← Book details Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 104

Sashe 57

Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a katafaren falon gidansu, ta canja tamkar ba Suhailat matar baseer ba, ta kuma cika da girma dan batafi sati uku da dawowa ƙasarba ma, tana Germany karatu, waya take latsawa hankalinta kwance, yayi da su Mom ɗinta ke kallon labarai.
Kamar ance ta ɗago sai ta kalli TV jin Daddynta tana kwarzanta bikin rantsarwar dayake shima yaje saboda mahaifin Meenal abokin sane.
Ƴar zabura tayi tana kuma ware idanunta akan tv n, “Kam bala'i, Baseer!!”.
Atare Mom da Daddyn ta suka kalleta tareda cewa, “Baseer kuma?”.
“Ƙwarai kuwa Daddy, wannan Baseer ne ya gama magana a matsayin surukin gwamna, Daddy yaran Alhaji Ɗalha nawane mata?”.
“Eh to, kamar guda biyu ne, ɗaya ce kuma tai aure shekara kusan biyar data shige, kinsan anyi bikin lokacin bana nan shiyyasa ban jeba sai Salman na wakilta”.
“To aiko lallai Abba shegen nan ne Baseer mijin”.
“Ya zakice haka Suhailat? Tayaya kika san haka?”.
“Mom ko shekara nawa nayi banga Baseer ba na gansa saina ganesa, Daddy kana da
Invitation ɗin bikin?”.
“Za'a iya samu Suhailat, amma fa kinsan kusan shekara biyar kenan, ganesa sai ansha wahala”.
“Daddy bazanji wannan wahalar ba, zanje na duba inda kake tara invitation card ɗinka yanzu nan, dan rayuwar yarinyar tana cikin haɗari, na tabbata itama ba sonta yake ba, kamar yanda yay min zai mata ya gudu”.
“Gaskiyarki kuma Suhailat, kiyi dukkan binciken daya dace, inhar shine kam ya kamata mu fargar dasu”.
“Insha ALLAHU kuwa Daddy na, nagode da goyen bayanka a gareni”.

“Amma Alhaji inaga ya kamata kasan mi Suhailat zata aikata ma yaronnan, kar tunanin ɗaukar fansa ta sakata aikata abinda zamu dawo muna dana sani, kaga dai bikinta kwana kaɗan ya rage, ni dama za'abi ta taune da an barsa kawai duniya ai makaranta ce, zai haɗu da daidai shine a cikinta”.
Murmushi Daddy yayi yana kallonta, “Karki damu a duk motsinta zan saka idanu, amma batun a barsa ma bai tasoba, dan kingansa fa yanzu a matsayin sirikin gwamna, zuwa nan gaba ina kike tunanin zai kutsa? Sannan bamusan su kuma da wace fuska yaje musu ba, irin waɗanan idan ba'a daƙilesu ba, suke zamewa al'umma wata babbar fitina yayinda ALLAH ya basu wata dama ta mulkin ƙasa”.
“Eh to hakane kuma Alhaji, ALLAH dai ya shiga tsakanin nagari da mugu, dankuwa yaron nan ya bar mana tabo mai girma, danma ALLAH ya taƙaita babu rabon ƴaƴa a tsakani”.
“Wlhy kuwa Hajiya”.

Yayinda suketa tattaunawa Suhailat nacan tana bincike, ganin zata wahala kafin ta gani saita ƙyale komai ta fito.
Daddy dake kallonta yace, “Kin gansa?”.
“A'a daddy, wannan zai zama mai wahala, ga shawara mana”.
“Ina saurarenki auta”.
“Daddy muje musu gaisuwar taya murna ta musamman dukkan iyalanka, ta wannan hanyarne kawai zan samu haɗa ƙawance da ita”.
“Eh to kinzo da shawara, ki bari komai ya lafa zanyi tunani”.
“Yauwa my sweet Daddy na, ALLAH ya ƙara yawancin kwana”.
Dariya sukayi shida Mom.
Itako ta fice zuciyarta fes, lallai Baseer yanzu ne za'ai karon, munafiki kenan mai fuskar zalunci, mai ƙyan ɗan maciji. dolene ta nemo abokansa su Najeeb, ta hanyarsu tasan zata samu bayanai na musamman insha ALLAH.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Wannan karon kam baba har gidan Alhaji Abubakar yazo shida inna harira, daga can suka ɗunguma zuwa gidan hajiya yaya, inda akaita haba-haba dashi, domin kuwa surukine.
Ya girgiza shima dajin labarin nan, duk da dai yaɗanji wani abun tun da ƙuruciya gameda hajiya yaya, amma kasan tuwar bata garin sai yazam komai an manta dashi, har ƙwalla yay daya tuna da matarsa abar alfaharinsa Ɗahara, wadda ashe sunanta na asali Hassana.
Kwana biyu da zuwan baba suka ɗunguma zuwa ɗilau su duka gidan, har hajiya yaya.
Kuka dai ta shashi, ƙalilanne waɗanda ta sani suka rage a raye, sai waɗanda tabari suna ƙanana, suma yanzu duk sun tsufa da yawansu, dan danan ƙauyen ɗilau ya ɗauki sabon salon labari, su Ummukulsoom kam ansha yawo, dama tana kewar garin sosai, ta daɗe batayi kwanakin nanba.

Komai na tafiyar Ummukulsoom ya gama kammala, dan haka suka baro ɗilau aka bar hajiya yaya acan akan itafa saita more zata dawo. sosai take ɗoki akan ganinta garin haihuwarta, wanda ada aka haramta mata shigarsa a shekarun baya.
Su dai su Ummukulsoom kd suka dawo sukai shirin tafiya legas.

*_Ummukulsoom a birnin ikko karo na biyu_*

A wannan karonma isowar ,dare sukayi, babu abinda ke fita a fuskar Ummukulsoom sai murmushin takaici, da tuna shekara biyar da wasu watanni da suka shuɗe, ta shigo garin a matsayin matar cushe a wancan karon, ta barsa a matsayin bazawara, yanzu kuma ta dawo cikinsa matsayin mai neman ilimi, fatanta ta fita a matsayin mai tarin nasarar cikar burinta.
Maman Ahmad dake kallonta itama tai murmushi tana nuna ma Attahir ita.
Murmushi shima yayi kawai, ya tabbata tana tuno waɗancan shekarun ne da suka shuɗe.
Ɗaukarsu akazo yi, Attahir da maman Ahmad suka shiga mota ɗaya, Ummukulsoom da Bily ma suka shiga ɗayar.
Tunda suka shigo Barrack ɗin Ummukulsoom ta fahimci wasu canje-canje da aka samu masu yawan gaske, su Attahir dai suna nan gidansu data sani, sai dai kayan ciki da aka canja.
Sam hana dukkan tunani mai alaƙa da tuna baya tai yay tasiri a kanta, ana basu masaukinsu ma itace ta fara shirin barci ta kwanta ba tareda ta nema abinci ba, dan sam batajin wata yunwa.
Bily ma dai shirin barci tai tazo gefenta ta kwanta suka lula duniyar barci hankalinsu kwance.

Washe gari da safe da taimakonsu maman Ahmad ta gyara gidanta tsaf ya dawo nomal kamar yanda take buƙata, bayan sun kammala breakfast Attahir ya fita ya barsu suna hirarsu.

★★★★★★

Kansa tsaye gidan Amaan ya nufa da ƙafa, yay sallama a falon da yake tsit babu motsin kowa, ko kaɗan bai kula da Amaan dake zaune a dining yana karyawa ba, shiko tun shigowarsa ya gansa, amma yaki magana, saima ɗauke kansa da yay ya cigaba da cin abincinsa.
Sai da yaga Attahir zai nufi bedroom ɗinsa sannan yace, “Kai kuma fa?”.
Juyowa Attahir yay ya kalli dani ɗin, “Oh ashe ga gwairon nan zaune yanacin girkin ƙato”. ‘Attahir ya faɗa cikin jan magana’.
Sai a kai sa'a Amaan ɗin bai tanka ba. Kujera Attahir yaja ya zauna shima, “Su Ajiwa masu guduwa, to laifin da kaine yasaka tserowa kana tsoron na maka hukunci ko?”.
Shi kansa baisan murmushi ya suɓuce masaba, duk yanda yaso ɗaukar zafi da Attahir baya iyawa, ya ɗago manyan idanunsa akan Attahir, “Wai kai bazaka canja bane ba?”.
Dariya Attahir yayi shima yana kallonsa, “Ajiwa inhar baka canjaba ya za ai nima na canja, shikenan saika gudo ka barmu bayan kuma tare mukaje”.
“Share kawai Attahir, ya ka baro mutanen kd n?”.
“Kowa lafiya yake”.
“To Alhmdllh, ga abinci”.
“Wa? Kaima kasan wannan ganganne Ajiwa, inada matata na zauna cin girkin ƙato, wannan sai ku gwauraye”.
“Kai dai ka sani mara mutunci kawai”.
Dariya Attahir yayi, yasan dai ƙarshen zancen kenan, babu wanda ya sake magana a cikinsu har Amaan ya kammala cin abinci suka dawo falo, abinda ya shafi aikinsu suka cigaba da tattaunawa, tareda shirye-shiryen ƙarin girman da ake shirin ƙara musu. Koda wasa Attahir bai sanar masa da zuwan su Bily ba.

★★★

Tsawon satin su Ummukulsoom uku a cikin Barrack ɗin ALLAH bai taɓa haɗata da Amaan ba, harma ta fara zuwa makaranta.

Yau ta kasance Alhamis, da wuri Ummukulsoom ta dawo gida saboda lecture ɗin safe tayi, akwai abokin su Attahir Bello matarsa ta haihu, gidansu kuma yana maƙwaf taka da gidan Amaan ne, lokacin da Ummukulsoom ta dawo daga school ta iske Maman Ahmad da Bily sun gama shirin tafiya gidan sunan, ita kaɗai suke jira, ganin zata ɓata musu lokaci sai Ummu tace suyi gaba, ita zata taho tare da Ahmad idan an ɗakkosa daga makaranta.
Tafiya sukai kuwa suka barta a gidan ita kaɗai, wanka tai ta zauna taɗanci abinci, tana zaune a falo saiga Ahmad ya dawo.
Oyoyo tai masa ya faɗa jikinta yana mai jin daɗin ganinta, yaron akwai wayo sosai.
“Aunty ina su Mama?”.
“Sun tafi gidan suna Amadina, muma yanzu idan kaci abinci zamuje mu samesu”.
Tsallen murna ya farayi jin za'aje yawo, itakuma tana masa dariya.
Wanka tai masa ta shirya sa tsaf yay ƙyau, sannan ta nufi ɗakinsu itama ta shirya baƙar jallabiya da akai mata ado da farin zare dayaji stons, ɗan ƙwalin kawai ta naɗa ta riƙe waya da handky a hannu, sai takalmin ƙafarta fari flat, tayi ƙyau masha ALLAH.
Kulle gidan tayi ta kama hannun Ahmad suka tafi cikin nutsuwa, tunda ta fito daga gida gungun matasan sojojin suka zuba mata idanu, kowa na yaba halittar ubangiji a ransa, itako ko sashen da suke bata kallaba, tafiyarta take kanta tsaye Ahmad na mata surutu tana murmushi. Ba taɓa zuwa gidan tayiba, amma maman Ahmad tace tai mata kwatance, tareda cewa ko Ahmad tacewa suje gidansu abokinsa Sulaiman zai kaita, kuma ma ai tunda taron suna ake zata gane.
Tsayawa tai daga tafiyar da takeyi ta kalli Ahmad, “My Amadi wai kasan ina kuwa zamuje?”.
“Eh Aunty, ba kince gidan su Sulaiman abokina ba”.
“Yauwa yaron kirki ashe baka mantaba kuwa, muje to”.
Ci gaba sukai da tafiya, kasan cewar Ummukulsoom taga da ɗan mutane a wajen ɗai-ɗai kuma ga fararen kujeru da aketa shiryawa sai tabi Ahmad kai tsaye inda yake jan hannunta. Dukda ta zauna a Barrack ɗin bazata ƙarar da komaiba tunda a wancan lokacin bawani yawo takeba sosai, sai gidan maman Ahmad, shima zata iya irga zuwanta gidan kuma.

★★★★
Chapter 57 · 0% Book details