← Book details Zayyan Zeeyat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 5

Sashe 1

Zayyan Zeeyat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```

Godiya ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Ina godiya ga Allah daya bani baiwar rubututa littafai Dan bada tawa gudun muwa ga Al'umma

_Ya Allah kaimun tsari daga sharrin mak'iyana Adik inda suke nakusa Dana nesa, Allah kasansu Allah kafiddani shairin su Ameen_

_SADAUKARWA GADIKAN ILAHIRIN MASOYANA NA DUNIYA🌎🌏🌍 INASONKU ALLAH YABARMU TARE INASONKU MASOYANA🥰_

*WANNAN K'IRK'IRARREN LABARI NE IDAN YAZO DAIDAI DA RAYUWARKI TO KIDAURE KIMUN AFUWA SANNAN KID'AUKE DARUSSUKA MASU KYAU DAKE CIKI MARASA KYAU KUMA KI WATSAR KODA YAUSHE BURINA NA FAD'AKAR HAD'IDA WA'AZANTARWA SHINE BURIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 ALLAH YASA MUGYARA KUMA ALLAH YASA MUDACE*

*Wednesday 7/12/2022 December*

_BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_

Free 🅿️ 1 to 5...

.................................. Kasa d'auke kyawawan idanuwansa kan wata matashiyar budurwa dake k'ok'arin hawa kan napep yayi,

Magana Salif take tamasa amma Sam hankalin handsome man d'in baya gurinsa yana kan wani gurin daban,

Kallonsa salif yayi Nan yaga meke damunsa dahar ya kasa sauraren sa haka, Maida kallonsa gurin da yake kalla yayi baiga fuskar matashiyar budurwar ba Dan harta shige amma ya hango bayanta, tana sanye da Wani yadi fari sai k'yalli yake,.

Wucewa sukayi sai A sannan Handsome man d'in ya sauke nannauyan numfashi wanda saida Salif yajishi,

Hunmmm"Wato Akwai Aiki Akace Saran dawa da hak'ori yanzu kadawo hayyacinka muyi maganar harka samu katafi? Ko a'a still kallon kake,"?

Dariya Nawar yayi had'ida cewa"Abokinmu ya kamu rana tsaka wllh saidai kash nibanga fuskar wannan masa'ar ba da dik ta kwashe Attention d'in jarumin maza nantake,"

Tind'azu baiyi magana ba kawai yana Tina yanayin yarinyar be amma gaskiya ta had'u,

Furzar da iskan bakinsa yayi kafin cikin sweet voice d'insa yace"Kuncika surutu Ni zanwuce kusame ni Office mayi discussed Akan maganar,". Baijira Ansarsu ba ya shige motar sa yabar wurin.

Dariya kawai sukayi dik da yazo Akan maganar Wani yaron company ninsu daya b'ata Amma ganin Wannan yarin yar ya hargitsa masa komai,.

Salif yace"Allah yasa dai ba Aljana bace dan ni banganta ba kuma baisan munada wata budurwa unguwar Nan ba,"

Nawar yace"kodai mene nan gaba zaifito nima zanwuce saimunyi magana kawai,"

"Okay kagaida madam da boy," cewar Salif

"Aha zasuji saimun had'u"...........

*WAYE ZAYYAN?*

Yaro matshi maiji da dukiya ilimi kyau izza, d'ane ga Alhaji Bashir wada petrol and gas wanda Nigeria ke damawa da mahaifinsa domun Akwai naira ga basira, Alhaji Bashir wada Yana da mata d'aya tak yara 4 maza 2 mata 2 Inda Zayyan shine babban d'ansa Yaro matashi wadda Ak'alla yanzu zaikai shekara 30 Saidai haryanzu baiyi Aure ba dik da kullum maganar Auren iyayensa kemasa Amma yakance lokaci yake jira kullum suna Addu'a Allah yanuna musu Auran d'an nasu, d'ayar k'anwarsa Nawal dake bimasa itace ta Aure Abokin sa Nawar wanda Ayanzu sunada yaro d'aya Affan wadda yaci sunan baban mijinta Nawar,. D'ayan Mannir yana waje yanzu haka yana Aikin soja, sai Autar su Ihsan wadda k'arama ce sosai yanzu take nursery 3 dika shekarunta bazasu haura 4 ba... Gidan Alhaji Bashir wada gida ne maitarbiya wanda hakan zaibaka mamaki ganin dik k'ud'insa yaransa basu b'aci ba ga taimakon talakawa Wannan yasamu me bisaga kyakykyawar uwa dasuka samu Hajiya Ameena kenan......

(Dama idan yara sukayi tarbiya to uwarsu ce sila haka itama idan zaku bincika IYAYENTA nada tarbiya suma nasu nada... Allah yabarmu da iyayenmu yak'aramuna ilimi)

Zayyan handsome man ne yanada kyau wanda har gida yaran manya ke kawo tallan kansu gareshi Amma baya kulasu hakama gun Aiki waya Ako Ina yaje saiya samu y'an Mata saidai baya bada fuskar su kusanceshi, dik da dukiyar ubansa hakan baisa yayi karatu yanemawa kansa Aiki likitanci ba b'angaren Idanuwa ya k'ware sosai har duniya tasanshi..................

Wash nagaji wllh kugafarce ni zan huta...

Sharin✔️✔️✔️ fisabilillah

Copy❌❌ kada kiyi
Allah ya Isa idan kikayi.

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

*WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948*
*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```

Free 🅿️ 6 to 10

.................... Tana hawa kan napep d'in direct gidan mahaifiyarta tanufa dama can gidan Aunty Salma ne taje,

Da sallama tashiga madaidaicin gidan Mama dake tankad'a garin masara natuwon yamma,

"Mama Wai yauma tuwon masara Kuma still," tanad'an tura baki tayi maganar had'ida wucewa d'akin nasu tacire hijab d'inta tafito waje tana cigaba da mitar tuwon da za'ayi,

"Dalla matsa wuce kifara Aiki yo mema yadawo dake yanzu? Ina ita salamen,"?

Cewar kaka dake b'alla goro tana gyara zamanta,

"Haba kaka wallahi nasan dika Aikin ki ne Ace kullum sai tuwon masara gaskiya Nikam yau bazan cishi ba,"

"Ja'ira ko ubanki daka uwar taki dikansu dashi Aka renesu kema haka"

"Hunmmm nidai banda ni kuma ba inda zandinga cin masara Kullum wallahi"

"Idan mijinki Yana cin masarar fa,"?

"Allah yaki yaye, Kinga kinda meni da surutu Aunty salma taje Asibiti kuma ko yanzu ciki ne da ita Wai shine takeson nakoma gurinta da Zama kafin tasami k'arfin jikinta"

Mama tace"shikenan Allah sawwak'e,"

Da Ameen suka Ansa..

*WACECE ZEEYAT*

ZEEYAT y'ace ga Malam bukar yajima da rasuwa Aisha sunan mahaifiyar su su uku me kawai Suka Haifa Malam bukar yarasu rashin uba baisa tarbiyarsu ta b'aciba dan Mama na k'okari dasu sosai, Samir shine babba sai Salma dika sunyi Aure sai Zeeyat kawai ta kammala karatunta da taimakon yayanta Samir tasamu Aikin koyarwa,. Zeeyat k'yakykyawa ce ga ilimi sannan sam Abunka baya tsone idanta shiyasa take burge mutane da dama,.

_MUNDAWO LABARIN_

Sam yarasa sukuni tinda yaga wannan budurwar, Shiga k'aton palourn nasamu yayi da sallama y'an Aikin saigaidashi suke d'aga musu hannu kawai yayi yazauna kan 1-ster dake palourn rintse idanuwansa yayi take suka fara haskomasa Wannan k'yakykyawar budurwar, ko Ina zanganta yanzu kuma"?

Tanbayar da yajefawa Zuciyar sa Kenan,

Ihsan ce tafad'a kancin yarsa tana fad'in "brothers yau Aka kawo muna sabuwar Aunty tamuna karatu Kuma maik'yau ce tana da.."

"Is okay Ihsan, Kincika surutu tana muku karatu kuna ganewa aishi kenan ko,"

"Brother gobe Kai zaka kaini school saika ganta ko"?

Mik'ewa tsaye yayi Yana sauke ta jikinsa Yace,"Oya go read your book kada Aunty tadake ki," baijira maganar ta ba yabar part d'in duka yakoma nasa Dan yasan Ihsan badai surutu ba yanzu idan yabiye ta saisu wuni haka bazata damu ba,.....................

_Kumun Afuwa ganin page d'in k'ad'an wallahi inada matsalar ido ne yanzu kutayani Addu'a Allah yaban lafiyarsu._

_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

Whatsapp number 07064904617 or call 07031012948
*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```

.....................

Page 11 to 15

...... Zeeyat! Zeeyat!! Zeeyat!!! Aunty Salma ke kwad'a mata kira ganin 7:30 Bata fita zuwa makaranta dama Nan baya Take karantawa A *NI IMA INTERNATIONAL SCHOOL* Makarantar k'ud'i ce Mijin Aunty Salma sani shine ya nemamata Karantarwa Acan mijin Aunty salma ba mazauni bane wannan dalilin Yana d'aya daga cikin dalilin Zaman Zeeyat gidan,.

"Na'am Aunty Ina zuwa Ina wanka ne!"

"Kai Zeeyat tind'azu wankan ne saikace Mai sauya fata haba kinsan makarantar kud'ice fa bazasu d'auke wannan sakarcin naki ba kiyi sauri koni da nake d'auke da lalura ga yarinya harmun shirya amm ke kina can kina bak'in nakin naki,"

Fitowa tayi bayan tashirya cikin farin yadi hijab d'in ta har k'asa dama shigarta kenan shiyasa take burge wasu daga kamilallun mazan dake school d'in harda na unguwa ma,

"Gani Aunty kinfaye mita kamar Grandma tacika mitar Abu jiyafa bankwanta da wuri bane shiyasa Ina making wasu Assignments d'in su ne sheyasa Amma badan hakan ba taya zaku rigani shiri"
Tak'arasa maganar tana k'urb'a tea daga tsaye,

"E munji d'in munada mita amma Kuma bazaisa kiyi zuciya ki gyara d'in ba, shiyasa gakinan Kullum sai k'arewa Kamar kud'in guzuri saboda baki tab'a tsayawa kici Abinci hankali kwance saidai tsai-tsaye,"

Jan hannun siyama y'ar kimanin shekara 4 tayi itace y'ar Aunty salma tafarko tace,"Muntafi Auntie kimana samosa kafin mudawo, Muna sonki Aunty.. had'a baki sukayi gurin maganar itada siyama . suna barin gidan,.

Girgiza kai kawai Aunty tayi tace Allah ya tsare munku INASONKU Nima da murmushi tayi maganar,.

Suna fita suka Sami napep Suka wuce.

*************

Brother! "Ni katashi yau Kaine zaka kaini school tinda daddy zaidawo kuma idi driver yatafi d'auko shi airport uncle katashi,"

Kansa tahaye tana cigaba damasa ihu Akunne,

Mik'ewa zaune yayi had'ida dafe kansa dake Sara masa sakamakon ihun da take masa Aka,

D'aure fuska yayi cikin fad'a yace," Ke bana hana ki fad'owa jikina haka ba kiwani zo kitadani daga bacci kinamun ihu Akunne dubi har kin sakamun Ciwon kai, dik Ina ma Aikatan gidan nan daba Wanda zai kaiki school saini Oya get out of my side!,". Cikin masifa yayi maganar
Chapter 1 · 0% Book details