← Book details Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 10

Sashe 6

Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malam gaskiya ka kyauta da wa'innan kaji, amma da akuya ka yanka mana kasan dai kaji hudu baza su ishe mu ba."inji Jummai.

"Uhm wallahi a kiyayi fushi na a gidan nan, domin babu wacce tsohon ta ya taba cewa Tanko ga ciyawa ka ba dabbobi."
"Kenan Iyayen mu kake zagi Malam?"
"Oho ban sani ba, nidai a kular min da nama ko kafar kaza bance a ciba idan an gama ni zan raba abuna da kai na."

Hannatu dake zaune ta yi tagumi ta doka tsaki. Jin tsakin ya sa mai unguwa juyowa yana fadin "Yar matsiyata kinyi ma mai alewa."
"Matsiyaci shine wanda bai san ya wadata iyalinsa ba."

Aikuwa mai unguwa ya mike ya nufota, ganin haka Jummai ta shiga tsakani tana aikamai da mugun kallo. Sanin idan ya tanka bazai ji dadi ba yasa ya juya yana fadin" Shegu mayu kawai, kuma ni zan dafa kajina da kaina yau billahillazi." ya karasa bakin murhu ya dau mafici yana fifita wuta.

Babu wacce ta kuma kula shi duk mikewa suka yi suka kama sauran ayyukansu na gida.

Shi kuwa mai unguwa cire malun-malun dinshi ya yi yana fifita wuta. Nama ba ruwa sai kamu yake amma bai masan yana yi ba. Matan najin yanda naman ke konewa sukai banza dashi.

Maman Dare ta shigo da gudu wanda hakan y tsorata mai unguwa ya mike zai gudu, ta dakatar dashi ta hanyar fad'owa gabanshi tana haki hade da fadin"Sun kashe sun kashe."
"Ke wa suka kashe?" ya daka mata tsawa.

"Don Allah mai unguwa kazo sun kashe kansu a gidan mu."

Jin haka ya fahimci mai take nufi don haka yaja tsaki "Babu inda zani su kara nakasa ni alkur'an."
"Don Allah kazo wallahi sunyi barin nama yara nata diba fa."
Jin ta ambaci nama yasa ya saba babbar riga yace" Muje na gani." suka fice bayan y babbaka m tukunyar naman shi wuta.

*Mezai faru kenan ga mai unguwa ya kuma komawa gidan 'yan haya, bayan yace bazai kara zuwa ba.*

*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

. 👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼

Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

_K'awas Ummu basher nd Anty Maimounath. Ina kuke 'yan'uwa rabin jiki, wannan shafin na kune kyauta domin soyayyar ku daban ce kuna raina kodayaushe. Ina godiya gareku sosai ana tare Allah ya kara basira._

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*45~50*

Matan shi na dak'i suna ji har ya fita, babu wacce ta kalli tukunyar naman.

Lado ya yi sallama hannunshi rike da bakar leda. Suka amsa mishi ya zauna bayan ya gaidasu, ya ajiye ledar yana fadin "Gashi nama ne na siyo muku na cika ciki."

Murna sosai suka yi suna fada mishi 'yanda suka yi da mai unguwa kan nama. Dariya ya yi sosai ya mike" Na wuce ba nasan yazo ta sameni gidan nan." Nan ya tafi abun shi.

"Maman Sani mu dafa mu boye kafin ya dawo." cewar Hannnatu.
"Basai kin fadi ba yanzu zamu dora mu raba, idan ya dawo ya dau nashi naman."

Suna hira suna aiki ko kallon naman mai unguwa basu yi ba.

*CIKIN GIDAN 'YAN HAYA*

Dambe ake na kin karewa, gashi duk sun tattake naman da tumatirin da suka zubar.

Maman Usman na dak'i tana girki, duk abun da suke tana jinsu ta yi banza dasu, domin tasan halinsu.

Inno ce tsaye gefen rijiya tana kwashe sauran naman Maman Ladi da ya zube. Jin saukar duka ta yi bayanta wanda ya haddasa zubewar naman hannunta.

Maman Ladi ce ta kai mata wannan duka bayan ta baro matar Malam cikin kicin ko motsi ta kasa yi. Cikin bala'i Inno tace "Maman Ladi ashe ke matsiyaciya ce ban sani ba, taya ina kwashe miki zakiyi min wannan duka?"
"Na zata ai cikin namanki zaki zuba yi hakuri."maman Ladi ta fadi tana haki.

Watsar da naman Inno ta yi tace "To don kaza-kazan mata na fasa kwashe wa."
Kau! Maman Ladi ta kwashe ta da mari, cikin huci take fadin" Ba a haifi matar da zata zageni ba wallahi don ubanta, nice nan Maman Ladi murucin kan dutse an buga an barni."

Nan sabon dambe ya kaure dai-dai shigowar mai unguwa. Aikuwa yana zuwa ya hau rabo yana rokon don Allah su bari, amma ina kamar basu ganshi ba. Gashi sai take nama suke yi, can ya leko kai cikin kicin da niyar ganin mai na ciki keyi. Saukar ruwa yaji a fuskar shi wanda ya haddasa daukewar ganinsa na wani lokaci.

Jin ba ruwan zafi bane ya sanya mai unguwa bude ido tare da goge ruwan fuskar shi da rigarsa. Inna Talatu ce ta watso ruwan da nufin ya sauka kan Ladidi, ganin bai zuba inda ta watsa ba yasa ta kuma daukar tukunyar ta nufi Ladidi ta k'wada mata. Mai unguwa na tsaye yana kallon wannan rikice ya rasa yanda zai yi ganin da gaske fad'a suke ba kakkautawa.

Matsawa ya yi kusa da dak'in Maman Usman yana sallama. Tana ji ta yi shiru domin ta gaji da rabon fad'a. Jin mai unguwa nata doka sallama yasa ta leko tace "Kayi hakuri mai unguwa, bansan ya zanyi su daina ba ni kaina takaicin fad'an nake wallahi."
"A'a Maman Usmanu baza mu barsu su kashe kansu ba, ki taimaka ki fito don Allah."

Jin magiyar mai unguwa yasa ta amince ta fito. Matar Malam na kwance ta kasa motsi sai taka ta suke yi. Maman Usman ta shigo ta daga ta da taimakon Abule suka fitar da ita suka aje ta kan dandamalin kofarta.

Maman Usman ta shiga tsakanin Ladidi da Inna Talatu ta rabasu suka fito waje, ta kalli yanda kicin din ya yi kaca-kaca da nama da kuma tumatiri. Girgiza kai ta yi tana takaicin halayyar matan gidan.

Duk suna tsaye ga mai unguwa dake yi musu fad'a da sunan nasiha. Maman Ladi ta kalle shi cike da takaicin fad'an da yake musu tace "Dalla malam rufe mana baki."
"Walle wanga mai unguwa gulma ta dashi, sai kace shi na da wanga gida." cewar Abule tana aikamai da harara.

"Billahillazi zanyi karar duk shegiyar data kuma zagina, kaji mahaukata ana yi..."
"Kaine mahaukaci wallahi ba dai mu ba, banza mai bakar fuska." Ladidi ta katse shi.
"Uban ki ne banza ba Tanko ba matsiyaciya mai zubin munafukai."
"Kai kuma mai zubin 'yan wuta ba." cewar Inna Talatu.

Takaici ya cika Maman Usman dake tsaye tana kallon duk abun da suke yi. Ganin abun nasu zai yi kamari ga mai unguwa kamar zai yi duka yasa ta daka musu tsawa. Duk sukai shiru suna kallon ta.
"Sai yaushe za kuyi hankali, ku gane abun da kuke bai dace da ku ba?, yara gare ku fa kuma tarbiyyar ku shi zasu dauka na roke ku don Allah ku yi ma kanku karatun ta natsu, ku gane zaman lafiya yafi komai dadi."
"Kiyi hakuri Maman Usman zamu gyara." cewar Mairon Ado dake tsaye jikin kofarta.

Sauran shiru suka yi suna hararar mai unguwa jin yana fadin " hankali ne bai ishesu ba shiyasa suke wannan haukan."
"A'a mai unguwa kai babba ne bai kamata kana fadin haka ba"
"To Maman Usmanu ayi hakuri, amma dubi yanda suka wulakanta nama kamar ba kudi aka sanya aka siya ba, dubi kiga matar Malam zube ko motsi ta kasa."
"Dadin abun mazajen mune suka siya mana, ita kuma matar Malam gulma ya kawo ta." Maman Ladi ta fadi tana jefa mai mugun kallo.

"To nidai na fada muku kuyi hankali domin watarana duk bama nan." cewar Maman Usman ta shige dak'i.

Ganin Maman Usman ta wuce yasa mai unguwa shima ficewa yana sababin anci mutuncin nama.

Sanin cewa sunyi ma juna ta'asa ya sanya babu wacce ta nemi a biyata namanta ku tumatir. Mai saura ta deba ta cigaba da girka wa.

*GIDAN MAI UNGUWA*

Matanshi sun gama nasu girkin tsaf sun raba, inda suka bar mishi nashi bisa wuta ko dubawa basu yi ba. Suna zaune suna hira ya shigo da sallama.

"Barka da dawowa Malam." cewar Hannatu tana dariya kasa-kasa ganin jikin shi duk ruwa.

Banza ya mata ya wuce tukunyar naman yana duba wa.
"Jakar uban nan, yanzu dama duk bakin ciki kuke dani ko, arzikin da tsohon ku bai dashi kuke wulakanta wa ko?, kaji tun dazu dana fita babu shegiyar data duba min."

"Haba Malam! Haba Malam! kai fa kace kar mu taba amma yanzu ka zo kana zagin iyayen mu?"
"Na zaga Jummala, nace na zaga akwai 'yar kwal uban da zata rama ne?, shegu masu zubin ifiritai."

Sanin idan suka biye shi makota na iya ji, yasa Jummai ta yi ma Hannatu alamun ta yi shiru.

"Kuma wallahi Allah ya isa tsinannu kawai, zanga uban da zai baku abinci yau a gidan nan. Kuma wallahi sai na kai karar ku gun ubannin ku, ko wacce sai ubanta ya biyani kazata data kone." ya fadi yana facali da tukunyar ya yi waje.

*GIDAN 'YAN HAYA RANAR LARABA*

*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: ⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜
*'YAN GIDAN HAYA*
🔱🔱⚜⚜🔱🔱⚜⚜🔱🔱

. 👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

©
*Badeeyerh Beauty Queen*✍🏼

Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
[email protected]

*'Yan uwana abokan aiki wannan shafin ya zamu naku kyauta wato Zamanawa masu karamci, mutane masu halin dattako, ina gaisuwa the musamman gareku. Allah ya daukaka Zamani ya kara hade kanmu.Ina son ku sosai domin kodayaushe Kuna fadakar da al'umma da dunbin basirar ku, Allah ya kara basira ya kare mu daga sharrin mahassada ameen. One Love ZAMANI WRITERS*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*50~55*

*GIDAN 'YAN HAYA RANAR LABARA*

Suna ta aikin su, duk sun shirya da juna a nata raha ana dariya. Inno ta fito zata je unguwa tace "Mutan gida da alheri zan tafi sai na dawo."
"Adawo lafiya dillaliya."duk suka fadi.
Chapter 6 · 0% Book details