← Book details Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 11

Sashe 10

Zainaba Yar Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Budar bakin kabiru yace Naga 'yar uwa tace murmishi tayi ta ciza baki Ta ce A'a niba jinin ka bace *Zainaba* ce Jinin ka ta juya zata tafi ya ce Yasmin Ki tsaya ki saurare ni Tsaya tayi Ta na kallon sama Tace ina sauraron ka, Tashi yayi ya zauna yace Badan halinaba A matsayina na mai laifi ki taimaka ki zauna kinji.

Zama tayi nesa dashi, ta ce to na zauna yaukuma wace k'arya za'a fadamin kuma idai kasan harzaka ambaci wannam yarinyar ko kuma akanta ne to karma kafara dan kuwa Natsani jin koda sunam ta, Murmushi yayi yace A'a Akan kine K'ara gyara zama tayi yace yasmin, Bawai na k'iki bane Ki fahim ce ni wani irin kallo tamasa tace dama kumaza haka kuke Dazarar mace ta bayyana muku Abunda ke cikin zuciyar ta cewa I tafa takamu da son ku dagawannam lokacin zaku tozar tata na gwammace da barin sonka nayi acikin ziciyata koda zaizoma ajalina da fada fada maka buk'ata ta Amma haka k'a k'ini Haba maza kidinga yimana adalci mana Gudun haka yakesawa yawancin 'yammata ke buyo damuwar su su barta cikin zuciyar su Amma kasani Hargobe Nidai ina sonka yaya Kabiru Amma nasam Kafison Zainaba fiye dani Komai ya wuce Ni zan hak'ura amma kasani kana cikin zuciyata Har abada mantawa dakai Abune mai matuk'ar Wahala Ba komai murmushi tayi ta share hawa yen da suke gangarowa daga kuma tunta.

Tatashi hartaje Bakin k'ofa Ta juyo tayi murmishi, Ta ce dan uwana Komai ya wuce Da dinnma bawai fushi nake da kaiba Kishi ne kawai irin namu na mata Na barka lafiya.

Kallonta kabiru yakama yi ya gagara cewa komai Ta fita kenam, Batawuce taku uku zuwa hud'u ba Ta ji Kabiru Yayi k'ara juyowa tayi A figice Ta taho yayi shiru taga kofin shayin a gefe A fashe Yace Haba kekuwa Baki fadamini ruwan shayin da zafi sosai ba ne, Murmishi tayi Tace Kaji wannam fa kodai tinanin ta kake Har kamanta ka d'id'ara shi Abakin ka kodai kana tinanin unty *Zainaba* ne kam?.

Tajuya tayi tafiyar ta, Kabiru yayi mamaki sosai Ganin yanda suke mu'a mala kamar da wasa dadariya Watarana suna zaune su biyu kabiru Yace wai nikam Natambaye ki mana dariya tayi ta ce ina sauraron ka a matsayin me nake Awajen ki, murmushi tayi tace d'an uwa mana kasan dai ni ba sa'ar ka bace nawuce Ajin soyayyah da kai.

Tintsirewa yayi da dariya yace, A haka kuma naga wata harda kuka, Ta ke tace banaso kadaina tinamin Abunda ya faru Baya dan allah ko so kake mu kuma Abunda ya faru da kenam ko?.

Lallab'ata yayi haka sukacigaba da mu'a malar su kamar da, Abun burgewa.

Yasmin, Ta dauki Kabiru A matsayin Dan u wanta, haka Tanaji Tanagani Ta Hak'ura DA muradin ta Danganin Ta farantawa Mishi Rai.

Zainaba Tashiga Damuwa Sosai bisa ga Abunda ta Aikatawa Kabiru, Zaune ta ke Tayi ta gumi..! A bun tausayi, K'yalla Ido tayi Ta hango Wayar ta, Ahankali cikin tsaro DA fargaba ta latsa lambar Kabiru, Tayi sa'a Alokacin DA wayar tashiga Tana hanun sa Dauka yayi yaji muryar mace, suka gaisata Ta ce Yaya kabiru Kayi hak'uri bisa Abun da ya faru ina mai Baka hak'uri.

Wani murmushi na musamman yayi, Ya ce Haba zainaba ni fahimci komai DA Komai, Karki damu Kinanam Acikin zuciyata juyawar dazaiyi kenam.

Yasmeen, ya hango A gefen sa tana murmushi, ta ce bazaka bani ita mugaisa bane?. Mik'amata wayar yayi Amma zuciyar shi na k'adawa tana k'arba tace Unty zainaba ya ya like?.

Amsawa tayi DA lafiya k'alau, Ta ce Yayana yana sonki Sosai Kirike mini shi Amana, inada tabbacin bazaki nuna gazawa wajen bashi kulawa sosai Unty zainaba.

Murmushi zainaba tayi tace Insha Allah zanyi iya ka k'okarina karkiji komai, Kidai kitaya mu da Adu'a mahaifinane Bashida Dad'i bankwana sukayi, tana gama wayar ta ganshi Akan ta.

K'are mata Kallo yayi, Yace kinbani Mamaki bazaki Tab'a fahimtar Mahaifin ki ba, Narabaki DA wannam yaron Amma Kink'i fahimtata.

Daka mata tsawa yayi, Yace To kisani nikuma Bazan tab'a Amincewa dashiba bazan had'a zuri'a DA matsiyata ba.

Juyawa yayi yai tafiyar sa.

Binsa tayi DA Kallo, yaje dai_dai Bakin k'ofa Kenam tace Baba kana son farincikin 'Yar ka Kuwait?, dakatawa yayi yai shiru Ta ce Baba kabarta Da auri Wanda take so, Amma duk Hukuncin daka yanke shikenam.

Tsayawa, yayi yace To ina so ki manta da wannam yaron, shiru tayi ta ce shikenam Baba, fashewa tayi DA matsanan cin kula!.

Ya koma d'aki yai zamanshi, washe Gari DA sassafe Yafito sukayi ban kwana, Yajuya zai tafi yace ina Yar gatan baba nekam?.

Juyowa yayi yanazuwa dai_dai Dak'inta yace Yar ghata bude k'ofa tayi tana Sosa Kai, murmushi taga yayi Abunda ya daure mata kai kenam, Yace Zan koma wajen aiki.

kalloshi tayi tace Allah ya tsare hanya ya kuma baka nasara adawo lafiya Baba.

ya juya zai tafi yace Nagode 'Yar auta akwai wata magana dazamuyi Dani dake Da mahaifiyar ki.

Daga nam Yayi murmushi ta k'arbi jakar hanun sa Ta rakashe har gidin mota sukayi bankwana ya Kama hanyar sa tazuwa cikin garin Yola wajen da ya ke aiki.

Ya fara tafiya amota kenam, ya kirowa number zainaba yace da ita ta turo masa number saurayin ta, Haka akayi ta k'ira kabiru tasanar DA shi sannam ta tura mishi number.

Yana sauk'a wajen Aiki number kabiru ya Fara k'ira, tana shiga ya ce........

To masu sauraro shin yaya kuke ganin k'iran da mahaifin zainaba yayiwa k'abiru, zai sauk'a daga kan ak'idar shi ta tsanan talakane kukoma zai bazai sauk'aba?.

♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥
*ZAINABA Y'AR GATA*
♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

*(RICH AND POOR..)*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

BY

*KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*

*31=35*

kalloshi tayi tace Allah ya tsare hanya ya kuma baka nasara adawo lafiya Baba.

ya juya zai tafi yace Nagode 'Yar auta akwai wata magana dazamuyi Dani dake Da mahaifiyar ki.

Daga nam Yayi murmushi ta k'arbi jakar hanun sa Ta rakashe har gidin mota sukayi bankwana ya Kama hanyar sa tazuwa cikin garin Yola wajen da ya ke aiki.

Ya fara tafiya amota kenam, ya kirowa number zainaba yace da ita ta turo masa number saurayin ta, Haka akayi ta k'ira kabiru tasanar DA shi sannam ta tura mishi number.

Yana sauk'a wajen Aiki number kabiru ya Fara k'ira, tana shiga bayan sun gaisa Yace Inason Magana Da Kai Kazo Kasamini Da yamma Ya kwatan tamishi Ofishin sa, Yamma nayi Yaci Ado Ya fesa turare Yayi bankwana da mahaifiyar sa, Da mahaifiyar Yasmin, Ya sako k'afa kenam Zai Fito ji yayi an sha gaban sa daga kansa yayi Yana kallon yasmin yai murmushi ya ce lafiya kam ko?.

Girgiza kai tayi Tace Naga ka fesa wankane kodai kayi wata ne kam?, Ba musani ba murmushi yayi Yace A'a Ai haryanzu zainaba ita kadai ce Acikin zuciyata, Ta ke Yaga ta yi shiru Ta had'e fuska Abun ya cimata rai sosai saita tina da alk'awarin da tayi Ta ke ta yi murmushi ta danne Abun Azuciyar ta Ta ce Gaskiya Ni zan rakaka Idan Har Babu damuwa shiru yayi Ya ce A'a Bazaki Ba Dayaga kamar ranta ya baci yace To naji Zamu tafi Ta re Amma da sharadl' Zaki jirani A mota Ta ce A na yadda Jiranta Yayi Ta shiga ta shafe Mintoci Talatin Da wani Abu Tana fitowa Tindaga Nesa Yaga Ta k'ara kayu sosai tsayawa yayi yana kallon ta.

Ya Fara sak'e-sak'e cikin zuciyar sa ya ce dama haka Ta keda kyau dagan gan Ta ke kin daukan gaye sosai, Tana isowa kusa dashi Tace Yaya kabiru duba kagani nayi kyau kuwa?.

Kallon ta yayi Yai murmushi yace Gaskiya bakiyi kyau ba, Sai jikinta yayi sanyi suka shiga mota yana tuk'i suna tafiya tana harara shi, Yana kallon ta ta gefen Ido yana murmushi Ta ciza baki Ta ce Wallahi Karka kuskura ka min magana Munyi baran baran nagama daukar wankana ka kushe Dan ka tsaneni Shikenam, Ba komai Ai Nima zan rama zan kuma baka mamaki Sai Kaima kaji Abunda naji Yayi shiru bai ce mata komai ba, Chan Ta kai mishi duka Ya tintsire da dariya Ya ce Kiyi hak'uri Tsokanar ki nake.

Kinsan wani Abu kuwa?.

Kallonshi tayi ta murgud'aba ki ta ce, A'a yace Gaskiya ba k'aramin kyau kikayi ba Ni bantaba zata k'anwar tawa haka ta ke da kyau sosai ba, Gaskiya wannam gayen nima kaina saida naji ya burgenj.

Kallon shi, Tayi Tace Ai kuwa Ahakama bawai na tsaya na yi da kayu ba ne, Saurayina shi yadace nayiwa gayen da ban taba wa kowaba kokuma mijina, kallon ta yayi yace nikuma fa?, hararar shi tayi tace kaje chan zainaba tamaka wayasanima ko bata iya gayeba Ko k'azama ce, dariya yayi yace A naji kuma sai me.

Dariya tayi Tace A'a ni karka huce a kaina banina hanaka ita ba Yau de gashi kace mahaifinta ne ya ke k'iran ka da kansa Yace A shine suna cikin Tafiya kenam Sunzo wucewa ta wajen wani shatale-tale Kawai yasmin, Ta ce Yaya kabiru Dan allah gawani Mai Sayar da (MAGARYA), dan allah kasaya mini neman waje yayi ya fa ka Ya ciro 200 naira d'ari biyu ya mik'amata yace Je ki siyo nima zan sha, Kallon sa tayi Ta ce kasan dai titin nam akwai cin koson Muta ne da Ababen Hawa dan allah karkace Na rainaka Gaskiya nikam saidai Na hak'ura ina tsoron titin nam, Jan motar Yayi zai tafi ta ce yanzu yaya kabiru tafiya zakayi ya ce kwarai ma kuwa Tayi shiru Tace To Jirani Zan je na siyo kuma dukda kudin kane Iya wanda zai ishe ni zan sayo.

Bud's k'ofa tayi ta kai kusan minti biyu sannam ta samu ta tsallaka ta riski mai sayar da magaryar tana zuwa tayi Sallamah ya masa tace Baba Abani Magarya na naira Hamsin Dauko leda yayi ya auna mata da gwan-gwami ya mik'a mata ta k'arbi 'yan chanjin ta.
Chapter 10 · 0% Book details