Sashe 13
Yakanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
“Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu””, Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri.
Malam ya ce,
“Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta”.
Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati.
Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce, “Fati kin kwanta ne?” “A‘a, ina harama dai”. “To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke”. Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam. Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban
Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe. Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi. Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano.
Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane.
Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman. Wannan taro na mene ne? Malam Sulaiman baya _shiga kankanuwar magana.
Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce,
“Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu”.
Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa. Ya ci gaba da cewa,
“Muna kara yi muku ta’aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa.
Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin ‘yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da_tarbiyyar ‘ya’yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma ‘yar uwarta ta karbe ta.
Allah ya riga ya hada mu, zuri’a ta hada mu. Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba. Za mu yi alfahari
daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya. Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin ta a rayuwa ya tagayyara shi ba.
Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar ‘yar uwarta ta hanyar aure, muna neman hadin kan ku, za mu samu Fatima da Sulaiman?”
Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta. Tana addu’a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita.
Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba. To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza? Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza? Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure. Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba.
Duk da yadda take hidima da ‘ya’yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a
zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba’in din Hadiza? Sannan da shakikiyar ta? Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba. Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar ‘yar sakandire ta maye gurbin Hadiza? Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza? Ya yada girman sa ya yi mu’amalar aure da ita? Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba.
In don ‘ya’yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba.
Malam Ja’afar ya ce, “Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba. In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa”.
Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce,
“Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba”.
Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa. Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon.
Ta yi dakinta ta dauki ‘yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci.
Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu’o’’l, sa albarka da fatan alheri a gare shi. Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama.
Mu tara a littafi na 2. Kuma na karshe inshallahu. Wanda tare suke da dan uwansa. Maman Safah da Marwah ce, ke yi muku fatan alheri.
c a
_=>
– =
– —=
_=
—=
– >
Advertisements