← Book details Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya yayi ya sake rubuta Mata yanzukibari zamuyi magana dazarar mun Isa inda zamu gyada Kai tayi Tace shikenam Tafiyar Awa biyar sukayi Har zuwa k'ofar gidan su zainaba Kwank'wasa gidan yayi Aka mar iso suka yak'arisa cikin wani falo na Alfarma.

Jim kadam, Yafito Yace kushiga mota muk'oma gida, Juyawa sukayi Suka sake cinhanya, misalin karfe shabiyu DA talatin DA hudu Na dare suna sauk'a yakalli kabiru yayi murmushi yace kabiru Na ba Abunda zaka buk'ata idai baifi k'arfina ba saika mallake shi sukayi bwakwana kowa yawuce bangarin sa.

Washe gari DA safe.

Amana Afuwa najina shiru dakukayi Ayyukane suka boyemu Yanzukam insha allah zakuna samun shi kan lokaci, saudaya ko saubiyu a sati.

♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥
*ZAINABA Y'AR GATA*
♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

*(RICH AND POOR..)*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

BY

*KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

7=8

Ya Kai d'an uwa/'yar uwa kayi iyaka k'okarin ka/ki wajen ganin ka kayutatawa Iyayen ka da sauran Abokan huldar ka, Iyaye bamuda tamkar su cikin fadin duniyar nam Koda kowa zai gujeka na tabbata iyaye sunanam tare ka mu, Amma saikaga wani Kullum yana cikin cusa musu bak'in ciki wani lokacin har suyi k'walla Ta kasani/ki sani duk mai k'untata wa iyayen sa bazai taba ganin harkokin sa suna tafiya dai_dai ba muzauna dasu lafiya susanya mana albar ka tabbas zamuga budi sosai A rayuwar mu, Allah yasaka muku iyayen mu kunmana komai babu abunda zamu ce daku saidai muce Allah yasaka muku da gidan Aljanna Amin.

Jim kadam, Yafito Yace kushiga mota muk'oma gida, Juyawa sukayi Suka sake cinhanya, misalin karfe shabiyu DA talatin DA hudu Na dare suna sauk'a yakalli kabiru yayi murmushi yace kabiru Na ba Abunda zaka buk'ata idai baifi k'arfina ba saika mallake shi sukayi bwakwana kowa yawuce bangarin sa.

Washe gari DA safe.

*"YASEEMIN"*, Ta fito Tana goge idanun ta juyawar dazatayi Ta hango *"KABIRU*, zaune yayi tagumi k'arisowa kusa dashi tayi takai minti biyar tana gaban shi amma sam taga kamar ya yi nisa budan bakinta tai magana tace yaya kabiru maiya ke damun ka?.

A firgice yadawo daga tinanin da yake yayi murmushi ya ce A'a Babu komai Girgiza kai tayi tace A'a ninasam Kanatinanin ko mahaifin wannam yarinyar da mahifinta bason ka yake ba kana tinanin yacewa baba zarafine kawai, nibanga wani Abun damuba ita kadaice mace A duniya kaje ka nemi wata mana Mahaifinta yanaji dakan sa shi mai kudine Wanda mu kuma talakawa ne Ammaduk dahaka muma ai munada na rufin asiri nidai inaga nin a tawa shawarar kawai kahak'ura da ita ni namaka Alk'awarin Zan samamaka 'yar gidan mutumci da karam ci Kallonta yayi ya gyad'a kai yayi murmishi yace tai maka kisamamini ruwa nayi Alwala yau nima na makara kamar ke.

Murmushi tayi tace Shikenam tatafi Ta dauk'o masa ruwa a buta ta aje masa Ta zauna gefen sa na dama yana Alwala yace kekin yi Sallar ne?.

Girgiza kai tayi tace A'a butar tawa nabaka idan kayi sai nima naje nayi ai yayi murmushi ya idar Da alwalar tashi ya mik'a mata tatashi zata tafi yace Dakata Anam zakiyi Ina kallon ki karkije ki kuskura baki kice kinyi sallah tintsirewa tayi dadariya tace to ai wannam halinku ne na samari, Tawuce tayi tafiyar ta Yatura k'ofar sa yashiga yayi Sallah.

Misalin k'arfe Shad'aya na rana kowa yana zaune A falo Anata hira amma kabiru yana d'aki ko fitowa baiyi ba, *YASEEMIN*, ta mintsine karamar K'anwar ta tace ke Akukuturu Jeki taso yaya kabiru Murguda mata baki tayi tace A'a bazan jeba ni kallo nake Tsawa tamata tace kitashi kitafi kona kashe kallon dakatar da ita mahaifiyar ta tayi Tatashi ta nufi k'ofar dakin sa tanazuwa tayi Sallamah taji shiru Ta tura k'ofa tashiga tana shiga ta tarar dashi Kwance Yanata famar Kuka murmushi tayi tace Nikam Mezan gani dan uwana kadaina kwallafa ranka akan abu Ba lallai bane kasamu abunda Kake so A lokaci d'aya saikasha wahala wani lokacin ma allah saiya jarrabeka da son Abu yakuma hana ka gwada ka, Kazamo mai tawakkali dan allah dan uwana kayi hak'uri dan allah ta ke itama tafashe da kuka tace Idan ka nayawan saka damuwar yarinyar nam aranka zata iya haifar ma da matsaloli mukuma bazamu juri ganin ka cikin damuba yaya Kabiru bazan iya jurar Ganinka cikin wannam halin ba tasake fashewa da kuka tayi ficewar ta tafita waje taci kukan ta tasa hanu tashare hawayen ta koma wajen mahifiyar ta cikin Fara'a ta danne Abun Acikin zuciyar ta.

Tana zuwa Tazauna gefen Mahaifiyar, *"KABIRU, kallon fuskar ta tayi tace Yasmeen yaya naga kamar idanun ki sunyi ja, Murmushi tayi tace Babata Wani k'earone ya shigamin idona Kabirune ma ya huremini Idona Murmushi tayi Ta kwalla kira *"KABIRU! KABIRU!! Har sau uku fitowa yayi yana sosa kai Ya durk'usa yace Anti Ina kwana ta amsa lafiya k'alau sannam ya sunkuyar da kan sa yace mama ina kwana Tace lafiya Wai dagaske Abune ya shiga idanun *"YASEEMIN, fadamin gaskiya kodai kaine ka mata laifi murmushi yayi ya girgiza kai ya ce A mama Na huremata Wannam kina kallonta sakalcinta yayi yawa Dajin Haka gabaki D'ayan su suka tintsire dadariya Suna cikin Dariyar Ne Saiga Alhaji Wata Dan uwan mahaifiyar kabiru Suka gaisa ya nemi gu yazauna kabiru na Durk'ushe a ka'asa yace Inason Wata magana Daku gabakidayan ku Duk Hukuncin da kuka yanke shikenam.

Shiru Yayi nadan wasu mintoci, Ajiyar zuciya yayi yace Kabiru Yace Na'am Baba yace Wannam Mahaifin Wacce kake son Ya tazar tani Tozarcin da zaiyi wahala na iya mantawa da shi A rayuwata.

Lokacin da muka sauk'a garin adamawa Mukakai Izuwa k'ofar gidan shi Saida nayi tinanin maganar da akafadamini Akan Bashida Kirki mutuminnam Yar sa kuma kowa na shedar ta 'yace Tagari tasamu tarbiyya sosai wajen mahaifiyar ta, alokacin dana shiga cikin gidan Ita d'iyar tashi ita ce tazo ta tareni ta durkusa har k'asa ta gaishe ni ko daga kanta batayiba da nufin ta kalli cikin k'wayar idona balle fuskata ba Awannam lokacin naji ta kwanta min Araina Naji Koda nawa ne zan kashe Dan Dana *"KABIRU, ya mallake ta a matsayin matar sa Bayan ta Kaini Wani masauk'i na musamman mahaifiyar ta tazo muka gaisa Ta kawomini ruwa nasha sun tarfeni Hanu bibbiyo Daga bisani Tadawo ta d'urkusa ta bani hak'uri tace Baba kayi hak'uri Abba na yana fitowa yanzu Kayi hak'uri bisaga jinkirin daya maka.

Nayi murmushi, na ce Ba komai tayi tafiyar ta jim kadam!, yafito saida ya k'are min kallo nina daga masa gaisuwa Cikin izzada gadara yace Kaine Mahaifin Wannam Yaron dayake zuwa wajen 'yata nace masa A tabbas nine Yanzuma nazo tambaya mar izini ne wajen ka Amatsayin ka na mahaifin i ta wacce ya ke so.

Wani kallo yamini, yace Befada maka Abunda nafada masa bane Bazan tab'a bawa matsiya ci 'yata ba Kaci sa'a kamin zuwa bazata ne bansan dazuwan ka ba da ko bata lokacina bazan yiba wajen sauraran sha_sha shu irin ku ba, Nayi murmushi dukda abun ya batamin rai sosai, Nace masa bekamata kayi Haka ba yarannam suna son junan su Banga wani Abun aibubu Dan d'an talaka yaga yar masu hali yace yana so.

Charaf yayi yace Lallai talaka idan har yazo gidana abu biyu be yakawoshi koyamin bauta na biyashi kokuma yazo neman na masara, Dan haka kadaina tsam_manin wannam had'in zai yuwu Natsani talaka.

Ta shi nayi A fusace jikina na bari nace To ai Shi Arziki nufin Abungiji ni Dan yabaka bawai muma Ya mata damu bane inamai bakashawara Kokuma ince Duk masu dukiya irin ka dasuke Cewa su bazasu bawa 'ya 'yan su talakawa, suna ruwa Karkamanta Idan Allah yagadama sai kabawa mai tarin dukiya Allah ya jarrabishi Gabaki d'aya dukiyar ta k'are Kenam zakaje kace Lallai saiya saki maka 'yar ka dan allah ka gyara halinka.

Bangama rufe bakinaba yasa hanu yamare ni tasss! Lakaci d'aya iyalin sa ta taho sukatar na rik'e kunci na na dama nayi shiru, Gabakid'ayan su kowanne jikinta yayi sanyi! Najuya zantafi yar tasa ta taho ta dur k'usa A gabana ta ce Dan Allah Baba kayi Hak'uri tsayawa nayi na kalleta ta fashe dakuka ta ce ni *"KABIRU, Nake so murmushi nayi na kalli mahaifin ta na girgiza kai nace mata Bakomai Tatashi tatashi Najuya zan tafi Ta sake bina tana kuka tace Karka Hana kabiru Shima yana sona Munason junammu.

Ya ga ma basu labarin kenam kowa jikin sa yayi sanyi yace ina mai neman shawari ne A wajenku wana hukunci kuka yadace Muzartar kowa yayi shiru baice komai ba.

Yayi magana har sau uku bawanda yace mai komai, Ya ambaci sunayen su d'aya bayan daya kowanen su yace duk hukuncin dayaga yadace shikenam, *"YASEEMIN, Ne tayi magana ta ce Abba Nibana goyon bayan Ace Yaya k'abir ya bar *"ZAINABA*, Cikin wannam hali Aganina Baikamata A biyewa mahaifin ta ba Tinda mahaifiyar ta da ita kanta suna son shi, Amma kuma Abba kai yakamata ka yanke hukuncin dakaga ya dace Tashi tayi Tana murmushi tace Zandan kwanta kaina ciwo yakemini Wucewa d'akin tatayi ta dura k'ufa ta sa kanta na kallon k'asa akan wani k'asaitaccen gado mai laushin gaske Hawaye ne kawai suke zubuwa daga idanun ta.
Chapter 5 · 0% Book details