← Book details Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 11

Sashe 3

Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tajira_Tajira harta gaji Bataganshiba Shiru tayi tace Lafiya kuwa banga Mutuminnam ba, balafiya ba dai kam Kwanciya *"Kabiru, yayi yana famar murk'ususu Zazzabi ya galabaitar dashi k'irar wayar tayi Shibesan ma ana k'iraba saboda zafin zazzabi Mahaifiyar sa ce, ta d'aga suka gaisa take tambayar ta shin me Qatar bay a Ku sane, murmushi tayi tace Ai gashinam yana kwance ba lafiya, Ta ke Zainaba ta ce subahanallahi Kihada ni dashi Girgiza kai tayi ta ce, Yata Baya hayyacin sa Kibari zuwa anjima ki k'ira kinji zainaba tace To Mama takashe wayar karfe 7:17 dai_dai na dare k'irar wayar tayi har Sau uku Ba'a dauka ba washe gari dasafe tasake k'ira *kabiru Yanafarkawa ya daga wayar yayi Sallama suka gaisa Yayi mamaki Dayaji zainaba tace masa yaya jiki.

Sunacikin tadin su tace Insha allah zanzo na dubaka koda yamma, kabiru yace A'a nama warke basai kinzoba murmushi tayi tace Bakaso naga gidan naku ne, kabiru yace A'a bahaka bane Nima zanzo Anjima karkidamu Murmushi tayi Tace Kaida bakada lafiya Kabari jikin ka yawar_ware kaji.

Sati d'aya yayi Amma jiki yaki ci yak'i cinyewa Dalilin haka yasa zainaba ta taho har *WURO HAUSA", Aunguwar su tana zuwa Sukagaisa da mahaifiyar sa Ta je tadauko likita har gida yabashi magani yamasa wasu Allurai Bewuce kwana ukuba jikin sa ya warware kamar Bashiba Yayi kwalliya ya kama hanya sai Unguwar su zainaba.

Yanazuwa ya tarar da ita Zaune Ak'ofar gida tana hiradawani tanaganin Sa, Tataso tazo wajen sa Wanda suke hirara ransa yayi matuk'ar naci Abusace Yataho ya ce Haba Zainaba Wannam talakan kike saurara mai zai tsinana miki dubeshima wari yake, murmushi yayi yace A'a bekama kafadi hakaba danasam zakazo nidana bari sai gobe, Cikin fushi yace Kai Aibaka isa mu hada budurwa tare Dakai ba talakan Banza Kaduba Akeke kake zuwa wanda kudin keken ko zoben hanuna bazai sayaba.

Shiruyayi *"Kabiru yace Da ace kafahaimceni daduk hakan bazata faruba, sannam Alziki da Wannam kuma nima Allah zai bani Saboda haka Kadaina cimun fuska Yanda kakeji da zainaba taka ce to nima tawace Kuma tawace nikadai Juyawa yayi yashiga motar sa ya fizgeta yayi tafiyar sa.

Kallon shi zainaba tayi Tace nibataka bace, Banason mutum mai son Tada husuma tatashi tayi tafiyar ta tindaga wannam lokacin koda yak'irata Awaya bama ta d'agawa Daga k'arshe Da abun ya dameshi cire sim card dinnashi yayi ya Aje shi na tsahon sati kuku ko sakashi ba'a yi Awaya....!

Washe Gari Yayi wanka, ya tattaro 'yan kayayyakin shi masu tsafta yataho ya durk'usa yagaida Mahaifiyar sa yace Mama Tafiyar nam tatashi Zanjeni Wajen *"BAFFANA*, murmushi tayi tace Aibazan hanakaba Kabiru Amma zakasha tafiya shiga d'aki tayi ta dauko ragowar 'yan kudaden ta dabazasu wuce naira dubu d'aya ba ta mika masa ya maida mata da kanyata ya ce, haba Mama na Kibar kudaden ki Idan naje chan zanna yiyo miki Aike tafashe dakuka ya rarrashe ta sukayi bankwana.

Tafiyar Awa Shida sukayi Kafin Isar Su *Garin kebbe*, Yana isa suna sauka atashar mota Ya daga wayar Baffan sa Daniyyar zai k'irashi jiyayi An wanke shi da kwatami Besan lokacin daya katse wayar ba Motar data watsa masa Ruwan kwata, Tana fakawa Yataho Ya tsaya daga gefe Wata zankadidiyar budurwa ce tafito daga motar Fiskar ta sanye da Tabarau,(Gilashi) Magana yamata yace Ke Bakida tarbiyya ne kinwatsa wa mutum Ruwan kwatami amma bakisan kibashi hak'uri ba ko?.

Juyowa tayi taimasa wani irin kallo Nagadara Tace Ayya..! To kayi hak'uri kaji Bude jaka tayi Taciro 10k ta zo tace Gashi kaje Ka sauya wasu kayan, besan lokacin daya ja Hanun ta ya wanka mata mari tasssss...! Ba gabakidaya Kowa dayake wajen saida ya zaro Ido rik'e kumatun ta tayi idon ta na hawaye tace Mari Na kayi Ko To yau zanga waye Gatanka A kaf Cikin Garin (KEBBI), murmushi yayi yace mezaki iya daga wayar ta tayi Cikin shagwaba Tace Dady kana Ina Yace Lafiya kam Fashewa tayi Dakuka Tace Inason Mota d'aya na yan sanda wani ne ya marini Haka kawai.

Wasa gaske Kabiru Jiyayi Hukuma sun nadeshi basutsaya dashi ko ina ba sai ofishin 'yan sanda Kabiru Yana zaune bece komai ba tamaida stetment, Tafadi k'arya da gaskiya.

Wani Contabul ne yataho ya kalli kabiru yace Kai dan saurayi meyakaika Marin Wannam yarinyar Gaskiya na tausaya maka Gashi har Cinhanci dabayar maitsoka wai A ajemata kai har zuwa lokacin da ka shirya bata hak'uri Kadurk'usa har k'asa murmushi yasakeyi yace nibak'one Kubani wayata Zan k'irawo baffana ya zo yayi belina Anam fa sukace ina ai bazancen beli hakadai kabiru yacigaba dazama A cikin magar k'ama harna tsahon Kwana hudu.

Rannabiyar ne, babban D.P.O daya ziyar ci Ofishin ya tarar da Kabiru, yasa akafito dashi Ya tambayeshi Shin wajen waye kazo garin kebbe Sannam kana bak'o maiyakai ka rigima.

Kabiru ya zayyana masa Abunda ya faru, dayaji Haka yabashi Hak'uri akadauko wayar sa Aka bashi, Acikin chaji ofishin 'yan sanda ya k'irawo Baffan sa wato *"ALHAJI BADAMASI*, yana isowa ta ke D.P.O yatashi suka gaisa yace wa Alhaji badamasi wannam d'in dankane Yace A danane Dan yata ce, Nayi nayi Yadawo wajena tare da mahaifiyar sa amma sai Kwanaki yak'irani yace yana zuwa ya kalli kabiru yace tashi muje Kaji Kabiru tashi Yayi suna tafiya yanata sak'e sake ina zaosamu budurwar nam Ya rama abunda ta masa, Tafiya suke Amota Amma komagana bayayi Suna shigowa Cikin Gida wata k'aramar yarinya ya hango tanaganin sa tataho dagudu ta rungumeshi tace yaya sannu dazuwa Yayi murmushi maganar da tamasa ne yasauk'o da gabaki d'aya A tsume yake.

Yanashiga cikin falo, matar baffan sa ya hango tana ganin sa tataso yagaisheta Tace Kasa gaba ki d'aya mun rikice murmushi yayi yace *ANTI LARABA*, bakomai ita tadauk'i jakar sa ta bude wani d'aki na musamman ta ce kashiga bari wannam fitsarariyar tazo zata tayaka sauran gyare_gyaren dakin kaji ko Yace to Anti laraba Tana tafiya k'aramar yarinya nam mai surutun tsiya tataho tace Yaya Yace Na'am tace Kullum baba saiya bani labarin ku yaushe Ba ba zatazo duk'usawa yayi ya rik'eta yace kwannam zatazo Zakitayani aiki tace A'a Gaskiya Saikabani Minti Ko chakuleti, Dariya yayi ya bude jakar sa yaciro Sweet ya mik'amata.

Yazauna yana ninke kayayyakin sa sunata tad'i Lokaci d'aya sun shak'u da ita sosai Hango wayar sa tayi tace yaya Zanyi wasa, murmushi yayi ya bide mata wayar Tanata game Shikuma yana gyara wajen Ajiyar kayan sa.

K'ira ne yashigo wayar Tace yaya Ana k'ira yace juyo muga waye ne yana kallo yaga number zainaba ce, Yace Kikashe kicigaba da wasank Haka kuwa akayi har sau uku Ana hudunne Ta daga tasa Wayar A kunen ta Tace Yaya na Yana Aike Zainaba murmushi Tayi tace Toh 'yar k'anwata Antinkece Take Magana Kashe wayar Tayi Tace Yaya Antina Ce Naji Tana Kuka.

Murmushi yayi yace Kinji k'anwata rabuda ita Ta gasa yayan naki Tace To Tacigaba Da game d'in ta Kida kakaje Natashi Tace Yaya muguwa ta dawo.

Danaso sai sabon shekara zan sakeshi, Amma insha allah zanna kawo musu shi saubiyu a sati.

*07035610661*
Zaku iya tuntuba ta WhatsApp tawannam lambar kamal ne naku akoda yaushe Muhuta lafiya

♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

*ZAINABA Y'AR GATA*
♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

*(RICH AND POOR..)*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

BY

*KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

5=6

Murmushi yayi yace Kinji k'anwata rabuda ita Ta gasa yayan naki Tace To Tacigaba Da game d'in ta Kida kakaje Natashi Tace Yaya muguwa ta dawo.

Yayi murmushi yace wacece muguwar?, ta kyal_kyale dadariya tace *"Adda YASMEEN"*, kulluma saita dakeni Yace to fa muje Namata kashedi to Kama hanunta yayi Suna zuwa tatura k'ofar d'aki Yabiyota Abaya Idakuma Tana kwance tatoshe da Abun jin k'ida akunen ta Shikuma yana labe Abayan k'ofa tana zuwa Yarinyar Ta lallaba ta kashe kid'am Zumbur tatashi tace Ke yarinyar nam lallai yau zanga mai kwatanki Agidannam daman kin rainani Dariya tamata tace Yaya Na zai ramamini Ai Dajin haka *"YASMEEN*, Tayi wufa zata makamata Tayi maza ta koma bayan *"Kabiru, tace Yaya karamamin Zataci zalina, Had'a ido sukayi Yayi shiru Itama tayi shiru Yace ke?, i ta ma tace Kai meyakawa ka gidan mu?, shiru yayi Yace gidan ku kuma Tab..!

Kama hanun K'anwar ta yayi yace zomutafi Ranshi yabaci sosai Tahotayi Da gudu tatare K'ofa tace Kodai Kaine Yaya Kabiru kallonta yayi ya Hada fuska yace Bashi bane Ta durkusa har k'asa tace Dan Allah Kayi Hak'uri.

Budan bakin sa yayi murmshi yace Tafa, kefakikace saina durk'usa Agabanki gashi ke kika durk'usa agabana, tashi Tayi Tace To Nafasa bak'a hak'urin ma Ta koma Dabaya Yayi wucewar Sa, Yanazuwa Falo yatarar Da *ANTI LARABA"*, Zaune tana kallo Ya zauna gefe suna kallo suna hirar su, Chan *"YASMEEN"*, Tafito tana zuwa ta zauna tana harara *Kabiru*, yacigaba da kallon sa budan bakin *ANTI LARABA*, Tace ke *"YASMEEN*,kinaganin Shi bazaki gaishe dashi ba dan bakida kunya budar Bakinta tace Wannam Zan gaisar Hmm, Shikuma yayi murmushi Yace Anti laraba rabuda ita wacce batada aiki saicin zalin yar k'aramar yarinyar nam.

Fusata tayi Ita kuma k'anwar tata tana gefe tana wasanta Dasuka hada ido ya yimata gwalo harsau uku, Tashi tayi ta koma wajen Anti Laraba Tace Mama *Yaya YASEEMIN, ce take harara ta Kafin kace me ta Fusata Kawai Tasakuka Sukuma sika tintsire dadariya Tashi tayi ta wuce dakinta Tahaye Gado ta kama Kuka, Tashi Kabiru yayi yabita Abaya yanazuwa tace fucemin Daga Dakina Banason ganinka Murmushi Yayi Ya zauna nesa Da ita, Yace Yi hak'uri k'anwata Tsokanar ki muke Dajin Ankirata da k'anwata saita Share Hawayen ta tazauna Tace Shikenam.

Yawuce, Kayi hak'uri Besa ga laifin danamaka Kallon ta yayi yace Tab..! Ai saina rama zaro ido Tayi tace Ramawa kuma yayi dariya yace A'a "ta durk'usa hark'asa tace Natuba Kayi hak'uri Naga kai dan uwanane Idan kuma kanaga bazaka hak'uraba to kaje kayi Duk Abunda zakayi, Wani kalla ta masa ta harare shi Shikuma yayi murmushi yace, kinga ni bak'one Agarin *KEBBE*, ko zaki rakani In Allah ya kaimu gobe mudan zagaya gari.
Chapter 3 · 0% Book details