← Book details Yaya Mata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 12

Sashe 12

Yaya Mata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sun dade suna hira sannan surayya tace ke husna yau ina hajiyarki take ne naji shuru gidan ,,,husna tace ay hajiya ta karye har sau biyu,surayya tace amma baki da kirki shine baki gayamin ba maza muje in dubata,,,da sallama suka shiga dakin hajiy daker suka samu gurin zama ,kacaca dakin ,ga wani wari dayake tashi ,rahama ko tayi ficewarta,kasancewar surayya nus ta duba kafar hajiya ,tace ay wannan kafa bata gyeruba ,nan fa tafara fada ,haba husna kina gidan nan da ya,yanki ace hajiya tazama haka ,maza leema dauramin ruwan zafi ,kafin kace an gyre hajiya da dakinta sbd tsbar datti kasan katifarta harda tsusa ,hajiya sai godiya take tana hawaye,

Surraya takira umar tace lalle gobe Monday akai hajiya asivity kashi dan kafarta ta lalace ,,,kafin surayya tabar gidan saida tayiwa husna nasiha sosai akan kula da hajiya ko ita baza tayiba tasa su leema su dunga gyrata kullum ay ko a lahira wani yana cin albarkacin wani,,,,

Washegari zaakai hajiya asivity ,akayiwa lami mgna tace suje zatazo matar ishak kam ko bude kofa takiyi ,,,hawaye umar yafara zubarwa shidai yana jin kunyar husna bazai iya sata doleba ,haka ya kuma dakin hajiya ,abin farin ciki husna yagani da leema da melat sun gyera hajiya ,husna tace ya mu futune yace eh muje ,aransa kuma yace Allah yasakawa surayya da alheri har inda take,

A asitvty ma albarkaci melat akaci dan tana practical agurin ,da sauri aka duba hajiya ina likita yayi ta fada yace lalle ne sai an yanke kafar dan ta baci sosaiiii

Takuce dai uwar farhana ,love u fans😘
*BRILLIANT WRITTES ASSO*

👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀

*YA,YA, MATA*

Abin Alfahari ne

👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀👱🏻‍♀

*BY UMMU FARHANA*

*ALHAMDULILAHI INA MAI GODIYA GA ALLAH DA YABANI IKON GAMA WANNAN LITTAFIN NAWA ,INA MAI RUKUN MAKARANTA ABINDA NA FADA MAI AMFANI SUYI AMFANI DASHI ,WANDA BASHIDA SHI SU WATSAR DASHI,ALLAH KAYAFEMIN KURAKURAINA*

*DEDICATED TO MY FANS LOVE U ALL*❤❤❤❤

Page 24

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Zaro ido tayi ,tace defuty gomv ,yace yes ina fatan an karbeni ,tace kana ganin ba matsalah ,yace babu ,to Allah ya tabbatar mana da alheri ,wani tsalle yayi yana tank u jameelah ,murmushi melat tayi ,taji dadin yadda ya kirata yafi kuwa iya kiran sunanta,

Anfito da hajiya Inda akayi nasarar aiki kafa da gyero sai dai da tafi daya tsayi,kifin tafara tafiya a keke ake fita da ita, umar ya kuma nijeria ,melat ce ke kula da ita ,anan Ali yake lalacewa guri taya melat kula da hajiya ,,,

Hajiya kullum sai tayi nadama marar amfani ta kuma yadda cewa ,YA,YA, MATA,abin alfarine ,gashin nan azahiri tagani uwa mace sai ya,ya, mata ,yanxo har kunyar husna takeji ,tana fatan ta yafe mata,

A gidah

Bayan tafiyar hajiya da Mubarak da affan sai sahal adakin hajiya suke kwana ,kuma na hajiya sun bata ,abin da zai kawu kudi kuwa duk sun siyar ,dawowan umar ne yaga barnar da sukayi hadasu yayi yana musu fada ,duk wata barna sahal ne ja gaba ,yace to Allah ya shirya ,yama rasa mai zai ce ,yacewa lami amma kuna nan a gida nan yaran nan sukayi kacaca da dakin hajiya ,tace ay sahal ne me barna su da girman su ,,,

Haka tun da umar yadawo kullum sai an kawu kara sahal ,haka zaiyi ta bada hakuri,

Husna ce taci kwalliyarta da riga da siket umar ya shigo yace maman yammata irin wannan kwaalliya haka ,rugumarsa tayi tace nayi missing din mijina ,fah ,yace kinyi kyeu husna ,,kinfa kusa zama kaka ,tace mundai kusa zama kakanne ,to ay leema kanwatace kaga ban tsufaba tukun ,yace haka ne amma melat fa ,tace itace yata ta fari ,yace to ay inaga tare zamu auran dasu ,,,azabure tace haba my melat fa 17 take haba ka manta burinmu na suyi karatu mai zurfi ,ita kuma ma bata da saurayi ay,yace tasamu acan Indian kuma naga hankalinsu yazo daya ,munyi mgn dashi dan nan ne amma acan yake aiki ,,,tace amma my tayi kantah ,yace eh mutanen da suke naiman aurent ba kananan mutane bane kuma ma ay bawani kan kanta da tayi aganina ,,tace dan waye keson melat din ,yace dan dupoty govm ne ,zaro ido tayi tace umar kana ganin basu fi karfin ya,ya,n muba ,janyota yayi ya kai mata kiss ta ku ina yace ni a matse nake kar ki cikani da zance ,

.
Sosai jikin hajiya yayi sauki ,har an basu sallama ,inda Ali yacewa umar ya zauna shi zai kawusu ,haka kuwa akayi saida suka biya saudiyya sukayi ummar ,sannan suka wuce ,tayi ta kuka a gaban Kaaba tana rokon yafiya a gurin ,Allah ,sun iso najira inda Ali yakawusu har gidah sannan ya wuce ,,,

Kakaf yan cikin gidan sun hallara a falon hajiya ,an gaggaisa an mata ya jiki ,,,husna har ta tashi zata tafi ,hajiya tace ,husnah kistaya ,husna tadawo ta zauna ,,,

Tace husna dan Allah badan niba na rokeki da Allah kiyafemin ,,abubuwan da namiki sharrin shaidan ne da kuma sun zuciya ,rusa kukatayi ,umar tasowa yayi yazo gaban husna yace maman yanm,matah ,kiyafewa hajiya ,kinji ,hawayene ya zubuwa husna tace na yafemiki hajiya ko da chan ma ban rikeki a zuciyaba,,,godiya hajiya da umar sukeyi ,haka hajiya ta janyo yaran daya bayan daya tana naiman gafarsu ,duk sun yafemata ,

Sannan tace umar nabaka izini ka kuma sabun gidan ka kaji, godiya yayi,,lema ce tace hajiya ina da mgn ,hajiya cikin wasa tace ,ina jin gimbiy halema,dariya sukayi duka , tace haka za abar rayuwar sahal ta lalace ,baya zuwa mkr ba islamiya ba boko yakamata ay wani Abu akai ,,hajiya tace awww ina sahal din yake ,tun zuwana ban sashi idoba, leema tace ay baya yin a gidah fah,umar yace to ya,zaayi dashi leema ,tace inaga akaishi tahafezul Quran na mudo mustafha ,in anci saa qurani ya nitsar dashi ,,,haka aka yarda da shawarar leema ,,,

Yau ne akazo sa ranar leema da melat ,ansa rana wata uku ,gaba dayansu ,gidan sarauta sun bata sadaki ,dubu dari biyar ,da kujerar makka goma da mukullin mota daya ,na lema kenan,melat kuwa milliyun dayane da mota ,da kayan sa rana cikin babbar mutah,haka akayi aka waste ana girmama juna ,

Inda gabadaya anguwa da dauka umar ya siyar da yayanshi ,lami ce kam gabar yadawa, amma da aka raba kujerar makka surayya tace abata itama taci Albarkacin YA,YA, MATA,nan fa baki ya rufu,

Umar da husna sun kuma Sabun gidansu inda leema ta dauki sahal ta kaishi mkrt ,kuma ta janyushi jikinta ,ba laifi ya rage rashin ji sosai mussamman yawo yanzu bayayi sosai

Shirye 2 biki ake babu kama hannu yaro inda surayyah kullum tana hanyar Maiduguri daga yobe,amare ma baa barsu abaya ba mussaman melat tafi leema rawar kai ,, kannen amarema ,suna nasu, harny da surayya karama da meemah ,anata tsare 2 ,hajiyama anata dingisa kafa ,ba a barta abayaba ,,,

Ali da melat sunshirya fati kala2 ,inda leema da yarima walimace kaya tacciya aka shirya,,,
Me gyeran jiki tazo ta fara yuwa amare ,,

Rana bata karya

Yaune duban mutane suka shaida daurin auren

Halema and yarima

Jameela and Ali

Nan aka zarce da biki babu kama hannun yaro gida yacika tab sai ga hajar nan,Ashe tayi wani aure,,,,

Yau surayya ta shirya mother's night,a barweee ,nan na hango su Zara,u dasu jannat ,maman mufi ,da ummu safwan ,sai borosh ake da kaji🤪

Haka a gurin walima da fati na hango duk yan brilliant sun hallara ,inda hango melat musa anata kora kunun aya, my jikas anata cin kaji,,

Angama biki lfy ankai am are gidajensu ,leema ankaita shehuri gidan sarki ,melat kuma g,r ,a ,aka kaita ,inda sati na zagayowa ,melat sukayi Indian acan zata karasa karatu,leema kuma honey Mon suka tafi,,,

Bayan kuwa ya watse daga surayya da husna,tace Anty Ashe haka haihuwa take da dadi ,surayya tace in Allah yabaki mai albarka sai ka godemasa, tace hakane Anty ,,

Husna da umar ne zaune suna hira ,,,yace ikon Allah ,ayanzu kumai ya wuce mana sai dai mu godewa Allah , A tare sukace

ALHAMDULILAH, NIMA NACE ALHAMDULILAH

TAMMAT

TAKU UWAR FARHANA😘
Chapter 12 · 0% Book details