Sashe 7
Yakanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Sulaiman ya fahimci damuwar Hadiza ta ragu da 80%, sai ya samu kwarin gwiwa da jarumtakar fuskantar aikin sa. Ya koma aiki ranar monday cike da tausayin Hadiza, yana mai tuno lokutan zirga-zirgar su cikin asibitin don ceton al’umma, da matsalar ta mai magantuwa ce ba ya tsammanin in zai rasa duk abin da ya mallaka zai gaza wajen nema mata magani.
A wani bangaren kuma yana tunanin shawarar su Dr. Ruth ne da suka ce
Hadiza za ta iya komawa aikin ta a haka. Da ya tuntube ta, ta nuna ba ta yi naam da shawarar ba, don ba ta yanke kauna da rahmar Ubangiji ba, za ta zauna a gida ta yi zaman aure, wanda a da ba ta yi ba. Ta ga shi kuma wace irin riba ce a cikin sa, tunda ta yi aikin, ta ga ribarsa da rashin ribar sa? A wautar Hadiza, tunda wannan lalura ta same ta shikenan Sulaiman ya daina sha’awar ta, wato ya daina mu’amalar aure da ita, tunda ta nakasa ba ta da abin da za ta ja hankalin sa. Ba ta yi la’akari da cewa soyayyar ta a cikin jinin Sulaiman take ba, ba’a abun jan hankali ba.
Kwata-kwata sati biyu cur da fitowar ta daga asibiti, sai labari ya sauya, Sulaiman soyayya har ta fi ta baya, kamar wanda ya je ya kara yin course a kan (lobe-making). Watakila da da hali da ya tsaga kirjinsa ya sanya ta a ciki, mai yiwuwa sannan ne zai zamo (contented).
Sai da komai ya lafa ya fahimci
Hadiza kuka take, ba kuma kukan komi take ba, ….kukan rashin yarda da kai ne.
Amma shi duk sai ya rikice, kukanta da hawayen ta ba karamin daga mai hankali ya yi ba.
Ya tarairayo ta ya dora a kan kirjin shi, cikin sassanyar murya yake tambaya, “Did I hurt you Hadizahh?’ Ta girgiza kai, cikin shesshekar kuka ta ce,
“Sulaiman kai ne?”
“In bani bane wane ne?”
Sai ta yarfar da hawaye da hannun
daman ta, ta ce, “Ni dai ka kara AURE!”
Sai ya janye jiki daga jikinta cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwa, “Kafin in baki amsa Hadiza, ko in bi umarnin ki, ina so in san mene ne dalilin ki na cewa hakan?”
“Saboda Hadizar da, ba ita ce yanzu ba, wannan nakasasshiya ce, ba ta cancanci wannan dimbin soyayyar
ba”.
Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken asubahi da ya soma keto shara-sharan farin labulen dakin, kamin ya yi murmushin takaici ya zauna sosai ya ba ta baya.
“Hadiza tafiyar ki ce ta sa na aure ki? Ko ko yanga da kwarkwasa kika yi min na ji ina son ki?”
Ta girgiza kai, “babu ko daya. Amma son da nake maka Sulaiman, ba zai barni in kware ka ba, idan ka ci gaba da zama dani ni kadai, na kware ka, a matsayin ka na _ lafiyayye kuma cikakken namiji. Idan ka kara aure zan ji dadi, zuciyata za ta sake. A kalla ina da tabbacin baka cikin kwaruwa, amma yanzu sai nake ganin, na kware ka…….. ”
Ya daga mata hannu ya ce, “Ya isa, ya isa Hadiza….” Ya ma rasa me zai ce don takaici, sai ya karkada kai ya fita ya bar mata dakin.
Kwanaki uku suna kan wannan takaddamar. Hadiza ta dage ta ja tunga a
kan bakanta, in ya yi fushi sai kuma ya sauko ya yi dariya don mamaki. Ba ya son duk wani abu da zai bata ranta a dai wannan lokacin da_yake angwancewa da kuma yin la’akari da halin da take ciki.
Don haka a rana ta biyar da ya ga ba zai iya jure wannan horon da ta tsiri yi mishi ba, don ba shi da juriyar a wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan. Sai ya cafki hannayen ta ya langabar da kai kamar karamin yaro, idanuwan nan sun juye sun rikide zuwa……..
Ya ce, “Hadiza na baki wuka da nama, ke ce mijin ke ce matar, ki zabo min duk yarinyar da kika ga ta dace dani, don bani da idon kallon wata diya mace, tun daga lokacin da Allah ya mallaka min ke……”
Ta cira kai a hankali ta dube shi, sai ya ba ta tausayi, don numfashi kanshi a wahale yake furzar da shi da sauri da sauri. Ganin yadda jidalin ta ya ramar da shi kwanaki biyar kacal, sai ta kara
jin tausayin sa.
Amma jan ajin mu na mata, sai ta balla masa harara wadda in ka lura ba komi ne cikin ta ba face tsananin son mijinta da matsanancin KISHI, ganin daga karshe ya sauko ya bi ra’ayinta kamar yadda take so.
Kamar ta yi kuka ta ce, “Nice ma zan nemo maka matar? Ashe you are not serious…!” Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr! Sun zubo a kan kundukukin ta.
Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi. A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, “Wai ko a cikin student din ward din ku, irin ‘yan yara-yaran ‘yammatan nan? Ko rikakkun ‘yammatan likitoci irin su Dr. Surayyah”.
Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya. Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba.
Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. A sanyaye ya ce,
“Ko kin daina sona ne Hadizahh? Kike neman kai dani? A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure. Which mean……. na gundire ki…. kina neman mataimakiya don ki huta…..
Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba? Inda nake aure zam-zam yake. Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi. Kafafu? Ni ba ina da su ba? Kuma ba ina daukar ki dasu ba? To meye damuwar ki?
In gaya miki gaskiya, ba zan iya sharing kaina ba, saboda ina da kyama, ba kowacce mace zan iya hada jiki da ita ba. Babu, ban taba ba, bana fata, kada ki tursasa ni, don ba zan iya ba, ba zan iya adalci ba. An ce kuma in ba za ku iya adalci ba, to ku zauna da daya. Amma in kin gwammace ranar kiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same, sai in auri Surayyah!
Kinga daga nan sai ku kara dankon zumunci…….. Ta ture shi da sauri, duk da jikinta ya yi sanyi da maganganun sa, ta tabbatar iya gaskiyar shi yake fadi, don shi bai fadin abin da ba haka bane a zuciyar shi. Don kaji dadi, ko don ya faranta maka. In haka ne kenan Sulaiman da gaske za ka iya auren Dr. Surayyah?” Sai hawaye suka zubo.
Magana take a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ba. Ya sauka daga gadon ya zauna dabas a kan kafet, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, “Ni SuJaiman na shige su, duk yadda na yi, ban iya ba. To ki fadi yadda kike so, ni kuma mijin ta ce ne!”
Idon ta fal hawaye ta dube shi cikin ido, abin da bata yi sai rana ta kure, “Ka gaya min gaskiya Sulaiman, Surayyah kake so?”
Ya yi murmushi ya shafi siraran lebbansa, “Ya ya ba zan so ta ba tunda tana son ki, tana son ‘ya’yana?”
“Ni ba wannan son nake nufi ba……..
Ya mike tsaye ya bata baya zai fice, “Koma wanne kike nufi shi ne, yarinyar nan rikicinki ya ishe ni, son ta nake na soyayya, soyet. Ki yi kulikulin kubura dani, ko ki yi ta kuka, har hawayen ya kare…….. ”
Duk da kuka take ba ta san sanda ta yi dariya ba, ganin kuma ya dawo ya cafko ta yana son a sauya hirar da irin wacce ya fi so ayi, mai ma’ana da tsayawa a zuci, hadi da dimbin lada. Ba ta da zabi (she habe no choice) ban da ta rungumi mijinta, mai son ta, mai kaunar ta. Ta nuna mishi son shi kawai ya sani, bai san nata ba. Duk hasashe take, amma ita ma ta san ba za ta iya raba Sulaiman din ta da kowa ba.
2K OK
D
a wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba.
Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba?
Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi.
Ta ce, “Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da ‘ya’yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?”
Surayyah ta ce, “Ke din ce dai kawai kin yi sa’a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr. Sulaiman ba”.
Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unikue, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi. Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa, “Shege Bunza, ya kasa ni”.