← Book details Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 11

Sashe 7

Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Darana tsaka Yaseemin Tare da mahaifiyar ta suna zaune Tana mata tsifar kayi, Tace nikam 'yata na tambaye ki Mana har yanzu yanzu kabiru yason yarinyar nam kuwa Dariya tayi tace Ai mama sai Abunda ya k'aru ma mahaifinta baya sonka yaci zarafin mahifan ka amma kak'i hakura da ita ni ganinake Anya ba tsaface yaya kabiru tayi ba kuwa mama?.

Haka sukacigaba da hirar su, Bata nunawa mahaifiyar ta Itama tana tsananin son *“KABIRU*, Ba Ta shata mata kitso mai kyan gaske Fitowa tayi Tana zuwa falo ta tarar da kabiru shikadai yana kallo tazo gefen shi, Tace Nayi Kitso duba kagani yayi kyau?.

Hankalinsa nakan tv, ta sake magana ranta ya baci ta tashi ta kashe tv Ya kalleta yayi murmishi yace A yayi kayu sosai Amma duk haduwar sa baikai na Amaryata ba, *“Zainaba* shak'a tayi tace Bawaninam wana kannata kamar naka anam kaduba gashina har gadon baya.

Gwalo yamata yace A naji Dukda haka ma ai Tafiki, Ni nagagara gane miki kwana biyunnam Fa zansa ba miki Antin naki zainaba ne kike Aiban tawa agabana.

Tura baki tayi tace Allah yasauwak'e banafatan ganin wannam ranar Waikai meka gani a tattare da ita kanace mata nekam, harar ta yayi yace diri da iya zance da kalamai masu kwantar da hankali ga dattaku gata da hak'uri sannam da rik'oda adini kindai ji Abubuwan dasuka sa na lik'e mata.

Murmushi tayi ta ce to *romio* sai ciwon zuciya yakamaka ta jawo munyi rashika kaga kuwa wallahi Bazamu kyale ta mukuma, kaga tafiya ta nikam tafiya ta kamayi tana dingisa kafafa *Kabiru* nace mata gurguwa.

*“Zainaba*, Kam ina tashigane tin lokacin da mahaifinta yayiwa mahaifin kabiru kurar kare had'e da munanam kalamai bamusake jin labarinta number ta bata tafiya Wai shin k'arbewayar mahaifinta yayi kokuma Ta hak'ura da *“Kabiru ne, To masu sauraro Muhadu A feji nagaba danjin yadda zata kasance.

♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥
*ZAINABA Y'AR GATA*
♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

*(RICH AND POOR..)*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

BY

*KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

*11=15*

*“Zainaba*, Kam ina tashigane tin lokacin da mahaifinta yayiwa mahaifin kabiru kurar kare had'e da munanam kalamai bamusake jin labarinta number ta bata tafiya Wai shin k'arbewayar mahaifinta yayi kokuma Ta hak'ura da *“Kabiru ne?.

“Kwance take kan Wani makeken Gado Daka ga wannam Gadon dolene Kaji Azuciyar ka ya maka saboda had'uwar Gadon Latsa wani *rimote* tayi gadon yayi k'asa kadam Da ita ta na kallon sama tayi zugum, Ta ce baba meyasa zaka yi haka Yanzu kasa banida idon kallon, *“KABIRU*,wayata ma na k'arya layina Na sauya sabon sim saboda tsabar Kunyar da wana ido zan kalleshi Irin wannam cin mutuncin damai yai kama hawaye ne suka fara bul_bulowa daga gurbin idaniwan ta K'ira taji Ana Zainaba! Zainaba!! Am sawa tayi Tace Abba Ganinam zuwa ta share hawayen ta.

Daga nesa tataho ta durk'usa Tace Abba gani, Kallonta yayi Yace zainaba Kizaba Koni, wan chan Matsiyacin K'afarsa daya nakan daya yana girgiza ta Tayi shiru takama hawaye, Ta juyo ta kalli mahaifoyar ta ta fashe da kuka ta ce mama na, Kallon ta tayi mahaifiyar ta_ta tayi murmushi ta girgiza kai, Ta kalli mahaifiyar ta ta kalli mahaifin ta Budan bakin ta tace Nazabe ka baba Duk abunda kace shi zanyi Amma ina son *KABIRU*, tashi yayi Afusa ce Mari Kake ji tasss, guda d'aya mai zafin gaske Ta ke yatsun sa saida suka fito A kumatunta Ya rik'ikai yace gashinam kin jawo Na mareki.

Daukanta yayi suka tafi Asibiti Likita ya bata magunguna suka dawo gida, Tawuce dakin ta Washe gari da sassafe Ya sakata ta shirya kayanta tsaf, Yace Zainaba dagani Har Mahaifiyar Ki Zamubar Cikin Adamawa, Fashewa tayi Dakuka ta ce Baba idan har dan kabirune Namaka Alk'awarin Bazan sake jayayya dakai ba Akan shi Amma kabarmu muyi Zaman mu Anam Inda zakakaimu Bazamuji Dadin zaman shiba kamar Wajen da muka saba zama.

Kallonta yayi yace Tafiya kam ba bu fashi, Suka had'a kayayya kinsu Iyaka nasawa sauran kuwa ko cokali basu dauka ba, Wata mota ta musamman yaciro daga wani waje cikin gidan su Mai dudun gaske ga k'arfin tsayi, shiga motar sukayi Sunfara tafiya zainaba ta juya tana kallon gidan su, Sun fita a gate kenam, Tace Baba nayi mantuwa Yace Me kika manta fada mini Naje nadauko miki Murmushi tayi Tace abarshi kawai nafasa ma, Tafiya suke baji ba gani Har bacci yadauki Zainaba, chan ta farka ganin su tayi Suna ta tafiya Kan wani dutse Mai tsahon gaske, Taba mahaifiyar ta tayi tace Nam kamar nasaba ganin sa Ahoto murmushi tayi Tace Wannam Hanyace dazata kaimu izuwa garin *(MAMBILA)*, shiru tayi Tafiya suke tana ta kalle_kalle Wajen Gawartaccen waje ne Ga ni'ima a wajen Saidai Wajen Akwai sanyi Sosai.

DA yamma lisss.

Sun samu Sauk'a Asalin cikin garin mambila, Kafin sufita Suka saka safa ak'afafuwan su Sannam suka saka manyan riguna Dazasu musu kariya daga sanyi, Saka k'afa “Zainaba, Tayi tana fitowa Taji Wani Sanyi na musamman, tana juyawa taga wani makeken Gida ta ce Abbana Wannam shine gidan Murmushi Yayi Yace Shine, Shiru tayi Tanifi gate Tana bide K'ofar Gate din Gidan Tashige kafin Suk'ariso taga komai Anriga An tanadeshi, Zubin gidan Bashida maraba da nasu tsohon Gidan.

Kwanaki Hudu sukayi Batare da lek'owa waje sunyi ba,😂 Arana tabiyar zainaba ta fito Ta zauna Abakin Gate Tayi Tagumi Gaba k'idaya Garin Baya mata dad'i Gasanyin tsiya Tana zaune Tayi Ta gumi tana zubda hawaye Tana cikin wannam Yanayin ne Kawai Ta ciro wayar ta Harta Dan na number,KABIRU sai tafasa ta gogeta.

Haka tazauna tin batajindadin Garin Haryazama Ta saba.

Unguwar dasuke unguwace ta masu, Hali Kowa harkar gabansa yake, Ba mai shiga harkar wani Watarana *“Zainaba,* ta fito Sai waige_waige take Chan ta hangout Wata Budurwa Tazo zata wuce Zainaba tace Jimana k'awata tsayawa tayi ta ce sannu Amma bak'uwa ce ke A nam Unguwar Ko?.

“Zainaba Amsa mata tayi Da A bamuwuce Sati biyu dazuwa Garin nam ba, Ta sake cewa dan Allah Ina zan Samu Awara Tintsirewa tayi da dariya Ta ce, Ai Kuwa Banam kusaba Idan ma Zakisamu, Shiru tayi Ta ce To Idan kinaso Muje sai Na nuna miki Amma kafinnam Zamufara Bin kasuwa Zandanyi Saye sayen Abubuwan Kayan girkine Sati sati nake zuwa Zainaba tayi shiru Ta ce A'a na hak'ura kijeki kawai Abbana bashida Dadi fitowannam Dakikaga nayi Bawai Dasanan shi nayiba Kijeki kawai murmushi Tayi Ta ce, baza ayi hakaba Zan siyo miki Idan Na samu Zan sayo miki kamar na nawa Kike so?.

Zainaba ta ce A to kona 15, d'ari da hamsin ma ya isa ciro 500 tayi Ta mik'a mata tace a'a kibarshi kawai Zan sayo miki Idan na dawo zan Neme ki, Zainaba ta ce A'a ga number ta nam Kema kibani naki Ta ke sukayi musayar lambar waya Ta wuce tayi tafiyar ta Zainaba ta koma cikin gida zaune suke tare da mahaifiyar ta jitayi wayar ta na k'ara ta na dauka ta ce Kifito ki karba ta ke taji wani farinciki ya kamata sosai Fitowa tayi ta k'arba saida sukayi tadinsu sosai Dama tinzuwan su ita ma tsahon wata shida kenam Ko k'awa batadashi Zata tayi zainaba tace Ai kuwa Kifadamini sunam ki Kafin Kitafi.

“Murmushi tayi Tace Sunana, “BILKISU" ke fa tayi murmushi Itama Ta ce Nikuma sunana “ZAINABA", sukayi bankwan ta shigo da leda A hanunta Ta baje tasamu guri ta zauna tace umma yaukam nasamo Awara Murmushi tayi Ta ce A'a nikam na k'oshi kici kayan ki.

Zainaba taci ta k'oshi ta d'ora zuwa mai dumi akai, Sannam ta cigaba da kallon ta Batada aiki Saidai taci Ta kwanta shine Aikin ta, Mahifin ta kuma Yakan tafi wani lokacin yayi sati Baidawoba Saboda yanayin Aikin Gwamnati.

Tsakanin *“BILKISU"* Tare da *“ZAINABA"*, Kawancen nasu Har yayi k'arfi sosai Watarana tazo gidan su zainaba bilkisu suna zaune, Tayi Tagumi *“BILKISU"*, ta ce k'awata tinanin mai kike Murmushi Tayi Tace *“KABIRU"*, kallon ta tayi Tace Hmm Soyayyah kenam Kunrabu kenam Ta gyad'a kai tace A A'a Bikisu ta ce To fa Maiyafaru K'awata.

Ajiyar dogon numfashi, “ZAINABA" tayi Tace Labari nai mai tsaho Tafara bata labari tiran tiran Tana bata labari Saida tayi k'walla Ta ce k'awata Kenam Ai haryanzu kinada damar Da zaki gyara soyayyar ki Amma saidai Kuma mahaifin ki, Ne kinga shine Baya sonshi Mahaifiyar Kuma tana sonsa sosai.

Nikuma nawa labarin yasha banban da nayi, Natashi cikin Gata Nakasance Nikadai ne Agaban Mahaifiyata, Tafashe da kuka tace *“ABBAKAR", yaso ni Amma daga k'arshe na fahimci Ba sona yake tsakani da Allah ba Soyake Ya Sure ni Ya mallake dukiyata Da na gada, Watarana Muna tare da *“ABBAKAR"*, Yace Bilkisu Nace na'am mijina ya ce dukduniya babu wacce nakeso fiye dake Zansoki har k'arshen rayuwa ta kece Bugun numfashina, Amaryata Dajin wannam kalamin Nashi Nayi murmushi nace masa nima haka Ahaka muka tafi dashi Mahaifiyata Ta yadda Dashi Sosai duk lokacin dayazo zance saiya Shiga sun gaisa Ta A haka ya sace zuciyar mu baki d'aya nida mahaifiyata Maganar Aure Hartakai Ga wake Baffana K'anin mahaifina Nafada masa Komai da komai Ya kalli *“ABBAKAR"*, sosai yayi murmushi Yace To naji Bakomai kutashi kuje Yatashi zaitafi Baffana ya tsadashi yace kuje kawai zanyi shawari.

Akwana Atashi, Ya turo magabatan shi Sukazo Aka k'arbesu Hanu bibbiyu Bayan An amince Masa An basa ni, Daga baya ina zaune *“KAMAL", Yazo hargida ya sameni Ina kallon sa nayi murmushi Nace masa Kamal kenam Ba aganin ku ina kashiga number kama bata tafiya murmushi yayi Yace Haba Sister *“BILKISU"*, Ai nayi tafiya ne kuma wayata saitafadi na sauya sabon layi nema nadawo kenam Mama na ta cemini Ai Kinata nemata Shine nazo kuma natarar Wai An kowa goron tambaya Da kayan lefe Rana kawai ya saura A saka musha buki, murmushi tayi Tace A wallahi Gashi ni zanrigaka kai har yanzu ko budurwar ma babu Kuma ahaka kullum kake cewa zaka rigani Aure, Dariya yayi yace sister kenam Dukda kece gaba dani yanzukam na baki gari na yadda zaki Rigani Aure.
Chapter 7 · 0% Book details