← Book details Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 104

Sashe 45

Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel · about 7 min read

............Rayuwa ta cigaba da shuɗawa, yau da gobe kayan ALLAH, tun ana ƙirgen kwanaki har aka koma sati, aka koma wattanin da suka ƙulla shekara, kafin wani dogon zango saigasu Ummukulsoom da shekaru huɗu a makaranta, karatu yayi nisa sosai, yayinda nasarori da ƙalubale ke ƙaruwa, to dama rayuwa ta gaji haka, dolene wataran ayi kuka wataran takaici wataran al'ajabi wataran kuma dariya, abinda kawai ke saka nutsuwa a zuciyar bawa shine haƙuri da karɓar ƙadda ta nasara ko faɗuwa, godiya ga ALLAH alokacin daya baka koda kaɗanne, rintse ido daga hangen nasama ka kula da wanda bai kaikaba, karɓar da hannu biyu daga nasarar sa'a ko faɗuwa, dan duk wanda yashigo duniya yasa a ransa makarantace ita, lokacin da wancan ke zuwa aji na gaba sannan wani ke dawowa baya maimaita ajin kokuma barin makarantar baki ɗaya.
Ummukulsoom tayi imani da waɗannan ƙalubalen a rayuwarta shiyyasa ta kwantar da hankalinta wajen maida hankali ga karatunta na boko dana islamiyya da Dad yazo da kansa ya sama musu. dan masu iya magana kance komai iliminka idan baka neman wani to lallai zaka rasa gaba ɗaya, kokuma kazama a jerin masu kafa tasu gidauniyar ta ɓata bisaga bigiren yarda da kai.
Ƙwarai da gaske Ummu ta canja a shekarunnan, danta sake girma da cika, a wanda ya santama ya ganta a yanzu idan ba faɗa maka akaiba bazaka shaidata ba, ga wata nustuwa da hankali data ƙara, tareda aji irinnan manyan yara masu aiki da tarbiyyar addinin islama.
Duk da kasan cewarsu acikin mafi rinjayen waɗanda ba musulmiba hakan baisa sun zubar da kimarsu da daraja ta ƴaƴan musulmaiba, basa shigar banza balle ballagazanci da sunan wayewa, akoda yaushe cikin taka tsantsan suke wajen girmama addininsu da al'adarsu, sun riƙe abinda yake nasu da hannu biyu, yayinda suka rintse idanu daga wanda bai dace dasuba ko bai zama mallakinsuba komai daɗinsa ko samun farin ciki daga garesa.
Wannan rayuwar tasu saita fara tasiri a zuciyar Peace, tana mamakin dama haka musulmai keda ƙyaƙykyawar mu'amula ashe? Gasu mutane masu gaskiya da ƙarfafa kai, aduk lokacinda wata ƴar matsala ta shigo a karatunsu takan damu, amma saita su Ummukulsoom suna faɗin haka ALLAH ya ƙaddara, maybe wani tushen nasarace yasaka ubangiji jarabtarsu danyaga imaninsu, mai makon taga rauni tattare dasu sai taga tarin tawakkali da ƙarfin gwiwa.
A ɓangaren ibada ko a ina suke lokacin salla yayi saisun sami wajen daya dace sunyita, ɓangaren mu'amularsu da maza akwai tsari, babu sakin fuska babu cuɗanya ta jiki sai dai da kuskure, Dakubo yayantane a gida ɗaya suke kwana suke tashi amma ko zama kusadasu basa bashi fuska balle taɓasu, sannan dukkan wani nau'in abinci ko nama da addininsu ya hanesu ci basa cinsa a gidan koda an girka, duk wani taro na shagala dasu jama'ar gidan zasuje su Bily basa binsu, tasha roƙonsu su rakata Choch dan kawai jan ra'ayinsu amma saisu sami hanya mai sauki su waske mata, samari da yawa sukan nufesu da kalmar so ko ƙawance amma basu taɓa tozartasu ko cin zarafinsu ba, ta hanya mai sauƙi suke fahimtar dasu karatune yakawosu port ba soyayya ba, duk yanda wani shaiɗani yaso mu'amulantarsu sukan nemi tsarin ALLAH da sharrinsa da gujema dukkan abinda zai ruɗesu da faɗawa tarkonsa.
Rayuwarsu a wajen bata hanasu saka hijjab ba, bakuma ta ruɗesu saka farce a hannayensu ba ko ƙara gashin doki a kansu, daduk abinda addinin islam ya hanesu dashi, ako ina kuma basajin shakkar nuna su musulmaine bare jin kunya.
Sunyi ƙawaye sosai yare daban-daban, sukan nema sani akan karatunsu ga wanda sukasan ya fisu, hakama wanda sukafi idan ya nemi taimakonsu sukan masa.
Waɗannan kaɗanne daga nasarori dasu Ummukulsoom suka samu da cigaban rayuwa.
A duk sanda suka sami sukuni kuma sakanzo gida suyi kwanaki su koma, hakama su Ummi sukanje su ziyarcesu aduk sanda suka sami ƙyaƙyƙyawar dama, kullum cikin musu nasiha suke da ƙara musu ƙwarin gwiwa tareda tsoratar dasu bijirema ALLAH da gangan saboda ruɗin duniya da tunanin ALLAH bazai kamaka ba wataran.
Haka rayuwar taci gaba da matsawa har suka kusa shefe wata shekarar, a yanzu haka watanni ƙalilanne suka rage musu kammala karatunsu, musamman ma Ummukulsoom, dan ita bily ma tana gab kasancewar ba tsarinsu ɗaya baneba.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Shekarar su yaa Amaan huɗu cikin ta biyar suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, dukda kasancewar yaƙine ya kaisu akwai cigaba tattare da tafiyar tasu mai yawa.
Ƴan uwa da abokan arziƙi sunyi farin ciki matuƙa da ganinsu, tareda godiya ga ubangijin daya basu ƙwarin gwiwa da nasara.

Lokacin da Attahir sukaje dubasu Ummu shida maman Ahmad ba ƙaramin mamaki ya shaba da ganin Ummukulsoom gaba ɗayanta ta canja, sai jinjina kai yake da sake girmama sunan ALLAH, wlhy koshi da ace a hanya yagamu da ita bazai taɓa shaidata ba, komanta ya canja tazama big girl ta gaske.
Baisan wata dariyar shaƙiyanci ta kufce masaba lokacin da Amaan ya faɗo masa a rai.
Lallai yana tausayin ƴan maza, ashe lokacin wasan yayi, dan angama gyara filin ga ƙwallo ga ƴan kallon wasa harma da alƙalan wasa a gefe.

Cike da zolaya ya kalli Ummu yana faɗin “Ummukulsoom baki tambayeni ina mutuminba?”.
Fararen idanunta ta ɗago ta kallesa, cikin muryarta mai sanyi da tarin nutsuwa tace, “Yaya Attahir wanene mutumin kuma?”.
Murmushinsa ya faɗaɗa sosai yana kuma kallon ƙyakykyawar fuskarta, “Lallai na kuma yarda ƙanwata ta girma, to tundama kin mantashi bara na tuna miki, abokina Ajiwa”.
Cikin halin ko in kula tace, “Yaya kenan, shida ba sallah ba yaza ai nai saving nashi a memory na dan gudun kiyayewa, shiba azumiba balle yazama cikin rubutattun ayukana na wajibi, mai riƙewa da adalci shike riƙe zuciya, mai ƙyautatawa da nasibi shike zane a dutse tamkar ruwa mai yaɗuwa a ƙorama, duk wanda kura ta koroshi a tafiya to ka tabbata bazai sake bin hanyarba, idan kaga an riƙe to ɗayan biyune, mosoyin na gaskiya, ko malami mafi kulawa akan ɗalibi, dan ba a taɓa mantawa da abubuwa uku, mutuwa, hisabi, makoma, tsoron ALLAH kesa a tuna mutuwa, Imani kesa a tuna makoma, ƙyaƙyƙyawan buri kesa a tuna alajanna, shikuma baya jerin ko ɗaya aciki, mizaisa yazama abin tunawata”.
Kai Attahir ya jinjina cikin fadaɗa murmushin fuskarsa, lallai duk bulalar daka raina itake zanar ciki da bayanka kaji zafi har ƙarkashin zuciyarka, Ajiwa lokacin yayifa, ga wuri ga kuma waina, ƴan kallo saiku ƙara shiri.

⛹🏻‍♀️lallai zamusha kallo na haƙiƙa🤣😝

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

“Fodio kana jinafa amma kaimin shiru ko?”.
Manyan idanunsa daya gada a wajenta ya buɗe a kanta, cikin muryar nan tasa mai amo da izza yace, “Momcy bansan mizan cemiki ba nikam, danni ban shirya auren ƴar kowaba”.
Harara ta zabga masa tareda watsa masa daƙƙuwa, “kaci gidanku Fodio, mikake nufi? Ba zakayi aureba a rayuwarka komi?”
Numfashi ya firzar tareda lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, sai dai yaƙi cewa komai.
“Wai miye ka tsuramin waɗannan idanun?”.
Karan farko da ya saki murmushin gefen baki wanda na tabbata da wata macen yaymawa saita kuma sumewa, bayi yakeba shiyyasa idan yayi saiya kasance na musamman, ita kanta Momcy da ta haifesa saida ta hangame baki, “O ALLAH, Fodio dan ALLAH karinga koda murmushi ne a rayuwarka, ba ƙaramin ƙyau yake makaba wlhy, amma ina daɗi ko yaushe fuska ɗinke kamar wanda aka haifa mala'ikun rahama basa kusa”.
Kansa kawai yaɗan dafe amma baice mata komaiba, yakuma maida fuskar ya ƙara haɗewa.
Dad dake bayansu tuni, yaɗan girgiza kansa kafin ya ida shigowa falon da sallama ciki-ciki kamar yanda ya saba.
Duk amsawa sukai, Hajiya Jamila dake kallonsa a ranta ayyanawa take “Oh ni jamila, wannan wane irin mutane ALLAH ya haɗani dasu, nikam nama ƙagara Bassam ya kammala karatunnan yadawo ko haƙoransa na rinƙa gani naji daɗi, amma kana tare da waɗannan ai dole ka zata kullum wani nasu ke mutuwa”.
Sudai basu san tanaiba, dan Amaan ma tashi yay yafice abinsa, dama abinci yazo ci, bayan yagamane yaɗan kwanta a falon yana hutawa kasancewar yanzu gidan nasu babu hayaniyar kowa, daga Momcy sai Dad, saiko idan ƴaƴan aunty Ummy su zo, yarinyar Ameer ma ba kawota akeba sai dai idan uwarta tazo gidan, hakama Ummayya yaronta sai tazo take zuwa dashi, Aneesa kam yanzune take da cikin, itakuma Aunty Nurse tana abuja abinta da ƴaƴanta tagwaye itama data haifa duk maza, inba zuwa taiba ba ganinsu akeba. Sai ƴan aiki wanda kuma dokace shigowarsu sashen musamman da ayanzu Yaa Amaan ɗin yana a gidan.
Chapter 45 · 0% Book details