan abun amma kika dakko kika kawomin yaushe nafara wasa dake dazaki min wannan rashin mutuncin"
Yasalam ta manta baya cin cous
"Am...am wallahi Yaya namanta....."
"Shut up kwashe su kibarmin daki sokuwa kawai komai kin manta shiyasa kike dakikiya both islamiyya da boko kanki Sam baya Ja fita ni"
Ai garani ina zuwa kaifa
Ta fada a zuciyarta ta kwashe kayan tana zumbura baki tana kunkuni
"Ke ni kikewa kunkuni na tattakaki wallahi kinsan halina sha
kawai"
ta bar dakin
"Indai zaka biyewa mata se Jininka ya hau"
Yai maganar a fili tare da yin tsaki
Jalila ta dage da tilawar haddarta malam Naziru se kuma lallaba Jalila yake saboda yana son taje musu musabaka Abuja
Kullum dare se tayi waya da Jawwad se suyi kwanaki basuyi waya da Nana a wayaba, amma kullum suna manne da Jawwad a waya
Yauma yana dakin Jalal suna hira Jalila ta kira waya in suna wayar nan Jalal bata masa rai sukeyi
Jawwad kuma yaita biye mata
"Yayana saura kwana uku insha Allah zamuje Abuja musabaka"
"Masha Allah, badaban inada lectures ba ranar dase nazo garin Abuja naga yadda kanawata zatayi musabaka in bata kwarin gwiwa"
"Koba ka nan kalamanka zasu bani karfin gwiwa, kasani a addu'arka Dan Allah"
"Addu'a kullum cikin yimiki nake Insha Allah zakiyi nasara"
"Godiya nake yayana ka gaida mutan gidan"
"Zasuji insha Allah, muna tare da yayanki Jalal zan gaya masa shima ya yi miki aduu'a"
Jalila dariya ta kwashe da ita tare da kashe wayar
"Jalal kanwarka zataje musabaka Abuja ranar Juma a insha Allah kasata a addu 'a"
Jawwad yafada yana kallonsa
"Kanwarka dai kasan ni bana kalen dangi"
"Kanwa tawace kalen dangi Jalal? kaima kanwarka ce Jalila ce fa"
Shiru Jalal yai be kuma cewa komai ba
Dama wannan yarinyar har wani karatu ta iya zata je musabaka kil ma karya take dama dai Neman magana ne ko Shiga abunda ba ruwanta ne yai maganar a zuciyar sa
Yarinyar dasuka hadu dasu Jalal a restaurant ce zaune akan gado Jeje na gabanta a tsaye yana rarrashinta
"Gaskiya Jeje ni bazan iya ba gaskiya zeyi taurin kai ko kallona fa be yiba har na gama surutuna na tashi be kulani ba se abokinsa ne yamin magana"
Tai maganar tana yatsina fuska
Jeje ne ya Dan gyara tsayuwarsa
"Hanna kiyi hakuri, dama tun farko seda nagaya miki, mugun Dan wulakancine baya saurarar mata Sam amma kicigaba da bibiyarsa kidage Hanna zaki iya"
"Amma dai kasan bana son wulakanci ko nida maza ke min layi, amma ace ana wulakantani Dan ma dai ya hadune gayen da bazanyi aikin nan ba"
"Kiyi hakuri Hanna seda na duba naga babu me iya min wannan aikin se ke,
Hanna ki dage tunda naga gayen yayi miki"
"Anyway I will try my best ka barni dashi da Hanna yake zancen zan sauke masa wannan taurin kan bani lambarsa"
"That's good Hannah shiyasa nake ji dake"
Jeje yafada yana jin jinamata
Jalila ce tayi sallama da Ummi
Ummi tayimata nasiha da fatan samun nasara
Haka taje islamiyya sukayi sallama da kawayenta da sauran malaman daba dasu za a tafi ba sunata musu fatan alkhairi da fatan samun nasara
Daga nan suka kama hanyar Abuja da sauran dalibai dazasu tafi tare,
Sun sauka lafiya aka basu masauki su huta da la'asar guri ya cika da manyan mutane daga gurare daban
aka fara gudanar da musabaka
Ilham suna parlour da mummy suna hira, mamanta tayi mata waya ta mike tace wa mummy tana zuwa
Daki ta nufa taje ta daga wayar
"Hello Mami ina wuni"
"Ke bar batun gaisuwar nan
Ya akayi yaci abincin"
"Ina fa yaci abincin na kai masa kaman zeci namanta bayacin cous
da ba shi na girka ba da tuni yaci"
"Ke ni yimin shiru tunda beci ba, kina wani shirmen kika dafa abinda baya ci
Yanzu yana ina"
"Yana part dinsa mana"
"To ke kina me ki tashi ki bar abinda kikeyi kije ki tayashi hira mana"
"Maami dan baki san halinsa bane mugun Dan rainin hankaline"
"Kiyi hakuri Ilham, ribarki CE fa da kin aureshi burinmu yacika zan dau fansar abinda uwarsa tayimin, a wuce gurin, in kina yawan zama a inda yake dahaka zaku shaku, in Allah ya kaimiu weekends kizo akwai turaren Dana karbo miki sannan yanzuma ki shafa wancan turaren Dana baki malam yacemin yayi aiki sosai a cikin turaren"
"To maami bari inje "
"Yawwa Ilham koke fa"
Mikewa ILHAM tayi tafara shiryawa tasaka wata doguwar Riga Ja me kama Jiki, ta shafa turare ta Dan Dora siririn mayafi akanta ta fito parlour bakowa a palour mummy ta tashi, Dan haka ta fito ta nufi part din Jalal
Yana kwance da gashi se dogon wando da vest ya kwanta ya lumshe Ido jinsa yake jikinsa Sam ba kwari kaman anyi masa duka
Ilham ce ta shigo parlour ta sameshi a kwance akan three seater yanajin shigowarta amma be motsaba kan kujerar dayake taje ta zauna daga karshen kafafuwansa ji yayi jikinsa ya kuma mutuwa
A hankali ta kai hannu ta dan matsa yatsunsa na kafa taji yayi shiru bece mata komai ba Dan haka ta cigaba da matsa yatsun kafarsa a hankali
"ILHAM"
Taji ya kira sunanta a hankali
"Na'am Yaya Jalal"
Ta amsa masa
"Wane irin turare ne wannan kikasa?"
"Me turaren yayi?"
Ta tambayeshi
"Ji nayi ya kashemin Jiki, kamar ya karamin ciwon kai"
Abun yabata mamaki dataga be hantareta bako ya koreta
Kashe murya tayi cikin shagwaba da iyayi ta fara magana
"Haba Yaya Jalal turaren da kasanni dashine fa"
Mikewa yai zaune tare da fadin
"No ILHAM this one smells different"
Kusa dashi ta matsa ta kwanta akan kafadarsa
"Kaine dai kaji haka amma ni ban canza perfume ba"
Dan tureta yayi kadan ya Dan kalleta "
dakkomin Wayne a fridge ki hadon da cup"
"OK angama my J"
Ta mike tanata karairaya, tare da mamakin wannan sakin Jiki da Jalal yai da ita haka
Shikam da ido yabita yanajin kaman ba shiba
Wayne din takawo masa ta bude ta zuba a cup ta mika masa ya Sa hannu ya karba itakuma ta dawo kusa dashi ta kwanta a jikinsa
Hannu ya mika ya dakko remote ya kunna Tv
Yana kunnawa yaci karo da fuskar Jalila
Tana murmushi tasha hijjabi blue ga farin glass tasaka ga sufiku a gabanta na karatu gani yayi kamar shitake kallo
Gabansa ne yafadi yaji tsigar Jikinsa ta tashi
Share please
More comments more typing.................
Ina alfahari daku masoya wannan novel
Irinsu
Jamila
Zakiyyat
Ummu hanif
Mabruka
Zainab
Da wannan tsofaffin Fatima zahras
Da duk members Na ABDUL JALAL NOVEL FANS
Wanda na fada da Wanda ban fada ba nasan daku ina alfahari daku
[8/31, 8:26 AM] Safiyya:
_ABDUL
JALAL_
(2020)
_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)
PAGE-